Mutumin da aka damfara N102m a auren ƙarya

- Marubuci, Daga Jonah Fisher
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Kyiv correspondent
A lokacin da ma'aikacin jinkai na Birtaniya ya kulla soyayya da wata 'yar kasar Ukraine, ya yi tunanin za su fara wata rayuwa ce mai inganci a garin Odessa, amma ina! Ashe ya yi shuka ne a idon makwarwa.
Ma'aikacin jinkan mai shekara 52 ya dade yana tsimayin wannan rana. A ranar ya zo wajen wani shakatawa na Otrada a kasar Ukraine, inda ya shiga murnar samun abar kaunarsa Irina wadda budurwa ce mai shekara 32 tana jiransa a kofar shiga wajen cin abincin Black Sea Coast, ta chaba kwalliya.
A daya gefen kuma, ga wasu mutum 60, wadanda James ya yi tunanin iyayen Irina ne da sauran baki. Fitowarsa ke da wuya, suka fara tafi.
A watan Yulin shekarar 2017 ne, wanda a yanayi na Odessa, ana tsananin zafi ne, sannan an shirya tebura a waje ne domin gudanar da shagalin biki.
Jim kadan sai James da Irina suka ratsa furanni, sannan suka karanta yarjejeniyar kulla aure a tsakaninsu.
Sai dai kash! Ranar da ta kamata ta zama ranar murna, sai aka samu akasi. A tsakar daren ranar, aka tafi da James a asibiti saboda buguwa da ya yi a abin da ya sha a wajen bikin. James ya yi aure, amma ba da matar da yake so ba, sai dai da wani tsari ne na masu shirya auren.

Wannan labari ne wani na dan Birtaniya da ya yi asarar arzikinsa mai yawan gaske da mutuncinsa, da kuma yadda tsarin shari'ar kasar Ukraine ya watsa masa kasa a ido.
Ba James ba ne asalin sunansa.
Bai bai wa kowa wannan labarin mara dadi ba a Landan, har da 'yan uwansa. BBC ta bi diddigin abun da ya faru ne ta hanyar amfani da takardun banki da sakonnin waya da kuma tambayar wadanda abin ya shafa kai tsaye.

Mai bincike
Mai binciken tsohon dan sanda ne. "Ba ma aiki da 'yan sanda, da kwalkwalwa muke amfani wajen bincikenmu," in ji shi, inda ya kara da cewa, "damfara aka yi wa wannan mutumin, za mu bi ta bayan gida domin dawo da su."
Titin da ke gaba da gidan da ofishin Mista Papinya yake a Odessa, Deribasovskaya ne, kuma nan ne babban wajen shakawata a birnin.
A titin da yamma, za ka ga mazan kasashe da dama suna zaune tare da kananan matan kasar Ukraine.
Kasar Ukraine na cikin kasashe masu fama da talauci a Nahiyar Turai. Akwai wata harkallar 'soyayya' da ake yi a kasar, inda ake hada auren karya.
James ma'aikacin jin kai ne a Landan. Wani abokinsa ya ce masa akwai bukatar ya assasa gidauniyar tallafa wa kananan yaran da suka gudo daga yankin Ukraine ta Gabas da ake yaki.
James bai saba aiki ba a kasashen waje, amma haka nan ya amince zai je, inda ya je ya fara aiki tare da tallafin tafinta mai suna Julia. A haka ya kwashe watanni yana zirya tsakanin Ukraine da Landan.
Kasancewar Lokacin sanyi ne, dusar kankara ta hana su aiki, sai Julia ta ce wa James ko zai fara fita shakatawa da kawarta Irina, mai shekara 32 daga birnin Donesk, wanda gari ne a Gabashin Ukraine.
James da Irina suka fara rayuwa, amma kasancewar Irina ba ta jin Turanci sosai, shi kuma ba ya jin harshen Rasha ko Ukraine, dole sai da tafinta kamar yadda tsarin hada 'soyayya' yake a Odessa, aikin da Julia ta yi akan kudi kusan Dala 150 kullum.

