Juyin mulki a Mali: Sojojin da suka jagoranci hamɓarar da Keita

Scène de joie au passage des militaires

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yadda ake murnar hamarar da gwamnatin Keita da sojoji suka yi a Bamako

Jagororin juyin mulkin da ya sauke Shugaban Mali Ibrahim Boubakar Keïta ranar Talata sun haɗa da mataimakin shugaban barikin soja da kuma wani janar da ya samu horo a ƙasar Faransa.

Ga guda uku daga cikin jagororin:

1 - Col Malick Diaw

Le colonel Malick Diaw est le chef adjoint du camp de Kati où la mutinerie a commencé

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kanal Malick Diaw shi ne mataimakin shugaban barikin soja na Kati, inda aka fara shirya juyin mulkin

Shi ne mataimakin shugaban barikin soja na Kati, inda aka fara boren da ya rikide zuwa juyin mulkin.

Babu wasu cikakkun bayanai a kansa baya ga cewa bai daɗe da komawa daga ƙasar Rasha ba daga samun horo.

Shi ne ya tsaya a kusa da mataimakin shugaban rundunar sojin saman ƙasar Col-Major Ismael Wagué a lokacin da yake karanta sanarwar ƙwace iko da dakaru suka yi a ranar Laraba, a madadin sojin da suka yi juyin mulki.

Wani saƙo da aka wallafa a tuwita ya ce: "An yi amannar Kanal Diaw ne jagoran juyin mulki a barikin Kati, mai nisan kilomita 15 daga Bamako. An ce ya gaya wa shugaban ƙasar cewa ya sauka daga mulki kafin ƙarfe biyu na ranar Talata.''

2- Kanal Sadio Camara

Col Sadio Camara

Asalin hoton, other

Bayanan hoto, Col Sadio Camara

Kanal Camara, shi ne tsohon shugaban sansanin Kati.

Shafin jaridar Tribune ta Mali ya rawaito cewa an haife shi a shekarar 1979 a Kati da ke kudancin yankin Koulikoro.

Ya kammala karatunsa a makarantar horar da sojoji ta Koulikoro da mafi girman daraja. Daga nan sai aka tura shi kudancin Mali inda ya yi aiki ƙarƙashin Janar El Hadj Gamou har zuwa shekarar 2012.

Daga baya Kanal Camara ya zama darakta na makarantar horon soji ta Kati, muƙamin da ya riƙe har zuwa watan Janairun 2020 a lokacin da ya tafi makarantar horon sojoji ta Rasha.

Jaridar Mali Tribune ta ce ya koma Bamako a farkon watan nan don yin hutun wata ɗaya.

''Ana yabon Kanal Camara a duk wuraren da ya yi aiki kuma abokan aikinsa na ganin girmansa da sha'awarsa. A ganinsu yana da halayyar tsantseni da mayar da kai kan aikinsa da kuma sadaukarwa,'' a cewar kafar intanet din.

3 - Janar Cheick Fanta Mady Dembele

Général Cheick Fanta Mady Dembele

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Janar Cheick Fanta Mady Dembele

Gen Cheick Fanta Mady Dembele, shi ne shugaban cibiyar Alioune Blondin Beye mai aikin tabbatar da zaman lafiya.

An ɗaukaka muƙaminsa zuwa birigediya janar a watan Mayun 2018 kuma ya karɓi shugabancin cibiyar ne a watan Disamban 2018.

Gabanin ba shi wannan muƙami a cibiyar, Janar Dembele ne shugaban sashen sasanta rikici da tsare-tsare na Ƙungiyar Tarayyar Afrika da ke birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha.

Janar Dembele ya kammala karatunsa a makarantar horon soji ta Saint-Cyr a Faransa. Ya kuma yi karatu a Kwalejin garin Koulikoro a Mali. Yana da digiri a fannin tarihi daga Jami'ar Paris I Panthéon-Sorbonne.

Mali

Yana da digiri na biyu a fannin injiyan gine-gine daga Jami'ar German Federal Army a Munich.