An soma kama masu kalaman batsa wajen tallan maganin gargajiya a Kano

Asalin hoton, HISBAH KANO
Gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta ce ta kama masu tallata magungunan gargajiya sama da 30 saboda suna amfani da kalaman batsa.
Hukumar ta ce ta kama masu tallata magungunan ne a gurare daban-daban a fadin jhar saboda sun yi biris da gargadin da gwamnatin ta yi na haramta amfani da kalaman da basu dace ba wajen tallata magunguna.
Wakilin BBC a Kano, Khalifa Shehu Dokaji ya ce akwai rudani tsakanin masu tallan magani a jihar Kano, wadanda ke cewa gwamnatin Kano na kokarin korar su daga kasuwancin magungunar gaba daya.
Hukumar wadda ke sanya idanu kan asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu a Kano, ta ce matakin kamen ya biyo bayan haramta amfani da kalaman batsa a yayin tallan magungunan gargajiya bayan da korafe-korafen jama'a suka yi yawa kan batun.
Bai dace da dabi'armu da al'adunmu da addininmu ba
Shugaban hukumar Dr. Usman Tijjani Aliyu ya ce a karshen makon da ya gabata sun kama mutum 13.
Ya kuma ce daga bisani suka kara kama wasu karin mutum 17 da suka bijirewa umarnin hukumar duk da ja musu kunne da aka yi mu su kan amfani da kalaman na batsa a yayin tattalata hajar tasu.
Dr. Usman Aliyu ya ce, "Gwamnati ta fi shekara guda tana fada mu su cewa su daina domin wannan abu bai dace da dabi'armu ba, bai dace da al'adarmu ba kuma bai dace da addininmu ba."
"Gwamantin Kano ta dauki wannan mataki ne a yunkurin ta na tsaftace sana'ar ta masu amfani da amsakuwa da ke bin unguwani da kasuwani suna sayar da magunguna ga abokan cinikansu ta hanyar amfani da kalaman da basu kamata ba."

Asalin hoton, OTHERS
Ihu zan yi ince ga magani?
To sai dai shugaban kungiyar masu siyar da magungunan gargajiya ta hanyar amfani da amsa kuwa a jihar Kano, kwamared Hafizu Ya'u Musa Kofar Mata ya zargi gwamnati da hana su amfani da amsakuwar ma baki daya.
"Ko kadan ba ma amfani da kalaman da basu dace ba wajen talata magaunguna da muke sayarwa", wanda yace hakan tamkar hana su neman abinci ne.
"An ce ba ma maganin shawara ko maganin basir ba, ko maganin rana, ko wane irin magani kake sayar wa a fadin jihar Kano, an ce idan an ganka da mota da lasifika, ko an gan ka da baro da lasifika, ko an gan ka da mp3 da lasifika, an ce gwamnatin Kano ta han gaba daya," inji Kwamared Hafizu.
"Wannan abu gaskiya lillahi wa rasuluhi bai mana dadi ba."
Ya kuma ce da alama gwamnatin Kano "ta dauko alamar hana mu cin abinci. Inna zo, ihu zan yi in ce ga magani? Wa ma zai san na zo?"
So ake a tsaftace harkar
Amma Dr Aliyu ya mayar da martani kan wannan ikirarin na kwamared Hafizu.
Ya ce gwamanti ba ta hana masu magungunan sayar da magungunan su ba, illa dai "Mun dakatar da amfani da amsakuwa ga kowane irin mai saiyar da magani har zuwa lokacin da gwamnati ta fitar da tsari nan gaba".
"Kashi 90 cikin 100 na masu tallan magani da ke amfani da kalaman batsa da lasifika suke sana'arsu. Shi yasa muka bayar da umarnin da su dakata yin haka har zuwa loakacin da aka yi shawara."
Ya kara da cewa bayan an duba za a yanke hukuncin matakin da ya dace; "So ake a tsaftace harkar. ya zamo ana yin komai bisa ka'ida."
Matakin da hukumar sa ido kan asibitoci masu zaman kansu a jihar Kano (PHIMA) na zuwa ne mako biyu bayan da gwamantin Kano ta kafa wani kwamiti karkashin kwamishinan lafiya Dr. Aminu Tsanyawa domin kawar da matsalar amfani da kalaman da ba su dace ba da wasu 'yan kasuwa ke yi wajen tallata hajarsu.
Kuma matsalar amfani da kalaman batsa wajen tallan magungunan gargajiya a mafi yawancin arewanci Najeriya, ta dade tana ciwa mutane tuwo a kwarya.