A wani sako da Irina ta aikowa James, cewa ta yi, "Kana ba ni labarai na gaskiya, ina matukar kaunarka bisa yadda kake sa ni farin ciki."
A wata shida, duk idan James ya shigo Odessa, tare yake kasancewa da 'matarsa'.
Sai dai babu cikakkiyar dama nuna soyayya kamar sumbata saboda kasancewar tafintarsu, Julia, sannan Irina ta fada masa ba ta yarda da saduwa ba kafin aure.
"Wannan ya sa na kara sakankancewa cewa tana da tarbiya mai kyau," in ji James.

Baikon James da Irina
Wata takwas kafin aurensu suka yi bikin baiko. A wani faifan bidiyo da muka gani, an nuna James da Irina suna rawa cikin murna da nishadi. An yi baikon ne a Nuwamban 2016, wata 11 bayan haduwarsu.
Tuni James ya biya kudi Irina ta fara zuwa koyon Turancin Ingilishi, wanda a tunaninsa hakan zai sa ta bi shi Landan, amma bayan ya zanta da wani jami'in Ofishin Jakadanci, sai ya gane tafiya da ita zai yi wahala.
Hakan ya sa ya yanke shawarar dawowa Ukraine domin su fara sabuwar rayuwa da irina. Sai ya sayar da gidan shi, ya ajiye aikin shi sannan suka fara neman inda za su zauna da Irina a Odessa.
"Abokaina a Landan suna ta taya ni murna."
Ashe dai daga nan ne matsalar ta fara

Gidan da za su zauna
Tura kudi daga Landan zuwa Ukraine akwai wahala. Ukraine na cikin kasashen da ake cin hanci sosai a Nahiyar Turai.
Hakan ya sa James bai yi mamaki ba da Irina ta ce ya tura kudin sayen 'gidan' dala 200,000.
Maimakon ya tura kudin a asusun ajiyar Irina, sai aka ce ya tura kudin a asusun ajiyar kamfanin wata kawarta Kristina, wadda ita ce mai shirya auren.
Duk da akwai abubuwan da bai gane ba, amma James ya tura wa Kristina kudin. Kudin na shiga, sai labari ya canja.
Irina ta fada wa James cewa banki ba za su yarda a cire kudin ba, sai an ce Kristina matarsa ce. Sai ta ce akwai tsarin da za su bi a kotu.
"Kuma aka ce baki 60 ne za su halarci bikin da kuma danginta. Ni kuma ba na so in watsa wa Irina kasa a ido. Sai kawai na amince in aura Kristina, idan na cire kudin rabuwa da ita ba zai min wahala ba."
A ranar Juma'a, 10 ga Yulin 2017, James ya yi aure da Kristina tare da amincewar budurwarsa, Irina.
A auren nawa da Kristina Irina tana ta murna da farin ciki.
Sai banki ta sakan masa kudi, amma a ranar da aka saki kudin Kristina da Irina suka fada masa cewa da dukan kudin ne aka saya gidan. Amma daga baya ya gane cewa dala 60 kawai aka saya gidan. Kuma gidnasu ne da 'matarsa' Kristina.
"Gaskiya na yi shiririta sosai," in ji James.

