Zamfara Circle: Ƴan bindiga sun mamaye ƙauyuka 70 a Zamfara

Wata ƙungiya mai zaman kanta da ke hankoron ci gaban jihar Zamfara a arewacin Najeriya, mai suna Zamfara Circle ta ce ƴan bindiga sun mamaye ƙauyuka da dama na jihar.

A cikin rahoton da ƙungiyar ta fitar ranar Laraba ta ce ƴan bindiga ke iko da ƙauyuka kusan 70 a kananan hukumomi 10 na jihar da suka ƙunshi Gummi da Tsafe da Bungudu da Anka da Shinkafi da Maru da Gusau da Bakura da Birnin Magaji da Zurmi.

Haka kuma ƙungiyar ta ce mutum 364 aka kashe daga watan Fabrairun 2021 zuwa watan Agusta a Zamfara. Ƙungiyar ta kuma ce a shekarar 2021 mutum 1200 aka yi garkuwa da su a jihar kuma kusan mutum 10,000 aka raba da gidajensu.

"Gwamnati ce ke kula da ikon manyan biranen jihohi da na kananan hukumomi yayin da kuma a ɗaya ɓangaren 'yan fashi ke iko da yankunan karkara," a cewar rahoton ƙungiyar.

Ƙungiyar ta ce girman kashe-kashe da garkuwa da mutane ya kai matakin da ba a taɓa gani ba tsawon shekaru 10 da jihar ke fama da matsalar tsaro

Zuwa yanzu hukumomin jihar Zamfara ba su ce komi ba game da rahoton.

Ƙungiyar ta ce ta tattara alƙalumman ne daga wakilan da ta tura zuwa sassan ƙananan hukumomin jihar Zamfara.

A matsayinta na ƙungiya mai wakilai a ƙananan hukumomi 14 na jihar, ƙungiyar ta ce tana samun rahotannin kai hare-hare a kullum kuma a cewarta hankali ya fi karkata ga satar mutane maimakon girman matsalar tsaron da ta addabi jihar ba.

Ƙungiyar ta ce ƴan bindigar sun karɓe ikon ƙauyukan ne "ta hanyar mutane da suka watse da kuma yadda suke shiga ƙauyukan su ci karensu ba babbaka."

"Mazauna yankunan na karkara da ƙauyukan sun tabbatar da cewa babu shugabanci gaba ɗaya a yankunansu, wanda hakan ya buɗe wa 'yan fashin damar mamaye yankunan."

Kungiyar ta kuma ba da rahoton cewa babu wani sansani na ƴan gudun hijira na hukuma da aka samar a fadin jihar Zamfara duk da yawan mutanen da aka raba da gidajensu.

Ta kuma bayyana fargaba kan ɓullar wata ƙungiya a yankin Dansadau cikin ƙaramar hukumar Maru da ke yin wa'azi tana kira ga mutanen yankin su shigo ƙungiyar domin za ta kare su daga hare-haren ƴan fashi.

Ƙungiyar ta yi kira ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa dokar ta-baci a Zamfara saboda girman matsalar tsaron da jihar ke fuskanta.