Shirin kawo sojojin haya na Rasha ya tayar da hankali a Afrika Ta Yamma

Russians and Malian flags are waved by protesters in Bamako, during a demonstration against French influence in the country on May 27, 2021.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga a Bamako, babban birnin Mali sun ɗaga tutar Rasha lokacin wata zanga-zangar nuna ƙin jinin Faransa a watan Mayu
    • Marubuci, Daga Moses Rono
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Monitoring

Akwai babbar fargaba a faɗin duniya game da tattaunawar da Mali ke yi da wani kamfani mai zaman kansa na sojojin Rasha mai suna Wagner group, amma ƴan Mali da dama na ganin sojojin Rashar ba za su iya maye gurbin dakarun Faransa a kwana-kwanan nan ba.

An fara sanin ƙungiyar ne a 2014 lokacin da ta mara wa ƴan awaren da ke goyon bayan Rasha a rikicin gabashin Ukraine.

Tun bayan nan, ta yi aiki da ƙasashe ciki har da Syria da Mozambique da Sudan da Libya da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika.

A shekarar 2013, an yi wa sojojin Faransa babbar tarba lokacin da suka isa Mali bayan da masu tsattsauran ra'ayin Musulunci suka ƙwace wani tawaye sannan suka yi barazanar ƙwace iko da gaba ɗaya ƙasar.

Amma kwanan nan Shugaba Emmanuel Macron ya ce zai janye rabin yawan dakarun Faransa masu ƙarfi 5,000, kuma hakan ya zaburar da Firai Ministan Mali Choguel Maiga ya zargi faransa da watsar da ƙasarsa.

Wannan ya haifar da zazzafan martani daga Faransa, inda Ministan Rundunar Sojojinta Florence Parly ta zargi gwamnatin Mali da "yin dumu-dumu da jinin sojojin Faransa".

Shugaba Macron ya ce ya yi matuƙar mamaki da zargin, kuma ya yi Allah wadai da gwamnatin Mali wadda ya ce ba ta da "ƴancin demokuraɗiyya" bayan juyin mulki biyu da aka yi cikin ƙasa da shekara guda.

Sai dai ra'ayoyin mutane a Mali ya nuna ƴan ƙasar ba sa goyon bayan zaman dakarun tsohuwar shugabarta ta mulkin mallaka.

French soldier in Mali

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Sojojin Faransa sun fara aiki a Mali tun a 2013

Shekaru takwas bayan da sojojin na Faransa suka isa, rikicin ya bazu zuwa Burkina Faso da Nijar inda ƙungiyoyi daban-daban wasu masu alaƙa da al-Qaeda ko ƙungiyar IS ke yawo a yankin daga sansanoninsu a Hamadar Sahara.

Kusan sojojin Faransa 55 ne da ɗaruruwan ƴan Mali aka kashe.

Cikin ɓacin rai kan yadda lamarin tsaron ya taɓarɓare, ƴan Mali sun riƙa gudanar da zanga-zanga kan rundunar Faransa tare da zarginsu da ƙin kawo wani sauyi a yaƙin da ake yi da masu iƙirarin jihadi. Sun ce zaman dakarun Faransa a ƙasar mamaya ce kuma sun buƙaci su gaggauta ficewa.

Da yawa na farin cikin sojojin Rasha su maye gurbinsu.

'Rasha ba ɗaukar ɓangare'

Oumar Cissé, wani sanannen mai faftukar zaman lafiya a yankin Mopti mai fama da rikici, ya ce Rasha ƙawa ce ga rundunar sojin Mali.

"Rasha ba ta da wani buri a siyasar Mali kamar Faransa, wadda ta ke tafi da rikicin bisa burace-buracenta na tattalin arziƙi da siyasa," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Wasu masu fafutuka na cewa zaman dakarun Faransa kansa ya haifar da rikici. Faransa ta daɗe tana adawa da tattaunawa da masu iƙirarin jihadi, matakin da wasu ƴan Mali suka so.

Ba a yi wata zanga-zanga a bayyane ba kan nuna ƙin jinin Rasha amma ra'ayoyin mutane kan aiki da kamfanin Wagner ya rarrabu.

