Abubuwan da za su faru a duniyar ilimin taurari na shekarar 2021

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Eva Ontiveros
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
Sabuwar shekara, tsare-tsaren kallon duniyar taurari!
Idan kai mai matukar kaunar kallon sararin samaniya a duhuwar dare ne da kuma duba abubuwan da ke faruwa a sararin samaniya, ka fara shiryawa tun daga yanzu, saboda shekarar 2021 za ta kasance cike da abubuwan ban mamaki da za su faru a duniyar sama jannati domin kowa ya ji dadi.
Ku sa ran ganin duniyar taurari irin su taurari masu wadari, da dandazon taurari mafi kusa da duniyarmu, da daukacin husufin wata, da haduwar duniyoyi, da zagayen wuta, da burbushin hasken taurari.
Kai har ma da shirye-shiryen suka a duniyar Mars a lokuta biyu, da kuma kaddamar da sabon madubin duba-rudun hangen duniyoyi, wanda zai ba mu da damar ganin duniyar da bamu taba gani a baya ba.
1. Ganin Duniyar Mercury

Asalin hoton, Getty Images
Idan ba ka taba ganin duniyar Mercury ba - duniya mafi kankanta a cikin tsarin duniyoyin hasken rana takwas da muke da su, kuma wacce ta fi kusa da duniyar Rana - ranar 24 ga watan Janairu ka iya zama abu mafi sauku a gare ka.
Za ta fiti fili a kan yammacin ..ga wadanda suke da kaifin gani, amma kuma mudubin hangen nesa zai kara taimakawa sosai.
Duniyar Mercury kan dauki kwanaki 88 kafin ta kewaya duniyar Rana, kuma a galibin wannan lokaci ba za mu iya ganin ta ba saboda walau ta buya ne ko kuma tana cikin sauran taurarin da muke iya kallo kuru-kuru a sama.
Amma zuwa karshen watan Janairu, zai kasance rabin bangaren Mercury din ne za a iya gani wanda ake kira 'dichotomy', kuma kashi 50 bisa dari ne kacal na bangaren nata duniyar Ranar za ta haska. Don haka wannan wata dama ce da za ka samu ka kalla ka kuma ji dadi a cikin wannan shekarar!
2. Tarkace masu launin shudi a bangaren kudancin duniya

Asalin hoton, Getty Images
Hangen taurari a kudancin layin ekweita ''equator', wanda ya raba duniya zuwa arewaci da kudanci, al'amari ne da masu koyon ilimin taurari da ƙwararru a fannin ke matukar kauna da darajawa.
Ga wadanda ke fara koyo, hanyar nan ta 'Milky Way' mai cike da biliyoyin taurari na da fili da matukar haske a nan, da a wasu lokuta ana iya ganin bakan gizon tarin taurari: wani layi daya ba ba ya katsewa na launkan haske iri daban-daban na haske daga tsakanin duniyar sama zuwa kasa.
"Kudu maso gabas na bangaren duniyar na dauke da abubuawa masu kyau,'' da wani Ba -Amurke na asalin Netherlands mai ilimin taurari, Bart Bok ya taba fada, wand shi da matarsa mai ilimin taurari Priscilla Fairfield suka gano wasu abubuwan ban mamak ikan tsari da sauye- sauye a duniyar taurarinmu.
Daga wannan bangare na duniya, kowa zai iya gani da idanunsa curarrun dandazon taurari (zagayayyun taurari da maganadisu ya cure su wuri guda ).
Ku nemi kallon tsakiyar taurarin, da aka fi sani da 'Southern Cross', wanda duk da cewa nan ne mafi kankanta a cikin duka taurarin 88 da suka hade wuri guda, amma kuma ya zama fitacce.
Gabas ta wannan tsakiyar za kuma ka iya kallon fasalin taurari na 'Coalsack Nebula', inda sabbin taurari ke fitowa a ko da yaushe.
Kuma tun ba a je da nisa daga wannan wuri na 'Coalsack' ba, za ka iya ganin wani akwatin da aka yi wa lakabi da J'ewell Box': wani fitaccen dandazon wasu launaka jajaye, da shudaye, da fararen taurari guda 100 cikin sauki ta hanyar amfani da karamin mudubin hangen nesa.
3. Duhun daren samaniya a lokacin hunturu daga arewacin kusurwar duniyar sama

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin hunturu na samar da dare mai tsawo, wanda hakan ke nufi masu ilimin taurarin za su iya samun isasshen lokaci wajen kallon taurarin, komai sanyin da ake yi.
Ka zabi duhun dare, kamar dai 11 ga watan Fabrairu, lokacin akwai cikakken hasken Sabon Farin Wata (idan ba a iya ganin Farin Watan, haskensa ba zai lalata shirye-shiryen da ka yi ba) kana ka yi kokarin sabarwa da idanunka kallon fiye da abinda kake tunani.
Ta hakan ne za ka yi kokarin gano wasu abubuwa masu nisa a sararin sama kamar su 'Pleiades'.
Kamar yadda ake musu lakabi da "Seven Sisters", wannan cunkusuwar taurari na da matukar haske da za ka iya ganinsu daga cikin manyan birane, muddin dai ka san ta inda za ka duba - don haka ka mayar da idanwanka wajen bangaren Kudanci da zarar rana ta fadi.
Idan ka ji kana da juriya, za kuma ka iya gawada nemo duniyar dandazon taurari ta 'Andromeda Galaxy', wacce ta ki kusa da babbar hanyar na tamu mai cike da biliyoyin taurari ta 'Milky Way', mai nisan tafiyar haske kimanin miliyan 2.5 daga duniya.
Yayin kallo daga wurin da babu gurbataccen haske, za ka iya ganin Andromeda da idanunka bude, da zarar rana ta fadi ta bagaren Yamma, kusa da dandazon taurari masu suna iri daya.
4. Taurarin Orion

