China da Amurka a Afirka: Shin tsakanin dimokuradiyya da gina ababen more rayuwa me 'yan Afirka suka fi so?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Dickens Olewe
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Kasashen Afirka 17 ne ke halartar taron kwanaki biyu kan Dimukradiyya da shugaban Amirka Joe Biden ke karbar bakunci, a matsayin wata kafa ta tattaunawa kan karuwar mukkin danniya. Masu sa ido na cewa manuniya ce ga yanayin dangantaka tsakanin Amirka da China.
Taron na zuwa ne, mako guda bayan taron da aka yi kan dangantaka tsakanin China da Afirka (Focac) da aka guanar a birnin Dhakar na kasar Senegal, wanda ake ganin China ta mamaye nahiyar ta fuskar kasuwanci.
Shugaba Xi Jinping ya sanar da zuba jarin dala biliyan 40, a fannin noma, da kasuwanci ta intanet, da sauyin yanayi, da masana'antu, da ba da tallafin miliyoyin allurar rikagafin cutar korona, da aikin hadin gwiwa na masana'antu.
"Ta bayyana karara kasashen da suke jaddada da inganta dimkradiyya sun fi kusanci da China," in ji W Gyude Moore, babban jami'i a hukumar ci gaba da bunkasar kasashe ta duniya.
"Babbar bukatar da ake da ita a Afirka ita ce ayyukan ababen more rayuwa, kuma wanda je ayyukan nan sama da shekaru 20 a nahiyar ita ce China," in ji shi.
Ayyukan ababen more rayuwa kan zabe
A wajen taron na Focac, an dauki hoton ministan harkokin wajen Saliyo David John Francis ya na mika wa takwaransa na China Wang Yi zanen wata gada mai nisan kilomita hudu da ake sa ran yin ta nan gaba, wadda ke nuna muhimmancin China da rawar da ta ke takawa a Afirka.
An yi kiyasin gadar ta Lungi da za ta sada birnin Freetown da babban filin jirgin sama na kasar za ta ci kudi dala biliyan 1 da miliyan 200, gadar za ta rage cinkoson ababen hawa da wani lokacin mutane na shafe awanni kafin isa filin jirgin.
Masu sa ido na cewa aikin gadar shi ne babban aikin da shugaba Julius Maada Bio, ya yi da ya ke son amfani da damar a gangamin yakin neman zabe a shekarar 2023, duk da cewa babu wani abun azo a gani ga tattalin arziki, da cewa makudan kudaden da za a kashe wajen yin gadar za a iya magance matsalolin da kasar ke fama da su da su a kasar musamman mace-macen mata wajen haihuwa da jahilci.

Asalin hoton, Twitter/Nairobi Expressway
Shugaban Gambia, Adama Barrow da ya yi nasarar zama shugaban kasa a karo na biyu, bayan bude gadar da China ta yi da ta inganta sufurin kasuwanci tsakanin kasar da makofciyarta Senegal, sannan ya sha alwashin yin wani aiki na hanyoyi da su ma China ce za ta zuba kudin da za a yi su.
Wata babbar mai bincike a jami'ar Oxford ta Birtaniya, Folashade Soule-Kohndou, ta ce 'yan siyasar Afirka na bukatar China ta zuba kudade a fannin ayyukan ababen more rayuwa domin cika alkawarin da suka dauka a lokacin yakin neman zabe.
Kamar yadda bankin raya kasashen Afirka ya bayyana, nahiyar na bukatar dala biliyan 130 zuwa dala biliyan 170, a kowacce shekara domin ayyukan ababen more rayuwa, amma a yanzu an samu raguwar matuka a dan tsakanin nan inda dakyar ake iya zuba dala biliyan 68 zuwa dala biliyan 108.
Za a iya cike gibin da sabon shirin Tarayyar Turai na dala biliyan 340 na ayyukan ababen more rayuwa, da shirin Amirka na Build Back Better (B3W), dukka ana kokarin tallata su ga kasashe maso tasowa idan China ba ta yi abinda suke bukata.
Amma a halin yanzu, ba a cika maganar wadannan shirin biyu ba idan aka kwatanta da BRI wanda tuni ya fara aikin hanyoyi, da titib jirgin kasa da manyan tasoshin ruwa a sassa daban-daban na duniya.
Amirka da China sun hade
Kwararre kan kasuwanci Francis Mangeni ya ce, zai fi alfanu ga Afirka ta maida hankali kan yi mata ayyuka masu inganci maimakon gasa da juna da kasashen masu karfin tattalin arziki ke yi a kan ta.
"Maimakon ganin China na gasa da wata kasa a Afirka, kamata ya yi a maida hankali wajen inganta ayyukan yankin," in ji shi..
Amma ya kara da cewa, ya ragewa kasashen Afirka su yi amfani da kasancewarsu anan domin tabbatar da cewa sun yi musu aikin da suke bukata.
Har wa yau, shirin Global Gateway da B3W, ka iya samun tagomashin kasancewar China na ayyukan wajen maida hankali kan ayyukan fasaha, da zuba jari mai kudin ruwa kalilan, in ji Mis Soule-Kohndou.
Mista Mooreya amince, "Afirka na bukatar karkatar da kudaden ayyukan ababen more rayuwa, dan hakan wanna dama ce gare su". Amma ya kara da cewa China ta zuba jari da kudade a ayyuka masu yawa a nahiyar da wuya aiya ja da ita, duk da cewa akwai kamfanonin gine-ginen Amirka da ke gasa da ita ta wannan fannin.
