Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Mpappe, Ndombele, Goretzka, Sarr da Diallo

Kylian Mbappe
Bayanan hoto, Kylian Mbappe

Dan wasan gaban Paris St-German da Faransa Kylian Mbappe na daga cikin jerin yan wasan da Manchester United za ta nema a kakar badi. in ji ESPN.

An yi ta rade-radin cewa Mbappe zai koma Real Madrid da ke Sifaniya, amma har yanzu babu tsayayyar magana.

Jaridar Athletic ta ruwaito cewa dan wasan tsakiyar Faransa Tanguy Ndombele. mai shekara 24, ya fada wa Tottenham cewa ya shirya barin kungiyar.

Rahoton da 90min ta rubuta ya ce Tottenham na dab da daukar dan wasan tsakiyar Metz da Senegal Pape Matar Sarr mai shekaru 18.

Ita kuwa Wes Ham na fatan kammala cinikin Luuk de Jong daga Sevilla, in ji 90min.

Dan wasan tsakiyar Jamus Leon Goretzka ya kawo karshen jita-jitar cewa zai koma Manchester United, bayan da ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya a Bayern Munich.

Sheffield United na fuskantar abokan takara wurin karbar aron dan wasan gefen Manchester United Amad Diallo, bayan da Atalanta na Italiya sun nuna sha'awar daukarsa.

Manchester United na tattaunawa da wakilin Aurelien Tchouameni na Monaco da Faransa, a cewar jaridar Mirror.

Ga alama an kusa cimma matsaya tsakanin Leeds United da Club Brugge kan Nao Lang mai shekaru 22.

Football Insider ta wallafa cewa mai tsaron bayan Manchester United Brandon William na shirin kammala zuwansa Norwich.

Inter Milan ta ce tana da kwarin gwuiwar doke Newcastle wurin sayen dan wasan gaban Midtjylland Evander in ji jaridar Sun.