Ƴan sanda sun ceto mutum 100 da ƴan bindiga suka sace a Zamfara

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya ta ce ta ceto mutum 100 da ƴan bindiga suka sace a yankin Dansadau da ke cikin mulkin karamar hukumar Maru.

Ƴan sandan sun ce mutanen sun shafe fiye da kwana 40 hannun ƴan bindagar kafin ceto su a ranar Litinin ta hanyar sa bakin tubabbu da gwamnatin jihar ta yi sulhu da su.

Kakakin rundunar ƴan sandan SP Mohammed Shehu ya shaida wa Awwal Janyau cewa ƴan bindigar sun sace mutanen ne a ƙauyen Manawa ranar 8 ga watan Yunin da ya gabata, suka yi garkuwa da su a wani daji na Kabaru fiye da kwana 40.

"Wannan ceto na daya daga cikin kokarin rundunar yan sandan jihar na ganin an kare rayuka da dukiyoyin jama'a.

"Tun lokacin da abin ya faru rundunar ta tashi tsaye da hadin gwiwar ma'aikatar tsaro da sauran masu ruwa da tsaki na al'umma da suke taimaka mana wajen samar da zaman lafiya.

"Aikin ceton ya ɗauki lokaci ne saboda yawan wadanda aka sace ɗin, dole sai an tsara an yi amfani da ilimi da dabara don gudun samun matsala wajen kuɓuto da su ɗin, kuma Alhamdulillah komai ya tafi daidai.

SP Shehu ya ƙara da cewa duk da dai mutum 100 aka sace a yanzu 80 ne da aka ceto ke hannun jami'an tsaro.

"Sauran 20 ba za su iya zuwa ba saboda yanayi na rashin lafiya ya sa ba za su iya zuwa Gusau ba sai muka miƙa su ga iyalansu don su kula da su wajen samo musu lafiya.

To ko ta yaya aka yi aka ceto su?

Gwamnatin jihar Zamfara ta daɗe tana cewa tana sulhuntawa da ƴan bindiga don samun zaman lafiya, to ko wannan hanyar aka bi aka ceto mutanen ko kuma fito na fito aka yi?

SP Shehu ya ce ba fito na fito aka yi da ƴan bindigar ba. "Hanyoyi biyu muke bi, na farko hanyoyin yaƙar waɗannan ƴan ta'adda da ba su son zaman lafiya.

"Kuma duk da damar da gwamnatin jiha ta bayar na cewa su bari su zo su tuba suka ƙi, to a wannan yanayin jami'an tsaro ba su da zaɓi sai yaƙarsu.

"Hanya ta biyu kuma akwai masu nuna cewa yaƙin ya ishe su su kan zo don sulhu kuma gwamnati kan yafe musu don a samu zaman lafiya.

"Har ma sukan taimaka wa jami'an tsaro don samar da zaman lafiya."

SP Shehu ya ce hanya ta biyu aka bi wato amfani da tubabbun ƴan bindigar don ceto waɗancan ba tare da biyan kuɗin fansa ko wani abu ba.

Abu na gaba da ya ce za a yi shi ne sake duba lafiyar waɗanda aka ceto ɗin, sai kuma a miƙa su ga shugabannin al'ummar yankunansu.

Daga cikin wadanda aka ceto ɗin mata 53 ne sai ƙananan yara 23 da kuma maza huɗu manya.

Jami'in ƴan sandan ya ce baya ga waɗannan da aka ceto ko a kwana biyu da suka wuce ma rundunar ta ceto wasu mutum 60 daga hannun ƴan bindigar a yankin Shinkafi.

Sai dai su wadannan ba su daɗe a hannun ƴan bindigar ba, "duka awa 24 suka yi ƴan sanda suka kuɓutar da su ba tare da biyan ko sisi ba har ma an miƙa su ga iyalansu," in ji shi.

Ya tabbatar da cewa a yanzu babu sauran mutane da suka yi ragowa a hannun ƴan bindigar.