Yaya za a yi da 'yan takarar APC masu 'shan miyagun kwayoyi' a jihar Kano?

Ganduje

Asalin hoton, DAWISU

    • Marubuci, Ishaq Khalid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja

Yanzu haka ƙurar siyasa ta sake turnuƙewa a jihar Kano da ke arewacin Najeriya, yayin da Hukumar Yaki da Ta'ammali da Miyagun Kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta bankaɗo cewa wasu 'yan siyasa na jam'iyyar APC mai mulki na shan miyagun kwayoyi.

Ta gano hakan ne bayan da aka yi wa 'yan takarar kujerun shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a jihar gwaji don tantance tafiyarsu ta fuskar ta'ammali da ƙwaya gabanin zabukanan kananan hukumomi da ake shirin yi a fadin jihar a watan Janairu mai kamawa.

Ƴan takarar jam'iyyar APC da dama ne ake zargin suna cikin wannan badaƘala ta shan miyagun Ƙwayoyi bayan gwajin na hukumar NDLEA.

Yanzu dai wasu kungiyoyin fafutikar tabbatar da shugabanci nagari da kare hakkin jama'a a Najeriya na kira ga gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma jam'iyyar ta APC da su sauya 'yan takarar shugubancin kananan hukumomin na jam'iyyar da ake zargin suna ta'amali da miyagun kwayoyin.

Kwamaret Kabir Said Dakata, na Cibiyar Wayar da Kan Al'umma da Tabbatar da Adalci, KAJA, ya ce hukumar NDLEA ''ta yi aikinta tsakani da Allah.''

Shugaban fafutikar ya ce muddin ana son gaskiya, to kamata ya yi a hana wa 'yan siyasar da lamarin ya shafa yin takara a zabukan.

Kwamaret Dakata ya ce tun da an yi bincike an gano sakamako, to kamata ya yi gwamnatin jihar da kuma shuwagabannin jam'iyyar ta APC mai mulkin jihar su dauki mataki kan 'yan takarar ta hanyar sauya su a jerin 'yan takara.

Ya kara da cewa rashin daukar mataki kansu, zai nuna cewa ikirarin da gwamnatin jihar ke yi na yaƙi da sha da fataucin miyagun kayoyi ba da gaske ba ne.

Su wane ne 'yan siyasar da aka gano suna ta'ammali da miyagun kwayoyin?

Bayanai dai na nuni da cewa 'yan siyasar da lamarin ya shafa 'yan jam'iyyar APC mai mulkin jihar ne.

Sun fito ne daga yankunan kanananan hukumomi daban-daban a jihar, wadda ke da jimillar kananan hukumomi 44.

Kawo yanzu babu cikakken bayani kan taƙamaimai 'yan siyasar da lamarin ya shafa da kuma kananan hukumominsu.

Haka zalika kawo yanzu hukumomi da kuma jam'iyyar APC ba su bayyana sunayensu ga jama'a ba.

Sai dai shugaban hukumar zaɓe ta jihar Kano wato KASIEC, Farfesa Garba Sheka, ya ce bayanan da suka samu bayan tuntuɓar jam'iyyar ta APC sun nuna cewa adadin 'yan takara da ke cikin badaƙalar ya zarce 10, ya kara da cewa da wannan na nufin suna da ''ɗan yawa'' kenan.

Amma Farfesa Garba Sheka ya ce ba shi da tabbacin ko dukkansu 'yan takarar kujerun shugabannin ƙananan hukumomi ne zalla ko kuma sun haɗa da na kujerun kansiloli.

Tun farko dai Hukumar Yaƙi da Ta'ammali da Miyagun Kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Kano ba bayar da sanarwar cewa 'yan siyasa ''fiye da shida'' ne gwajin miyagun kwayoyin ya nuna cewa suna ta'ammali da muggan ƙwayoyi.