Yakuma ce Amirka da China na da mabanbantan ra'ayi da fannin da kowa ya kware akai, hakan zai kai ga samar da ayyukan da Afirka za ta mora da suka hada da fannin lafiya, da ilimi, da tsaro wadanda su aka fi bukata a nahaiyar.
"Makarfafar Amirka ita ce a fannin gina al'umma. Jami'oin Amirka na sahun gaba a masu inganci na duniya, haka tsarin kiwon lafiyarsu. China za ta iya gina asibitoci ya yin da Amirka kuma ta bai wa likitoci horo mai inganci," in ji Mista Moore.
Ya yin da ake sa ran al'ummar nahiyar Afirka za su rubanya sau biyu da mutum biliyan 2 da miliyan 500 nan da shekarar 2050, kuma abin da za a maida hankali a nahiyar akai shi ne bunkasa tattalin arziki da ayyukan da za su bunkasa al'ummarta.

Asalin hoton, Getty Images
Yarjejeniyar kasuwanci maras shinge da aka cimma tsakanin wsu kasashen Afirka (AfCTA), da aka kaddamar a watan Junairun da nufin inganta kasuwanci tsakanin kasashen, ana masa kallon babbar hanyar cimma wannan damar.
Mista Mangeni, ya ce bukatar China ta shiga tsarin BRI da AfCTA "zai matukar bunkasa fannin kasuwanci tsakanin yan kin fiye da tunani".
"Kudaden da ake batarwa a kasuwanci a Afirka musamman na sufuri ya fi na kowacce kasa a duniya, inda ake kashi 90 cikin 100 a wannan fannin," ya kara da cewa "yawancin mutanen da ke sukar China, su na yi ne saboda ba su fara shiga fannin zuba jari da ayyukan ababen more rayuwa ba".
Shugaba Yoweri Museveni na Uganda, wanda aka gayyata taron na Dimukradiyya, tura mninistan harkokin wajen kasar a matsayin wakili baban kuskure ne gare shi, hakan ya sanya karsashin masu zuba jarin kasashen wje da sage musu gwiwa.
Mista Museveni na daga cikin shugabannin da sukai matsa lambar kara kai kayan da Afirka a kasuwannin China. A baya-bayan nan ya musanta rahotannin da ke cewa babban filin jirgin saman kasar na cikin barazanar fadawa hannun China saboda bakin bashin da ta ke bin kasarsa, sai dai zargi ne da dukkan kasashen suka musanta.
Sai dai wadannan ayyukan na cike da rashin gaskiya, da cin hanci da rashawa, abin da ake ganin na taka rawa wajen jibagawa kasashen Afirka bashin da suke gagara biya.
A matsa gaba babu Yammaci ko Gabashi
Wasu kwararru na nuna damuwa kan rashin manufa ga kasashen Afirka, wajen duba tsarin da China ke tafiyarwa.
"Baki daya, China na taka muhimmiyar rawqa wajen bunkasar nahiyar Afirka ta fuskar hulda da juna, amma dai dole Afirka ta zage damtse da sabon tsari kan hulda da China," kamar yadda Davice Monyae na cibiyar bincike kan hulda tsakanin China da Afirka wadda ke jami'ar Johannesburg a Afirka ta Kudu.
"A shekarar 2006 China, ta fitar da tsare-tsare uku kan Afirka, tun lokacin har yanzu Afirka ta gagara yin hakan kan hlda da China," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Awani littafinsa, Howard French ya tuna tattaunawar da ya yi da tsohon jakadan China a Zambia, wanda ya yiwa tsarin huldar Amirka a Afirka shagube.
"Ke [Amirka] ku na daukar ma'aikata aiki, sannan ku sanya su dinga sa wa juna ido a ko ina ...daga nan sai me? Ban ga wasu hanyoyi ko makarantu ko asibitoci da suka yi da mutane ke amfanuwa da su, wanda za su dade ana amfani da su. Watakil bai wa mutane horo kan zabe, ita ce kadai babban tallafin da suka ba da," in ji Zhou Yuxiao ambasadan Zambia a wancan lokacin.
Wani marubuci dan Faransa ya maida martani da batun tallafin gaggawa da Amirka ke bayarwa, wanda ya taimaka da inganta lafiyar mutane ta hanyar samarwa miliyoyin mutane magani tun bayan kaddamar da shirin a shekarar 2003.
Sai dai ita kan ta Afirka, kamata ya yi ta shrewa kan ta hanya, kamar yadda shugaba Kwame Nkrumah da ya karbarwa Ghana 'yanci ya sha nanata cewa ''kada ku kalli gabas ko yamma'' ku sanya gaban ku kawai ku ci gaba da aiki.
Kamar yadda wani bincike ya nuna, yawancin 'yan Afirka na son rayuwa a kasashen da Dimukradiyya ke da cikakken 'yanci, amma su na son gwamnatocin da ke musu ayyukan more rayuwa da suka shafi gina hanyoyi masu inganci, da inganta fannin lafiya, da fannin ilimi da tsaro da sauransu.
A karshe, masu sharhi kan sha'anin kasashen waje na ganin cewa, idan ana son cimma hakan, dole sai shugabannin Afirka sun fara sanya muradun kasashensu a gaba ba na kashin kan su ba, su fito da shirye-shirye da tsare-tsare, maimakon su zama 'yan amshin shatan kasashen yamma ta yadda sai abin da aka bukaci su yi suk yi domin ci gaban nahiyarsu.











