Burkina Faso: Dalilin da ya sa sojoji suka hamɓarar da Shugaba Roch Kaboré

People show their support for the military after Burkina Faso President Roch Kabore was detained at a military camp in Ouagadougou, Burkina Faso, January 24, 2022

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu mazauna Ouagadougou babban birnin ƙasar sun fito don nuna goyon bayansu ga sojojin
    • Marubuci, Beverly Ochieng
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Monitoring

Juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso abu ne mai tayar da fitina amma bai zo da mamaki ba.

Hamɓarar da Shugaba Kaboré shi ne juyin mulki na huɗu a Afirka ta Yamma cikin wata 17 da suka gabata.

Ita kuwa ƙasar Mali, ta fuskanci juyin mulkin har sau biyu cikin wannan lokacin saboda zargin da ake cewa gwamnati ta kasa kawo ƙarshen yaƙin masu iƙirarin jihadi.

Yaya girman matsalar masu iƙirarin jihadin take?

Kamar a Mali, sauke Kabore ya biyo bayan zargin da wasu sojoji suka yi cewa gwamnatinsa ba ta ba su goyon bayan da ya dace wajen yaƙi da 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙ da ƙungiyoyin al-Qaeda da Islamic State.

A ranar Lahadi an samu rahotannin yin bore a barikokin soja da dama a babban birnin ƙasar, Ouagadougou, da kuma garuruwan Kaya da Ouahigouya.

Rikcin ya biyo bayan watanni da aka shafe ana yi wa gwamnati bore da zimmar nerman shugaban ƙasa ya sauka daga mulki.

Rikicin 'yan bindigar da ya fara a 2015 ya kashe aƙalla mutum 2,000 sannan ya raba miliyan ɗaya da rabi da gidajensu, a cewar Wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD). Kazalika, an rufe makarantu a sassan ƙasar da yawa saboda abu ne mai haɗari ga ɗalibai.

An yanke ƙauna kan shugaban ƙasar ne jim kaɗan bayan an kai hari kan garin Solhan da ke arewacin ƙasar a watan Yunin 2021. Fiye da mutum 100 ne suka mutu a harin da aka zargi 'yan bindigar da suka tsallako daga Mali.

Harrin ya jawo zanga-zanga a faɗin ƙasar, abin har ya sa Shugaba Kabore ya yi wa gwamnatinsa garambawul, inda ya naɗa kansa a matsayin ministan tsaro.

Haka nan, wani harin da aka kai kan sansanin soja na Inata a Nuwamban 2021 ya ƙara ta'azzara fushin al'umma a kan gwamnati.

Jami'an tsaro fiye da 50 aka kashe. Daga baya an samu rahoto cewa dakarun sansanin sun nemi a kawo musu kayan abinci da kuma kayan aiki sati biyu kafin harin amma har yanzu babu su babu labarinsu.

Shugaban ya kari dukkan ministocinsa, ya naɗa sabon firaminista da kuma ministan tsaro yayin da ake shirin tattaunawa da 'yan jam'iyyar adawa.

Ta yaya masu iƙirarin jihadi suka shiga Burkina Faso?

Duk da matsalolin tsaro da na siyasa da ake fama da su a Afirka ta Yamma, Burkina Faso ba ta fuskantarsu har zuwa boren da aka yi a 2014, wanda ya haddasa kifar da gwamnatin Blaise Compaoré - shugaban da ya fi kowa daɗewa a kan mulki.

Wani yunƙurin juyin mulki da aka yi a 2015 ya raba kan sojojin sosai. An zaɓi Mista Kabore a wannan shekarar da zimmar zai haɗa kan ƙasar.

Sai dai kuma 'yan bindiga daga Mali - inda masu iƙirarin jihadi suka yi nasarar ƙwace fafutikar ɓallewa a 2012 - sun kai hari a babban birnin ƙasar a lokacin da Mista Kabore ke shirin hawa mulki.

'Yan bindigar sun yi amfani da damar da suka samu ta ƙarancin kayan aiki na jami'an tsaro wajen kai hare-hare a kan iyaka sannan suka kafa kansu a yankunan.

Masu jihadin sun haddasa husuma tsakanin Musulmai da Kiristoci da suka daɗe suna tare a baya a Burkian Faso.

