Mutum-mutumin NASA ya isa duniyar Mars lafiya ya fara aiko da hotuna

Asalin hoton, NASA
- Marubuci, Daga Jonathan Amos
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Science Correspondent
- Lokacin karatu: Minti 5
An kai sabon mutum-mutumi duniyar Mars.
Hukumar da ke kula da sararin samaniya a Amurka ta yi nasarar kai mutum-mutumin mai suna Perseverance zuwa wani rami mai zurfi kusa da tsakiyar duniyar wanda ake kira Jezero.
"Labari mai daɗi shi ne mutum-mutumin ya isa lafiya lau," a cewar Matt Wallace, mataimakin babban jami'in da ke kula da aikin aika mutum-mutumin.

Asalin hoton, Reuters
Injiniyoyi a hukumar NASA a California sun kaure da murna lokacin da aka tabbatar da isar mutum-mutumin.
Na'urar mai tayoyi shida za ta yi shekara biyu tana huda rami a duwatsun duniyar don gano idan an taɓa rayuwa a can.
An yi amannar cewa akwai wani gagarumin tafki a Jezero biliyoyin shekaru da suka shuɗe. Kuma idan dai an taɓa samun ruwa a waje, to akwai yiwuwar an taɓa rayuwa a wajen.
Tawagar da ke kula da tafiyar jirgin sama jannatin sun alamta cewa jirgin Perseverance ya sauka lafiya da misalin ƙarfe 8.55 na dare agogon GMT.
A baya idan aka samu irin wannan nasarar tawagar kan rungume juna ne tare da tafawa amma a yanzu dokokin cutar korona ta sa an sa gilashi tsakaninsu da juna. Sai dai sun yi ta jinjinawa juna ne ta hanyar dunƙule hannu suna ɗagawa.
Amma duk da haka farin cikinsu bai ɓuya ba. Sannan an ci gaba da tafi bayan da hotuna biyu na farko suka iso. An ɗauki hotunan ne da wasu kyamarori da ba sa ɗaukar hotuna masu inganci.
Ƙura ta lulluɓe gilashin ɗaukar hoton jikin kyamarar, amma akwai yiwuwar a ga dandaryar ƙasa a gaba da bayan jirgin.
Wani sharhi da aka yi bayan isar mutum-mutumin ya nuna jirgin ya sauka ne kusan kilomita 2 daga kudu maso gabashin yankin Jezero inda a can ne Perseverance ke shirin yin bincike.
"Muna wani wajen dandarya mai kyau. Jirgin ya ɗan karkace da kusan digiri 1.2," a cewar Allen Chen, wanda ya jagoranci tawagar. "Don haka cikin sa'a mun samu waje mai kyau da abin hawan ya sauka ya tsaya lafiya. Gaskiya ina matuƙar alfahari da tawagata da ta yi wannan aikin."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Wani babban jami'i a hukumar Nasa Steve Jurczyk shi ma ya jinjina wa nasarar: "Wannan babbar nasara ce ga tawagar. Kalli irin gagarumin aikin da suka yi da fuskantar ƙalubale masu yawa na sauka a Mars da kuma ƙalubalen annobar Covid. Babbar nasara mai ƙayatarwa."
Shi ma wani darakta a Nasa Mike Watkins, cewa ya yi "Akwai wani abu na musamman dangane da wannan lamari, wannan ne karo na farko da aka tura wani wakili daga duniyar Earth zuwa Mars.

Asalin hoton, NASA/JPL-Caltech
Sauka a Mars ba abu ne mai sauƙi ba, kuma duk da cewa Nasa ta zama ƙwararriya a harkar, duk wanda ke cikin tawagar Perseverance ya dinga yin kaffa-kaffa gabanin tafiyar ta ranar Alhamis.
Wannan ne karo na farko da mutum-mutumi mai nauyin tan ɗaya ya sauka a Mars daga hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka.
Na farko mai suna Curiosity ya sauka ne a wani yankin daban a shekarar 2012.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Tawagar za ta shafe kwanaki masu zuwa don nazartar jirgin, da duba ko wani abu na jikinsa ya lalace a sakamakon sauka mai cike da gargada a ƙasa.
Dole a ɗaga turken Perseverance da kyamarorin da ke jikinsa. Na'urar da ta kai jirgin Mars a yanzu dole a sauya ta da wata na'urar da za ta bai wa mutum-mutumin damar zagayawa a wajen.
Baya ga haka kuma, ana sa ran Perseverance zai ɗauki hotuna da dama a mako mai zuwa da kuma yadda masana kimiyya da injiniyoyi za su nazarci yanayin yadda wajen yake.

Asalin hoton, NASA
Sannan za a sa wani ƙaramin jirgi mai saukar ungulu ya zagaya duniyar don nazartarta. A cikin Perseverance akwai ƙaramin helikwafta da zai zama shi ne jirgi na farko da zai zagaya a wata duniyar - abin da ake iya bayyana shi da irin hikimar waɗanda suka ƙirƙiri jirgin sama.
Bayan wannan kuma sai batun yadda mutum-mutumin zai fara ainihin abin da ya kai shi duniyar. Zai nufi wani yanki mai ruwa na delta da tauraron ɗan adam ya gano.
Yankuna masu ruwa na delta na ginuwa ne daga koguna ta yadda suke haɗuwa ta ƙasan kogunan su yi nasu rassan. Masana kimiyya na fatan a ce hakan ne ya samar da ruwan da ake tunanin akwai a baya a yankin Jezero.
Perseverance zai kwashi samfur ɗin yankin delta sannan sai ya tafi ta inda ƙarshen babban ramin nan yake. A ta ƙarshen ramin ne tauraron ɗan adam ya gano duwatsu, waɗanda a duniyarmu ta Earth suke da kyau wajen amfani da su don gano al'amuran rayuwar mutane.
Perseverance na da na'urorin da za su iya gano bayanai kan waɗannan abubuwa har zuwa ƴan ƙananan halittun da ba a iya gani sai da madubin microscope.

Asalin hoton, NASA

Me ya sa Ramin Jezero ke da ban sha'awa?
Ramin Jezero mai faɗin kilomita 45 ya samo sunan ne daga wani gari a ƙasar Bosnia-Herzegovina. Da yaren Slavic "jezero" na nufin "tafki".
Jezero yana da duwatsu daban-daban da suka haɗa da laka da za su iya adana ƙwayoyin halitta da zai iya nuna wata rayuwa da ta gabata.
Babban abin da ya fi jan hankali shi ne kwamin da ke cike da duwatsu a wajen da wataƙila tafki ne mai tsohon tarihi a wajen. A nan ne Perseverance zai iya gano duwatsun da ake samu a ƙarƙashin teku a duniyar Earth.













