Paul-Henry Sandaogo Damiba: Tarihin sojan da ya jagoranci juyin mulki a Burkina Faso

Hoton da aka dauka daga wani faifan bidiyo na nuna Kyaftin Kader Ouedraogo yana magana a gidan talabijin na 'RTB' a birnin Ouagadougou na Burkina Faso.

Asalin hoton, Anadolu Agency

Bayanan hoto, Hoton da aka dauka daga wani faifan bidiyo na nuna Kyaftin Kader Ouedraogo yana magana a gidan talabijin na 'RTB' a birnin Ouagadougou na Burkina Faso a ranar 24 ga Janairu, 2022. Laftanar Kanar Paul-Henry Sandaogo Damiba ke zaune a gefen damansa.

A ranar Litinin ne sojoji a Burkina Faso suka sanar da hambarar da gwamnatin Shugaba Roch Kaboré.

Hakan na nufin wannan ne karo na hudu da sojoji suka kwaci mulki a kasashen Yammacin Afirka cikin wata 17 da suka gabata.

A halin yanzu Kwamitin Kishin Kasa da Kare Muradu da Sabuntawa na Burkina Faso yana karkashin jagorancin Laftanar Kanar Paul-Henry Sandaogo Damiba.

Sai dai mutane da dama ba su san tarihin wannan sojan da ya kawo karshen mulkin Shugaba Kaboré.

An haifi Laftanar Kanar Paul-Henry Sandaogo Damiba ranar 2 ga watan Janairu na 1981.

Babban hafsan sojojin kasan, mai shekara 41, ya yi karatunsa na digirin farko a makarantar sojoji ta École militaire da ke Paris.

Ya kuma yi digirinsa na biyu a kan fannin aikata miyagun laifuka daga Conservatoire national des arts et métiers (CNAM) duk dai a birnin na Paris.

A baya ya taba rike mukamin Kwamandan yanki na 3 da ke kula da babban birnin kasar Ouagadougou.

Kanar Damiba tsohon mamba ne na bataliyar da ke kare shugaban kasar, kuma tsohon dogarin Blaise Comaoré ne wanda aka hambarar daga mulki a 2011 bayan wani bore da sojojin kasar suka yi.

A shekarar 2015, yana cikin manyan sojojin da suka ki goyon bayan yunkurin hambarar da gwamnati da wasu sojojin bataliyar da yake aiki suka yi, kuma an rushe ta jim kadan bayan aukuwar lamarin.

An kira shi ya bayar da shaida a shari'ar da aka yi daga baya saboda alakar da yake da ita da Janar Djibril Bassolé.

Tun shekarar 2016, yana cikin wadanda ke kan gaba da yaki da ta'addancin da ake yi a kasar.

Ya sami horo a kusan dukkan sassa na rundunar sojin kasar.

Ya kuma wallafa wani littafi mai suna: Sojojin Afirka ta Yamma da Ta'addanci: Martani Maras Tabbaci.

Paul-Henri Damiba ya jagoranci bataliyoyin soji daban-daban, cikinsu har da na Dori da Ouahigouya, wani yanki da ake kai hare-hare akai-akai.

Sabon shugaban Kwamitin Kishin Kasa da Kare Muradu da Sabuntawan shi ya gaji Emmanuel Zoungrana, wanda aka kama ranar 8 ga watan Janairu kuma ana tuhumar sa da yin zagon kasa ga tsaron kasar ta Burkina Faso.