ECOWAS ta ƙaƙaba wa Mali takunkuman karya tattalin arziki

Asalin hoton, Getty Images
Masu sharhi kan lamuran siyasa sun fara tofa albarkacin baki a kan takunkuman karya tattalin arziƙi da Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) da takwararta Ƙungiyar Harkokin Kuɗi ta Afirka ta Yamma suka ƙaƙaba wa Mali da yammacin ranar Lahadi.
ECOWAS ta yanke shawarar maƙwabtan ƙasashe su rufe kan iyakokinsu da ƙasar Mali tare da ƙaƙaba mata tsauraran takunkumai saboda jan ƙafar da take yi wajen gudanar da zaɓuka bayan wani shirin miƙa mulki na tsawon shekara ɗaya da rabi.
Haka kuma ECOWAS ta amince da rufe dukiyar ƙasar Mali da ke jibge a Babban Bankin Ƙasashen Afirka ta Yamma, tare da dakatar da duk wata hulɗa da gwamnatin ƙasar sai dai ta kayayyakin lafiya da sauran kayan buƙatun rayuwa da suka wajaba.
Mamman Sani Roufa'i mai sharhi kan harkokin siyasa a Jamhuriyar Nijar ya shaidawa BBC cewa baya jin wadannan takunkumai za su yi tasirin kai tsaye ga Mali, wadda dama can matsaloli sun yi mata yawa, sai dai ya ce duk da hakan kasar za ta ji a jikinta.
''Wannan mataki, an jima ba a ga an dauki irin shi mai tsauri akan wata kasa da ke cikin mambar Mali ba, a ma iya cewa yun lokacin da aka kafa ECOMOG , da lokacin da aka samu matsala a kasar Guinea Bissau, ECOWAS ba ta taba samun kann ta cikin matsala kamar na halin da ake ciki a Mali a yanzu ba.
A iya cewa matakan da aka dauka masu tsaurin gaske ne, amma idan aka yi duba ga halin da kungiyar ta samu kann ta a ciki na tattalin mutuncin ta sai ace matakin ya yi daidai.
Matukar ECOWAS ta bari aka ci gaba da tfaiya kann halin da Mali ke ciki,wato sojoji da suka ce sai sun shekara biyar kafin su mika mulki ga farar hul, zai bude hanya ga wasu kasashen da suke son yin haka misali Guinea Conackry, don haka matakin da aka dauka kann Mali ya yi daidai,'' in ji Roufa'i.
Sai dai ya kara da cewa wadanna takunkumai da aka kakabaewa Mali ba wani tasirin azo a gani za su yi ba, la'akkari da cewa a yanzu mu'amala tsakanin kasashe daman ta ja baya.
Idan aka ce za a tsaida asusun ajiyar kasa ko zirga-zirga tsakanin kasashe makofta, kamar su jamhuriyar Nijar, Burkina Faso da Senegal da sauransu, wanda kai tsaye Mali ta dogara ne akan su saboda ba ta da iyaka da teku, don haka sai ta kasashe makofta ake iya shigo da wasu kayan bukatun, ta nan kam za ta ji a jikinta.
Amma a yanzu da wasu sabbin kasashe suka shiga cikin mu'amalarta, kamar su Rasha da Turkiyya da sauransu, sanin cewa akwai ta inda za ta samu sassauci babu wani mummunan tasiri da takunkuman za su yi.
Sai dai Hakan ba ya na nufin sam ba za ta ji a jikinta ba, musamman talakawa su ne za su fi kwana a ciki, a takaice dai tasirin tsaka-tsaki ne ba kamar yadda ake zato ba.
Babbar matsalar dai ita ce batun taro, musamman a kasar da a haka ma Yaya ta kare bare an bar ta ita daya, wanda a halin da ake ciki ma kusan kashi biyu cikin ukun ta a hannun mayakan jihadi ko 'yan tawaye ya ke.''
A karshe ya ce daman Mali kasa ce da ta ke daidaice, dan haka wasu na ganin babu wani abu da zai sauya.
Sai dai kuma batun da ake yi na farfado da rundunar tsaro ta ECOMOG ka iya magance matsalar tsaro da Mali ke fama da ita.
To amma abin lura shi ne yawancin kasashen da ke taimakawa wannan runduna takansu suke yi su na fama da matsaloli tsaronb musamman Najeriya, wadda a baya ita kadai ce kasar da ke zuwa warware rikici a wata kasar.











