NDLEA: Buba Marwa na shan yabo a wurin ƴan Twitter kan yaƙi da masu safarar miyagun ƙwayoyi

Buba Marwa

Asalin hoton, @ndlea

Bayanan hoto, A watan Janairu Shugaba Buhari ya nada Buba Marwa shugaban Hukumar NDLEA
Lokacin karatu: Minti 4

Ƴan Najeriya sun karya kumallo da shugaban Hukumar da ke hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya a kafofin sada zumunta na intanet musamman a Twitter.

Buba Marwa, wanda aka naɗa shugaban NDLEA a watan Janairun 2021, yana shan yabo daga wurin ƴan Najeriya kan yadda yake bankaɗo masu safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

A ranar Lahadi ne Hukumar NDLEA ta ce ta kama hodar ibilis da kudinta ya kai naira biliyan takwas tare da kama babban mai safarar ƙwayoyi a filin jirgin saman Legas.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an kama babban mai safarar ƙwayoyin ne da ke zama a ƙasar Brazil a ranar Juma'a 14 ga watan Mayun 2021 lokacin da yake ƙoƙarin shigo da hodar iblis a Najeriya.

Hukumar ta kuma ce ta kwace dala dubu 24,500 da aka nemi a bayar a matsayin cin hanci domin hana gudanar da bincike, matakin da ya ja hankalin ƴan Najeriya.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Tun a ranar Lahadi ƴan Najeriya ke tsokaci game da hukumar NDLEA da kuma shugabanta Janar Buba Marwa a shafin Twitter.

Sunan Buba Marwa ya kasance ɗaya daga cikin wadanda aka fi yin tsokaci a Najeriya a ranar Litinin, inda ya samu tsokaci sama da 4,000 a Twitter kawai.

Me ƴan Najeriya ke cewa?

Yawancin ƴan Najeriya na tsokaci ne kan yadda kusan kullum hukumar NDLEA ke bankaɗo masu safarar miyagun ƙwayoyi a ƙasar ƙarƙashin shugabancin Buba Marwa.

Haka kuma suna fatan ɗorewar ƙoƙarin da hukumar ke yi na ci gaba da kama masu safarar miyagun ƙwayoyi.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

@BukkyAfolabi ya ce: Ya zama dole mu jinjina wa Buba Marwa, tun da ya hau NDLEA ke aiki ba kama hannun yaro. Amma har yaushe za mu dogara da samun masu kishi kafin a ce hukumomi na aiki. Wannan matsalarmu ce!

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

@ShehuAGwandu ya ce: Wannan shi ne tasirin naɗa waɗanda suka cancanta. Sannu da aiki Buba Marwa.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

@real_okoye ya ce: Idan da dukkanin shugabannin hukumomi na aikinsu yadda ya dace, da an samu ci gaba a Najeriya.

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

@kennygee_70 tambaya ya yi cewa: Kenan ba za a binciki tsohon shugaban NDLEA ba? Waɗannan mutanen da aka kama ba yanzu suka fara ba, sun daɗe suna yi. Muna godiya Oga Buba Marwa kan shugabanci da ya dace na yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi daga ƙasarmu.

Haka shi ma a cewar @Fareed_Dbt: Ina mamakin ayyukan da shugabannin NDLEA da suka gabata suka yi a shekarun nan, Buba Marwa ya samu nasarori da yawa fiye da dukkaninsu a shekara ɗaya. Allah Ya taimake shi.

Kauce wa X, 6
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 6

Wasu sun bayyana damuwa kan makomar hukumar NDLEA da kuma ayyukanta kamar yadda @AbuBakr_MaShI ya ce: Da ma wannan ita ce babbar matsalarmu, babu tsarin da zai iya tilasta wa ma'aikata yin abin da ya kamata. A yau idan Buba Marwa ya bar NDLEA duk nasarorin da aka samu za a iya komawa gidan jiya.

Kauce wa X, 7
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 7

Yawan kama masu safarar ƙwayoyi

A tsakanin watan Mayun 2021 kusan a kullum sai Hukumar NDLEA ta ce ta kama masu safarar miyagun ƙwayoyi.

  • A ranar 16 ga watan Mayu, Hukumar ta ce ta kama kwalayen ƙwayar tramadol da darajarsu ta kai kusan naira miliyan biyar.
  • Haka kuma ta kama wiwi kilo 218.6 a jihohin Adamawa da Ondo.
  • A ranar 12 ga watan Mayu, hukumar ta ce ta kama hodar ibilis ta miliyoyin naira a jihar Legas.
  • A ranar 9 ga watan Mayu NDLEA ta kama masu safarar ƙwaya a Abuja mutum biyar tare da kama tabar wiwi kilo 75.8 a jihohin Ondo da Ribas.
  • A ranar 7 ga Mayu, hukumar ta kama hodar ibilis da aka shigo da ita daga Italiya a Abuja tare da cafke wadanda suka uyi safararta.
  • Haka ma a ranar 5 ga watan Mayu, hukumar ta ce ta kama wata mata ƴar shekara 80 da jikanyarta da safarar hodar ibilis da nauyinta ya kai kilo 192 a jihar Ondo.

'Mutum miliyan 15 ke tu'ammuli da kwaya a Najeriya'

Mohammad Buba Marwa:

Asalin hoton, NDLEA

A ranar farko da ya kama aiki a a matsayin sabon shugaban hukumar da ke yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Najeriya, Birgediya Janar Buba Marwa ya bayyana damuwa kan ƙaruwar yawan masu amfani da miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

Ya ce a 2018 an gano kimanin ƴan Najeriya miliyan 14.3 ke tu'ammuli da miyagun ƙwayoyi. Kuma a cewarsa yawancinsu ƴan tsakanin shekara 15 ne zuwa 64.

Buba Marwa ya yi gwamnan soja na Legas da Borno kuma tun naɗa shi shugaban NDLEA ya sha alwashin tabbatar da gyara tare da faɗaɗa ayyukan hukumar

Ya ce, hukumar za ta yi ƙoƙari ƙarƙashin jagorancin shi domin rage yawan tu'ammuli da ƙwayoyi sannan ya yi alƙwalin inganta rayuwar ma'aikatan hukumar.