Wakilin BBC a Kano, Khalifa Shehu Dokaji, ya ce gano 'yan siyasar na jam'iyyar APC mai mulki a badaƙalar amfani da miyagun kwayoyi ya sauya salon tafiyar siyasa a jihar, musamman a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zabukan na kananan hukumomi, wadanda su ne zabukan da suka fi kusa da talakawa.

Mene ne mataki na gaba?

ABDULLAHI ABBAS

Asalin hoton, ABDULLAHI ABBAS FACEBOOK

Bayanan hoto, Shugaban jam'iyyar APC na Kano Abdullahi Abbas ya ce bai ga sakamakon gwajin ba balle ya san su waye abin ya shafa

Bisa dukkan alamu wannan lamari na neman dagula wa jam'iyyar APC lissafi.

Hukumar NDLEA ta ce tuni ta miƙa wa gwamnatin jihar ta Kano sakamakon gwajin da aka yi wa 'yan takarar.

Shugaban jam'iyyar a jihar Kano, ya tabbatar wa BBC cewa sakamakon binciken na ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar.

Sai dai ba yi wani ƙarin bayani ba, domin a cewarsa shi bai ga sakamakon ba idonsa ba, amma da zarar ya samu sakamakon zai yi karin bayani.

To amma hukumar zabe ta jihar ta ce ba za ta karɓi sunayen 'yan takarar da aka samu da ta'ammali da ƙwaya ba.

Shugaban hukumar, Farfesa Garba Sheka, ya ce ka da ma jam'iyyar ta tunkare su da sunayen wadanda aka samu da shan miyagun ƙwayoyin, domin yin hakan tamkar ɓata lokaci ne.

Ya shawarci shugabannin jam'iyyar ta APC da su sauya 'yan takara a yankunan da lamarin ya shafa.

''Abin da muka tabbatar da shi, shi ne, lallai duk wanda aka same shi da wannan illa ba zai tsaya takara ba.''

Ya kara da cewa dole za a cire sunayensu daga jerin 'yan takara domin ''shi ne muhimmancin yin gwajin.''

Kawo yanzu babu tabbaci kan irin matakin da gwamnatin jihar ta Kano da kuma jam'iyyar APC za su dauka kan wannan batu ta fuskar sauya 'yan takarar ko kuma ladabtar da su.

Tasirin miyagun kwayoyi a siyasa

Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da ke kan gaba wajen ƙaurin suna game da amfani da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

Amfani da miyagun ƙwayoyi a fagen siyasar Najeriya dai ba wani sabon abu ba ne domin an dade ana zargin cewa wasu 'yan siyasa na bai wa wasu matasa miyagun ƙwayoyi don tunzura su cikin aikin daba ko sara-suka.

Lamarin ya kan kai ga rigingimu na siyasa wadanda kuma kan kai ga hasarar rayuka da dukiya.

Sai dai ba kasafai ake yi wa su kansu 'yan siyasar gwajin lafiya mai nasaba da amfani da miyagun ƙwayoyi ba.

Wannan ya sanya mutane da dama na cewa jihar ta kasance kyakkyawan misali game da matakin gwajin.

Wakilin BBC ya ce a jihar ta Kano matsalar ta'ammali da ƙwaya ba ta tsaya ga maza kawai ba, ta hada har da mata da 'yan mata kuma lamarin na gurbata tarbiyya, da yawan faɗace-faɗace da kan rutsa da mutanen da babu ruwansu.

Masharhanta da dama na yaba wa da yadda hukumomi suka dauki matakin yi wa 'yan takarar muƙamai na siyasa irin wannan gwaji kan amfani da kwayoyi domin zai iya sanya 'yan siyasa su shiga taitayinsu.

Amma wasu na ganin abu mafi muhimmaci shi ne tabbatar da nuna ba sani ba sabo kan gwajin da kuma sakamakonsa, sannan a tanadi tsarin da matakin zai ɗore.