Juyin Mulki a Mali: Me zai faru bayan hamɓarar da Ibrahim Boubacar Keita?

Les militaires maliens indiquent ne pas vouloir s'éterniser au pouvoir

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasu sojoji yayain da suke murna bayan yin juyin mulki
    • Marubuci, Daga Kahofi Jischvi SUY
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Dan jarida

Hamɓarar da Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta ya haifar da fargaba kan makomar siyasar ƙasar Mali.

Ƙasashen duniya da dama sun yi Allah-wadai da juyin mulkin, inda ake bayyana damuwa kan yiyuwar ƙazancewar rikici a Mali, wadda tuni take fama da rikin mayaƙa masu da'awar jihadi da kuma rikicin ƙabilanci.

Sojojin da suka jagoranci juyin mulkin sun sanar da kafa kwamitin da zai tsara mayar da mulki ga farar hula sannan sun nuna cewa ba za su dauwama ba a kan mulki.

Amma tambayar a nan ita ce, yaushe za a gudanar da zaɓe kuma wace rawa ƴan siyasa za su taka a wajen sauya gwamnatin?

Me za mu yi tsammani daga ECOWAS?

Mahamadou Issoufou

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mahamadou Issoufou, shugaban Nijar kuma shugaban ECOWAS

Ecowas wacce ta yi kakkausar suka ga kama shugaban Mali da kuma juyin mulki abin da ta yi ke nan a 2012, lokacin da Amadou Haya Sanogo ya jagoranci juyin mulki.

Kungiyar ta ƙasashen yammacin Afirka ta yi matsin lamba ga sojojin, inda ta ƙaƙabawa wa sojoji takunkumi idan suka ƙi miƙa mulki ga farar hula.

Ɗaya daga cikin matakan da Ecowas ta ɗauka bayan juyin mulkin 22 ga Maris shi ne matakin rufe kan iyakokinta da Mali, tare da saka wa ƙasar takunkumin hana kasuwanci da hada-hadar kudi.

Matakin ya yi tasiri sosai ga ƙasar inda ta rasa samun fetir da wasu manyan buƙatu da tattalin arzikinta ke buƙata. Dole sojojin suka miƙa mulki.

A wannan karon, Ecowas ta ɗauki irin wannan matakin inda ta sanar da rufe dukkanin iyakokinta na ƙasa da sama da Mali da kuma katse duk wata hulɗar kasuwanci, sa'o'i bayan kama shugaban ƙasar da wasu manyan jami'an gwamnati da sojoji suka yi.

Nan take kuma ƙungiyar ta sa aka ƙaƙaba takunkumi kan waɗanda suka yi juyin mulkin da waɗanda suka taimaka masu.

Ecowas, wacce ta shiga tsakanin rikicin Mali tun watan Yuni, ana sa ran za ta tattauna ta Intanet a ranar Alhamis game da abin da ke faruwa a Mali.

Nijar da shugabanta ke jagorantar Ecowas, da kuma Faransa sun kira taron gaggawa a kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya kan Mali. Wasu majiyoyi sun ce an yi taron ranar Laraba da yamma.

Ɗaukar mataki kan rikicin Mali na da matuƙar muhimmanci ga Ecowas, a cewar Etienne Faka Ba, Farfesa a Jami'ar Mali.

Masanin ya ce "Mali da ke fuskantar barazanar ƴan ta'adda idan ba a ɗauki matakai ba matsalar za ta shafi sauran ƙasashen Ecowas.

Daga riƙon ƙwarya zuwa ga zaɓe

Manifestants

Asalin hoton, Getty Images

Sojoji sun sanar da gudanar da zaɓe kuma kundin tsarin mulki ya nuna cewa idan babu shugaban ƙasa dole a gudanar da zabe cikin kwanaki 40.

Dangane da wannan wa'adi da kundin tsarin mulkin Mali ya shata, Balla Konare, masanin shari'a a Jami'ar Bamako ya yi ƙarin haske.

