Olaf Scholz: Tarihin sabon shugaban gwamnatin Jamus da ya gaji Angela Merkel

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz na sallama da tsohuwar shugaba Angela Merkel, bayan ta mika ragamar ofishin a hannunsa a wani kwarya-kwaryar biki da aka yi a birnin Berlin ranar 8 ga watan Disamba 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Olaf Scholz na sallama da shugabar gwamnatin da ya gada, tare da gode ma ta kan sadaukarwar da ta yi a zamanin mulkinta
Lokacin karatu: Minti 4

An rantsar da Olaf Scholz a matsayin shugaban gwamnatin Jamus, da ya jagoranci gamayyar jam'iyyu uku, bayan mulkin Merkel na shekaru 16.

Ya yi alkawarin yin aiki tukuru, domin ciyar da Jamus gaba.

Yayin da take bankwana da fadar gwamnati da ke Berlin, wanda ya kawo karshen aikin siyasarta na shekaru 31, Misis Merkel ta shaida wa tsohon mataimakin nata da ya tunkari aikin cikin nishadi da farin ciki.

Jam'iyyarsa ta matsakaicin ra'ayin sauyi ta Social Democrats za ta yi mulki kafada da kafada da jam'iyyar 'yan kasuwa ta Free Democrats.

Mista Scholz, mai shekara 63, mai tausasa harshe ya kai jam'iyyarsu ta Social Democrats ga yin nasara a zaben da aka yi a watan Satumba, inda ya zama wanda zai gaji Merkel, wadda ya yi wa mataimaki zamanin mulkinta.

'Yan majalisar Jamus sun kada kuri'ar amincewa da shugabancinsa da kuri'u 303 cikin 395, daga nan aka rantsar da shi a hukumance a matsayin shugaban gwamnatin Jamus na tara, wanda Shugaba Frank-Walter Steinmeier ya jagoranta.

Bayan zabe a majalisar, shugaban Bundestag Bärbel Bas ya tambaye shi ko ya amince da mukamin? Inda ya kada baki ya ce ''E ya amince.''

Daga nan ya sha rantsuwar kama aiki, sai dai ba kamar wadda ya gada ba, ya ƙarƙare da cewa "Allah ya taimake mu".

Tun bayan zabe, jam'iyyar Mista Scholz ta yi aiki kafada da kafada da jam'iyyar Greens da ta Free Democrats a matsayin ƙawance, wadda a ranar Talata suka rattaba hannu kan amincewar kawance.

Dukkan ministoci 16 sun sha rantsuwar kama aiki a ranar Laraba, hakan ya sanya sun shiga majalisar gwamnatin Jamus a hukumance, kuma sun hada maza da mata ne.

German President Frank-Walter Steinmeier (C) and newly appointed Ministers pose for the media during the appointment of the Federal Ministers at the Bellevue Palace in Berlin, Germany, 08 December 2021

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Gwamnatin Mr Scholz ta hada da 'yan jam'iyyun Social Democrat bakwai da Green biyar da hudu ƴan Free Democrats

Sabuwar na da burukan shirye-shirye na yaƙi da sauyin yanayi ta hanyar kawar da amfani da makamashin kwal tare da mayar da hankali kan sabon makamashi, amma ainihin babban abin da suka fi bai wa muhimmanci shi ne daƙile annobar cutar korona.

Hukumomin lafiya sun sake samun mutum 69,601 da suka kamu da ciutar cikin awa 24 da kuma mace-mace har 527 - mafi yawa da aka samu tun hunturun bara.

line

Fuskar da aka sani amma ba ta Merkel ba

Analysis box by Katya Adler, Europe editor

"Na ce 'ƙwarai'," kamar yadda Olaf Scholz ya wallafa a tuwita, jim kaɗan bayan zaɓarsa a matsayin shugaban gwamnati.

Wannan ne lokacin da ɗan siyasar ya daɗe yana jira. Bayan shafe shekara 16 da Angela Merkel ta yi, lamarin ya zama na samun wani sabon abu da zai maye tsohon.