Ƙungiyar The Coordination of the Movements of the Azawad (CMA), wata gamayyar tsoffin ƴan tawayen Larabawa da Buzaye a arewacin Mali, ta ce aiki da ƴan Rashar zai zama barazana ga yarjejeniyar zaman lafiyarsu ta 2015.

Burning of a French flag

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Wasu na ganin Faransa ta daɗe tana tsoma baki a harkokin Mali

Fargabar da ake da ita a faɗin duniya kan shirin kawo Wagner na da alaƙa da rashin gaskiyar da kamfanin sojojin hayar ya yi a baya. Musantawar da gwamnatin Rasha ta yi kan alaƙarta da kamfanin ya janyo zargi.

Sai dai, ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya tabbatar da cewa Mali "ta nuna buƙatarta ga wani kamfanin sojoji mai zaman kansa na Rasha" don taimakawa waken yaƙi da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

A Afrika, an yi rahoton cewa jami'an Wagner na da hannu marar kyau a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika, inda ake tunanin wasu sojojin Rasha da ke mara wa gwamnatin da ke cikin mawuyacin hali baya, sojojin haya ne. Sannan ana alaƙanta su da laifukan yaƙi a yaƙin basasar Libya.

Ofishin harkokin ƙasashen waje na Burtaniya ya bayyana Wagner group a matsayin "mai ruruta rikici" kuma ya ce "yana amfani da rikici don cika burin kansa, kamar yadda muka gani a wasu ƙasashen da rikici ya shafa kamar Libya da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika".

Idan kamfanin ya daidaita da Mali, zai alamta faɗaɗa ayyukan sojojin Rasha a Afrika kuma babban koma baya ga ƙasashen Yamma. Tura dakarun Rasha na haya zai alamta gaggarumar rabuwa tsakanin Faransa da ƙasashen Yamma.

Russian Foreign Minister Sergei Lavrov and Malian Foreign Minister Abdoulaye Diop

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Russian Foreign Minister Sergei Lavrov (left) met Malian Foreign Minister Abdoulaye Diop at the UN general assembly last month

Ministar Faransa Ms Parly ya yi gargadi cewa "ba za mu iay samun jituwa da sojojin hayar ba." Ta zargi Firaministan Mali da "munafunci da rashin amana da rashin kamun kai" bayan da ya ce ba a tuntuɓi gwamnatinsa ba kan rage yawan dakarun Faransa a Barkhane.

Jamus da Estonia, wadanda dakarunsu suka yi aiki a ƙarƙashin tawagar dakarun yankin Turai da ke Mali da ake kira Takuba, su ma sun yi barzanar janye sojojinsu.

Ƙungiyar ƙasashen Afirka Ta YAmma Ecowas ta yi watsi da shirin kai sojojin hayar.

Ministan harkokin wajen Chadi Cherif Mahamat Zene, da shi ma ya taka muhimmiyar rawa a wajen yaki da ƙungiyoyin masu da'awar jihadi a Afirka Ta yamma, ya ce ƴan tawayen da suka kashe tsohon shugaban ƙasa Idriss Deby a watan Afrilu, kamfanin tsaro na Wagner ne ya yi musu horo kuma ya yi gargadi kan barinsu su yi aiki a yankin.

Helikwaftocin Rasha sun isa

A yayin da ake ci gaba da yin fushi da Faransa, zabar Rasha ya zama abu mai sauƙi. Alaƙa tsakanin Mali da Rasha ta inganta sosai a shekarun baya-bayan nan, musamman tun 1994 lokacin da suka ƙulla yarjejeniya wacce aka sake sabunta ta a 2019.

Ministan Tsaro Sadio Camara da wasu sojojin da suka jagoranci juyin mulki Mali duk an yi musu horo a Rasha.

A makon da ya wuce ya yi maraba da isar helikwaftocin Rasha, abin da ya bayyana a matsayin "ƙasar da ƙwance da ita ke da daɗi da a ko yaushe take inganta kyakkyawar alaƙar da ke tsakaninsu."

Ya ce hakan na cikin yarjejeniyar da suka ƙulla tun watan Disamban 2020 - tun kafin Faransa ta rage yawan dakarunta.

Shigar Rasha cikin maganar zai iya zama wani uzuri mai kyau ga gwamnatin riƙon ƙwaryar Mali don ci gaba da tsawaita wa'adinta, tun bayan ƙwace mulki da ta yi a wata mayu.

Map
1px transparent line