Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƴan bindiga sun kashe mutane da dama da ƙone gidaje a Zamfara
Ƴan bindiga sun abka garin Kuryar Madaro da ke cikin ƙaramar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara inda suka kashe mutane da dama tare da ƙone motoci da gidaje.
Wasu mazauna yankin sun shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare inda suka shafe sa'o'i suna ta'asa a garin.
Wani mazaunin garin ya ce sun ƙirga gawar mutum 19 zuwa yanzu waɗanda ƴan bindigar suka kashe.
Sannan sun kwashi abinci a shagunan mutane da dabbobi.
Ƴan sandan Zamfara sun tabbatar da harin, inda suka ce sun tura jami'ansu.
An kai harin ne cikin sabbin matakan tsaro da hukumomin jihar suka ɗauka da suka haɗa da katse layukan salula da hana cin kasuwar mako-mako da hana hawan babur.
Kuryar Madaro na cikin yankin Zamfara da aka katse hanyoyin sadarwa na wayoyin salula da intanet.
Mazauna yankin da suka tsallako zuwa Gusau da aka buɗe layukan sadarwa sun shaida wa BBC cewa gida 13 maharan suka cinna wa wuta da motoci 16 da suka hada da na ƴan sanda.
"Sun kwashi abinci a shagunan mutane sannan suka cinna wa shagunan wuta," kamar yadda wani mazauni yankin ya bayyana.
Wasu hotuna daga mutanen yankin sun nuna yadda aka ƙone gidajen mutane da wasu shaguna da aka ajiye citta.
Fiye da wata ɗaya kenan da aka katse hanyoyin sadarwa a Zamfara a wani bangare na fatattakar ƴan fashin daji da suka addabi jihar kafin buɗe layukan a Gusau a babban birnin jihar a makon da ya gabata
Duk da Hukumomi na cewa ana samun nasara kan ƴan fashin dajin da ke faɗin jihar, amma kuma ƴan bindigar na ci gaba da kai hare-hare.