Kauce wa X
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X

1px transparent line

Dama dai an san Mr Scholz kuma an yarda da shi a Berlin da Brussels. Ya tallata kansa ga ƴan takara da cewa shi ne Merkel Mark Two (na biyu), duk da cewa ya fito daga jam'iyya daban.

Amma ba batu ne na ci gaba ba kawai, kuma abokai da abokan kasuwanci na wannan ƙasaitacciyar ƙasa mai ɗumbin arziki za su saka ido sosai.

Gwamnatin haɗaka ta Mr Scholz wata gamayya ce da ba a taɓa gani ba a baya. ABin da ya haɗa su, sun yi ikirarin cewa, waniƙuduri ne na zamanantar da Jamus, a yayin da kuma za a ci gaba da tattalin yanayin ƙasar na tsayawa ƙyam.

Ƙalubalen da ke gabansu a yanzu:

  • Annobar cutar korona - Jamsu na tsaka da fama da annobar zagayeb na huɗu da kuma duba yiwuwar mayar da riga-kafi wajibi
  • Barazanar kutsen Rasha cikin Ukraine
  • An zargi Angela Merkel da sanya batun kasuwanci a gaba fiye da na soyasa. Ana sa ran tawagar Scholz za ta kasance mai tsauri a kan Rasha da China duk da sa ran da ake da bunƙasar tattalin arziki da zai shafi kasuwancin Jamus.

Dangantaka da Amurka za ta iya inganta a sakamakon hakan wataƙila, hakan wani abu ne aka sanya shi cikin muhimmai duk da cewa gamayyar Olaf Scholz ɗin ba ƙwararriya ba ce.

line

Bulaguron Mr Scholz na farko zai yi ne zuwa birnin Paris a ranar Juma'a. Shi da Annalena Baerbock wacce ta zama ministar harkokin waje za su mayar da martani kan fargabar da ake da ita kan mamayar da sojojin Rasha suke yi a kan iyakar Ukraine.

Duk da cewa Rasha ta yi watsi da shirin yin kutse cikin maƙwabciyarta, Angela Merkel ta yarda da batun shugaban Amurka Joe Biden da kuma shugabannin Birtaniya, Faransa da Italiya a ranar Talata, cewa za su haɗa ƙarfi wajen ɗaukar matakai iri ɗaya don mayar da martani ta hanyar ƙaƙaba takunkumai masu illatarwa kan trattalin arzikin Rasha.

Wani abu da yake a bayyane cikin matakan shi ne na yin barazana ga bututun iskar gas na Rasha da ya ratsa har Jamus, wanda aka kammala shi amma har yanzu yana jiran hukumar makamashi ta Jamus ta amince da shi.

Jami'an Amurka sun ce sun cimma yarjejeniya da Jamus cewa za a rufe bututun, wanda zai iya zama wani muhimmin shiga tsakani.

A wani saƙo na taya Mr Scholz murna, shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce yana duba yiwuwar tattaunawa mai inganci, kuma yana fatan cewa Jamus za ta ci gaba da fahimtar cewa "babu abin da ya fi sulhu alheri".

1px transparent line

A yayin da take barin ofishinta a ranar Laraba da rana, ma'aikata sun yi ta yi wa Mrs Merkel tafi a lokacin da ta shaida wa magajinta cewa ya karɓi ragamar don ci gaban Jamus.

Da yana nasa jawabin, sai ya yi magana a kan rigingimun da suka haɗe su waje guda da kuma haɗin kan da ke tsakaninsu na amana da suka samar.

Angela Merkel wacce aka fara zaɓarta a watan Disamban 1990, ta samu muƙamin minista nan nan daga shugaban gwamnatin na wancan lokacin Helmut Kohl.

Amma kuma sai ta taimaka wajen hamɓarar da shi ta zamo shugabar jam'iyyar Christian Democrat a shekarar 2000, kafin daga baya ta zama shugabar gwamnatin a shekarar 2005.

Har yanzu tana da ofishi a kusa Bundestag, a wani gida da Margot Honecker ta taɓa amfani da shi, wata mace mai ƙarfin iko a yankin kwaminisanci a gabashin Jamus a wancan lokacin.

Presentational grey line