"Ba ma cikin yanayin da kundin tsarin mulki ya tsara inda majalisar wakilai ta nuna an samu gurbi a muƙamin shugaban kasa amma yanzu a halin da ake ciki sananne ne a doka."

"Wa'adin gudanar da zabe zai iya ɗaukar lokaci kuma muna da tanadin doka kamar lokacin (juyin mulkin da aka yi wa Amadou Toumani Toure ATT) a 2012."

Bayan juyin mulkin, an ɗauki tsawon shekara kafin Mali ta shirya zaɓen shugaban kasa: "sojoji ba za su mutunta wa'adin kundin tsarin mulki na kwana 40 saboda abubuwa sun taɓarɓare a ƙasar kuma sojoji su kaɗai ba za su iya yanke hukunci ba kan gudanar da zabe kamar yadda kundin tsarin mulki ya shata."

Amma a yanayi na rashin tabbas bayan juyin mulki musamman kan tattalin arziki da rikicin siyasar Mali, sojoji za su iya yin matsin lamba ga masu bayar da tallafi su taimaki Mali ta gudanar da zabe.

Shirya wannan zaben zai iya zama babban ƙalubale.

Ka da mu manta watsi da sakamakon zaɓen ƴan majalisa a Maris ɗin da ya gabata ne ya haifar da wannan zanga-zanga da rikici da aka shafe tsawon watanni huɗu inda kuma akwai yiyuwar zai dawo a wannan makon, a cewar (M5-RFP).

Gamayyar ƴan adawar siyasa da shugabanni addini da wasu mambobin kungiyoyin fararen hula a Mali.

Rikicin kasar Mali ya dade yana ruruwa shi ya sa mutane ba su yi mamaki ba da aka ture gwamnatin Keita
Bayanan hoto, Rikicin kasar Mali ya dade yana ruruwa shi ya sa mutane ba su yi mamaki ba da aka ture gwamnatin Keita

Tattaunawa tsakanin Sojoji da ƴan adawa

Shugabannin ƙasashen Ecowas tuni suka mayar da hankali kan rikicin Mali inda suka fito da kuɗiri na kafa gwamnatin haɗaka domin magance rikicin siyasar ƙasar.

Ƴan adawa sun yi watsi da wannan buƙatar inda suka jaddada lalle sai Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta da Firaminista sun yi murabus.

Sojoji sun hamɓarar da shugaban ne ranar Talata inda suka yi amfani da buƙatar Ecowas ta sanar da cewa za su kafa gwamnatin riƙon ƙwarya.

"Ƙungiyoyin fararen hula da masu fafutikar siyasa dukkaninsu muna gayyatarsu su zo mu tafi tare domin kafa gwamnatin riƙon ƙwarya da za ta jagoranci gudanar da zaɓe bisa sabon tsarin da zai gina sabuwar Mali," in ji Kanal Ismael Wague.

Mahmoud Dicko

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mahmoud Dicko, shugaban gamayyar M5-RFP

Ba a dai bayyana waɗanda ya kamata su jagoranci gwamnatin riƙon ƙwaryar ba, duk da a cikin jawabinsa ya ce masu fafutikar siyasa inda ake ganin yana nufin gamayyar ƙungiyoyin adawa ta M5-RFP.

"Yanzu ya yi wuri mu ce mun ji daɗi ko akasin haka," kamar yadda Soya Djike ɗaya daga cikin ƴan gamayyar adawa ya shaida wa BBC.

"Muna tunanin wasu daga cikin matsalolin da sojoji suka bayyana sun shafe mu. Amma a tsarin gwamnatin dimokuradiyya kamar yadda muka sani ba mu ƙaunar mulkin soja.

''Za mu tattauna irin rawar da ya kamata mu taka kuma muna fatan za mu cimma matsaya kan abin da muke ganin zai tabbatar da shugabanci nagari.

Ko wa zai jagoranci gwamnatin riƙon ƙwarya da sojoji ke magana? Soja ko kuma wani ɗan siyasa? Ko wani daga ƙungiyoyin farar hula? Tambayoyin da babu amsarsu har yanzu.

Map