Kazalika, sun yi amfani da irin halin ƙuncin rayuwa da mutane suke ciki na rashin tallafin gwamnati.

A 2020, mutanen da suka tsere daga gidajensu ba su samu damar jefa ƙuri'unsu ba a zaɓen shugaban ƙasar da Mista Kabore ya yi nasara da kashi 58 cikin 100 a wa'adi na biyu.

Mene ne ya bambanta da na Mali?

An yi ta samun fargaba cewa wani sabon tsari na shirin faruwa.

Abubuwan da suka faru kafin juyin mulkin sun yi kama da waɗanda suka faru a Mali kafin a hamɓarar da gwamnati a Agustan 2020.

Mutane sun fara zanga-zanga ne bayan hare-haren da aka dinga kai wa kan sojoji da mutanen gari, abin da ya sa 'yan ƙasa suka yanke ƙauna da gwamnatin Mali ta Marigayi Ibrahim Boubacar Keïta.

Sai dai kuma yayin da 'yan Mali suka goyi bayan juyin mulkin, 'yan Burkina Faso za su kasance cikin ɗar-ɗar saboda kar abin da ke faruwa ya ci gaba a ƙarƙashin mulkin soja.

Ko masu ƙin jinin Faransa sun taka rawa?

Dukkan ƙasashen sun kasance ƙarƙashin mulkin mallakar Faransa kuma ƙasar ta ci gaba da ƙawancen soja da na tattalin arziki masu girma a ƙasashen har bayan samun 'yancin kai.

Kamar dai a Mali, sojojin Burkina sun dogara da tallafin da Faransa ke ba su wadda ta tura sojoji 5,100 a yankin cikin wani shiri da ta kira Operation Barkhane.

An ƙaddamar da shirin ne lokacin da Faransa ta tura sojoji su dakatar da masu iƙirarin jihadi shiga babban birnin Mali Bamako a 2013.

Sai dai 'yan ƙasa sun fara dawowa daga rakiyar Faransa bayan abubuwa sun ƙara taɓarɓarewa.

A watan Disamba, wasu mazauna Kauya sun tare wa dakarun Faransa hanya da ke kai wa sojojin Burkina kaya suna masu zargin dakarun Barkhane da haɗa baki da masu iƙirarin jihadin.

An ci gaba da korar Faransa daga yankin na Sahel da ya ƙunshi ƙasashen biyu sakamakon hatsaniya tsakaninta da Mali, abin da ya sa Faransa ta janye kusan rabin sojojin Barkhane.

'Yan bindigar ka iya amfani da giɓin da aka samu, yayin da rikicin siyasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa ka iya haifar da rashin yin aiki tare tsakanin sojojin haɗin gwiwa na G5 Sahel wanda ya ƙunshi daakrun Mali da Nijar da Burkina Faso da Chadi da Mauritania.

A lokacin da Mali ke neman taimakon Rasha don maganin matsalar, maƙotanta na Sahel - kamar Burkina Faso - ba sa goyon bayan dabarar ko kaɗan.

Ko ya kamata yankin ya yi fargaba?

Juyin mulki a Burkina Faso na nuna cewa masu aikata shi ba sa tsoron matakan da ƙungiyar Ecowas - ta ƙasashen Afirka ta Yamma - za ta ɗauka a kan su. Takunkuman da aka saka wa Mali da Guinea a kwanan nan bai hana sojoji ci gaba ba.

Shi ma Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar ya fara mulki cikin fargaba a 2021 lokacin da aka yi yunƙurin juyin mulki a ƙasar kafin a rantsar da shi.

Ya sha sukar rikicin siyasar da ke faruwa a maƙociyarsa Mali da kuma tasirin da hakan zai yi kan dakarun sojansu a yaƙi da masu iƙirarin jihadi.

Shugaban na yunƙurin kauce wa duk wata fargaba da za a nuna game da harkokin tsaro ta hanyar ziyartar dakaru a fagen fama, wanda a yanu ake ganin suna aiki.

Tashin hankalin da ke faruwa a Mali da Burkina na ƙoƙarin shafar maƙociyarsu Ivory Coast. An samu hare-haren masu iƙirarin jihadi a yankunan ƙasar tun daga Yunin 2020 da ake kai wa jami'an tsaro.

Map
1px transparent line