Juyin mulki a Burkina Faso: Dawowar mulkin kama-karya a Afrika ta yamma

Asalin hoton, Reuters
Bayan juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso, mai sharhi a Afirka ta Yamma Paul Melly ya ce ya lura da wani sabon salon juyin mulki bayan dimokuraɗiyya ta yi kamar ta samu gindin zama a yankin.
Ƙasa da wata biyar da sojoji suka bayyana a gidan talabijin na gwamnatin Guinea don sanar da hamɓarar da gwamnatin Alpha Condé, an maimaita irin haka ranar Litinin a Burkina Faso, inda sojoji suka tumɓuke Shugaba Roch Kabore.
Kar kuma a manta da hawa biyu na juyin mulkin Mali, inda suka hamɓarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar Keïta a Agustan 2020.
Sun yi wa ƙungiyar Ecowas, mai lura da al'amuran tattalin arzikin Afirka ta Yamma, alƙwarin cewa za su shirya zaɓe a wata mai zuwa amma sai suka sake yin wani juyin mulkin a Mayun 2021 don tabbatar da ƙarfin ikonsu sannan suka sake tsara zamansu a mulki na tsawon kusan shekara biyar.
Wani abin mamaki kuma, a Afirka ta Yamma ne tsarin dimokuraɗiyya mai jam'iyyu barkatai ya samu gindin zama.
Kusan dukkan ƙasashen yankin dimokuraɗiyya suke bi a hukumance, ko da kuwa wasu daga cikinsu sun zaɓi shugaban ƙasa sau ɗaya, shugabannin kan bi duk hanyoyi don tabbatar da kan su a kan mulki na tsawon lokaci.
Yanzu ƙasa uku mambobin Ecowas (Economic Community of West African States) na ƙarƙashin mulkin soja.
Ko zamanin da aka manta da shi na mulkin soja na sake dawowa ne?
Ba za a iya amsa wannan tambayar cikin sauƙi ba, idan aka kalli al'amuran ta wata hanya.
Lamarin Guinea ya sha bamban da na saura - sakamakon tarihinta da ke cike da katsewar gwamnati da kama-karya.
An zaɓi Alpha Condé a matsayin shugaban dimokuraɗiyya na farko a 2010 amma daga baya ya mayar da kansa ɗan kama-karya ta hanyar gyara kundin tsarin mulki don ba shi damar yin takara a 2020 da kuma garƙame 'yan adawa masu yawa.
Hamɓarar da shi da sojoji suka yi ya sa an samu ƙwararin gwiwar gwamnatin haɗin kai, mutane da dama sun yi murna, hatta 'yan jam'iyyarsa ba su yi wani ƙorafi ba.
Yadda aka yi masu iƙirarin jihadi suka sake jawo juyin mulki
Kamar a Burkina Faso da Mali, hare-haren masu iƙirarin jihadi ne ya tashi hankalin mutane da dama.
Rahotannin da aka dinga samu na kai wa wurare hari sun jawo ɓacin rai daga sojojin da suke ƙorafin ana tura su yaƙi ba tare da kayan aiki ba, ko kuma ma babu abinci.
Juyin mulkin makon nan a Burkina - da ma irinsa a 2020 a Mali, har ma da na 2012 a Malin - sun nuna yadda ƙananan sojoji ke sadaukar da rayuwarsu a fagen yaƙi.
Abubuwa sun ƙara ƙazancewa ne bayan harin 14 ga Nuwamba kan sansanin soja na Inata da ke arewacin Burkina, inda aka kashe dakaru 53 cikin 120.

Asalin hoton, Reuters
Neman a haɓaka harkokin tsaro ya ƙaru a shekarar da ta wuce, abin dda ya sa Shugaba Kabore ya yi wa gwamnatinsa garambawul da kuma hafoshsin tsaro da zimmar rufe bakin 'yan adawa.
Sai dai cikin shekara biyu, an rufe makarantu fiye da 1,000 sannan mutum fiye da miliyan ɗaya da rabi suka tsere daga muhallansu don cira da raayuwarsu. Wasu sun zama mabarata a titunan babban birnin ƙasar. Kazalika, an kashe mutum fiye da 2,000.
Tabbas rikicn na yankin Sahel ba sabo ba ne. Tsawon lokaci, rikice-rikicen ƙabilanci ya ƙara ta'azzara matsalar tsaro a ƙauyukan yankin, yayin da gwamnatoci ke ci gaba da fama da ayyukan raya ƙasa.
Shigar sojojin Faransa da na ƙasashen Airka ta Yamma a Mali a 2013 ya sa an ƙwato wasu yankuna daga hannun masu iƙirarin jihadi. Sai dai bai hana ci gaba da faruwar tashin hankali ba a rikicin ƙabilanci.
Cikin shekara biyu da suka wuce, hare-haren masu iƙirarin jihadi kamar ma ƙaruwa yake yi, inda suke kashe jami'an tsaro da fararen hula.
Manyan garuruwan Fada Ngourma da kuma masu maƙotaka da Nijar sun zama abubuwan tsoro. Haka nan, ana yawan binne ababen fashewa a kan tituna da ke hana zriga-zirgar zuwa kasuwanni da makarantu.
A watan Yunin da ya wuce, hae-hare a garuruwan Solhan da Tadaryat, da ke gundumar Yagha, sun yi sanadiyyar kashe mutum 174.
Yadda Shugaba Kabore ya rasa farin jini
An zaɓi Mista Kabore a Nuwamban 2015 yayin da mutane ke hanƙoron sabon salon mulkin da ba na kama-karya ba. Shekara biyar haka, an sake zaɓen sa a wa'adi na biyu ba da wata matsala ba.
Sai dai bayan haka farin jininsa ya fara raguwa sakamakon ƙaruwar hare-haren masu iƙirarin jihadi.
Bayan ƙorafin da suka yi, a ranar Lahadi sai wasu sojoji a manyan barikokin sojoji suka yi bore a Ouagadougou. Wannan boren na yammaci ne ya rikiɗe zuwa juyin mulki washegari.
A bayyana take cewa abin da ya faru a Mali a 2020 na gab da faruwa. Hakan ta faru ne bayan ƙaruwar hare-hare a shekara kafin haka duk da shigar sojojin ƙasashen waje.
Sai dai a wannan karon, a Burkina Faso, an hango faruwar hakan da wuri.
Harin Inata ya zo ne a daidai lokacin da gwamnati ke tsaka da tsara dabarar yaƙi, wanda kuma lokacin tuni zukatan mutane suke cike da fargaba.
Ƙasa da wata uku bayan haka, Mista Kabore ya sauka daga mulki kuma yana hannun sojoji.

Asalin hoton, Getty Images
Kusan ka iya cewa da gangan 'yan bindigar ke so su tayar da hatsaniya cikin sojojin yankin Sahel.
Amma a ƙashin gaksiya, kisa bayan kisa da ke ɗauka rayukan mazauna ƙauyuka da jami'an tsaro ka iya haddasa bore da jefa tsoro a zukatan sojoji a ko'ina.
Yanzu haka ana raɗe-raɗin ita ma Nijar, wadda ke fuskantar irin waɗan nan hare-hare, za ta iya fuskantar juyin mulki.
Masu sharhi na ganin cewa an mayar da matsalar yankin Sahel ta tsaro kawai alhalin kuma ayyukan ci gaba ya kamata a saka a gaba.
Amma mazauna yankin kan ce ba zai yiwu a yi wani aikin raya ƙasa da haɓaka tattalin arziki ba ba tare da samar da tsaro ba tukunna.