Bikin aure
Washegarin auren Kristina, sai James ya yi kudurin auren Irina. Tunaninsa shi ne ya auri Irina, sannan daga baya ya yi batun sakin Kristina.
Nan ma James ya kashe wasu kudaden. Kasar Ukraine karamar kasa ce, amma daga kashe dala 20,000 na auren Kristina, da 'cake' na biki na dala 1,200, kudin dakin taron da aka yi biki dala 2,0000 kayan abinci da kayan shaye-shaye kusan dala 7,500 da sauransu, an kashe kudade.
Nan da nan James ya gane cewa duk abin da aka tsara na bikin auren akwai zamba.
Ya gane cewa baki 60 da aka gayyato kamar biyansu aka yi, ita kanta 'mahaifiyar' Irina din, ashe mahaifiyar tafintansu Julia ce. Shi kadai ne kawai ya zo bikin a matsayin wanda ya zo biki na gaskiya.
Ashe budurwarsa Irina tana da miji. Takardun da BBC ta gani, sun nuna cewa Irina ta yi aure da Andriy Sykov tun Agustan 2015, wata uku kafin ta hadu da James.
Ita kanta mai shirya auren, Kristina tana da miji mai suna Denys. BBC ta gano cewa Kristina ta rabu da Denys mako uku kafin ta aura James, da tsarin cewa ita suka gama ha'intar James, za ta koma gidan mijinta Denys.

A yammacin bikin, ranar da James yake tsammanin zai samu kadaita da Irina, sai lissafi ya canja. James ya ce nan ne mahaifiyar Irina ta karya da bugar da shi kwaya.
"Ta ba ni wani abu na sha, wanda daga baya na gane akwai kwaya a ciki. Nan da nan na fara rawar jiki da har dole sai da aka dauke ni aka fitar da ni."
A asibiti James ya kwana a wannan daren. Irina ta ki bin shi zuwa asibitin, sannan washegari ta ce ya kunyata ta a gaban danginta ta hanyar buguwa.

Daga nan Irina ta fara nesa-nesa da James, sai ta turo masa sako cewa,"ina asibiti amma ba dama ka zo kusa da ni yanzu saboda ni ba matarka ba ce. A takardn aure Kristina ce matarka."
Nan ma James ya tura mata dala 12,000 domin ta yi 'jinya'
Nan ne wani abokin James dan kasar Ukraine ya shigo lamarin, inda ya fada wa James cewa kudin gidansu dala 63,000 ne, kasa da dala 140,000 da ya biya.
Nan James ya farga ya gane cewa Irina ta ha'ince dala 250,000, kusan biyu cikin kasha uku na arzikin shi.

Fafutukar ƙwato haƙƙi
James ya yi kokarin kaucewa fadawa damuwa, sai ya shiga kokarin kwatowa kansa hakki.
"Ina da takardun tura kudadena na banki da kuma sakonnin manhajar Viber, wannan ya sa na yi tunanin abubuwa za su zo da sauki."
Sau hudu yana zuwa ofishin 'yan sanda, "wani lokacin ma dariya suke min."
Idan ana so 'yan sanda su yi aiki, sai an ba su cin hanci, wanda James ya ki amincewa.
Abu daya da James ya samu shi ne da aka yanke cewa aurensu da Kristina bai yiwu ba, sai aka yanke cewa gidan da suka saya na dala 63,000 nasa ne.

Wasan bayan fage
James ya ce duk abin da ya kamata a yi, ya yi amma 'yan sanda suka ki yin komai.
"Dole kawai mu ma muka shiga yadda suke so a yi."
Dole muka biya mai bincike dala 3,000 da kuma yarjejeniyar kashi 30 na kudin da aka kwato nasa ne.
Mai binciken, Mista Papinyan ya fada mana cewa daga cikin tsarin shi akwai jefa fargaba a zuciyar wadanda yake bibbiya.
Mista Papaye ya ba James lambobin mazan Irina da Kristina. "Mijin Irina Andriy ya ce bai san maganar ba, amma ya hada mu da ita. Sai dai ta ki amsa mu, sai dai mun cigaba da ganinta a kafar neman aure cewa ta rabu da mijinta, inda ta bayyana cewa tana neman miji.
"Ban fada wa kowa ba a iyalina."
Amma me za ka ce ga duk wanda ya karanta labarinka ya ce wannan mahaukaci ne?
"Sun yi gaskiya," in ji James.
James ya ce ya amince ya bai wa BBC labarin ne kawai domin ya zama izini ga wadanda suka son shiga irin wannan 'soyayyar' a kasar Ukraine.