Asalin hoton, Getty Images
Idan farkon farawarka ne na nazari ilimin taurari ko kuma kana son ka koyi yadda za ka iya gano cunkusuwar taurari daya kawai, me zai hana ka fara da wani abu na musamman wanda za a iya gani daga ko duka bangarorin biyu na duniya?
Orion ta fi saukin ganowa a lokacin hunturu - ko a kudu maso yammacin sararin sama idan kana zaune a Arewacin duniyar ne, ko kuma arewa maso yammaci idan kana zaune a Kudancin Duniya ne.
Fitaccen curarrun taurarin da ake kira "The Hunter" saboda yanayin fasaslinta na kirar kalangu, kana tana madauri da aka yi da taurari masu haske uku da kuma takobi.
Kallon tsaf da za a yi wa wannan wuka zai nuna cewa daya daga cikin abubuwan da ta kunsa ba tauraruwa ba ce amma Orion Nebula ce, wurin da sabbin taurari ke fitowa.
5. Sauka a Duniyar Mars

Asalin hoton, Getty Images
Muna fatan a cikin wannan shekarar za mu kalli shirin sauka a duniyar Mars ba ma sau daya ba, har sau biyu a lokuta daban-daban.
A ranar 18 ga watan Fabrairu, hukumar NASA na sa ran sauka a kan duiyar Mars mai jan launi.
An dankare dakin binciken tafi- da- gidanka da jerin kyamarori na daukar yadda sukar za ta gudana.
Za ta duba alamun baya da na rayuwar lokacin, ta kuma yi gwajin sabuwar fasaha saboda sauran ayyukan da za su yi a nan gaba.
A cikin watan Afrilu, kumbon kasar China Tianwen-1 zai same su - wanda aikinsa shi ne ya nemo makwancin ruwan da ke karkashin dandamalin kana ya dasa harsashi don saboda samun samfuri wajen dawowa duniyar doron kasa.
Hukumar lura da sararin samaniyar kasar China za ta zama ta biyu a cikin hukumomin sararin samaniya bayan NASA wajen gudanar da aiki na musamman bayan sauka a duniyar Mars.
6. Burbushin taurari na Meteor Sowers

Asalin hoton, Getty Images
A kowace shekara, sararin samaniya na samar da burbushin hasken taurari da ''gaskiyar magana abin kallo ne'' in ji wani masanin taurari Greg Brown.
Yayin da duniya ke zagayawa a kan hanyarta, ta kan bi ta cikin gajimaren kurar da dandazon taurari masu fitar da iskar gas da kuma wasu nau'ukan duwatsu suka bari a kan hanyar duniyoyinmu.
Wannan labari ne mai dadin ji a gare mu, saboda yayin da wannan burbushi ke sauka a sararinmu, suna haifar da launin kyalkalin haske masu kyau daban-daban a cikin duhun daren sararin samaniya.
Hanya mafi kyau da za ka fi jin dadin kallon ikon Allah na tartsatsin haske daga duniyar sama ita ce, ka jira har ya zuwa tsakiyar dare, a ranar da taurarin suka yi cikar kwari, tare da tunkarar wani wuri da gurbataccen hasken.
Zai fi kyau ka kalli sararin saman a lokaci guda, don haka ka shira kwanciya a kasa kana jira: '' Bayar da isassshen lokaci, da kuma samun sa'a, za ka iya tsinkayar burbushi daya kan ko wane minti ɗaya.
Ko kuma zubar ɓurɓushin mai yawa sau biyu a matsayin wata garabasa, bakin tabarau da ka saka zai kalli abubuwan mamaki na taurarin,'' in ji Brown.
"A ranar 4 ga watan Mayu, burbushin hasken taurari na Eta Aquariids zai sauka, wanda aka sani a matsayin daya daga cikin burbushin da taurarin Halley Comet suke fitarwa," har ila yau in ji Brown.
Zubar burbushi ma fi girma shi ne 'Perseids' (ranar 11 ga watan Agusta), amma idan muna so mu ga wanda suka ya fi su kasaita sai mu jira zuwa karshen wannan shekarar.
Burbushin hasken wucewar taurari na 'Geminids'' (ranar 13 ga watan Disamba) "na faruwa ne daga ɓaraguzan duwatsun sararin samaniya ba na iskar gas ta 'comet' da taurarin ke fitarwa ba, da hakan kan haifar da launukan kyalkyalin haske a duniyarmu mai kama da irin wasan tartsatsin wuta da mukan yi,'' in ji Brown.
Kuma idan kan son ka yi kyakkyawan shiri ga shekarar 2022, ka rubuta zubar gagarumin burbushin haske ka ajiye a littafinka don tunawa, saboda ana sa ran faruwarsa a farkon sabuwar shekarar mai zuwa.
7. Husufin Wata

Asalin hoton, Getty Images
A ranar 26 ga watan Mayu, Wata zai yi husufi - inda wani bangare na duniya zai lullube shi - ta wani gefen inuwar duniyar ce za ta lullube shi.
Wadanda za su kalla daga yankin Pacific Rim (yankin da ya kewaye tekun Pacific) za su iya amfani da wannan dama ta husufin watan.
Wurin kallo na farko zai kasance a birnin Hawaii, tun da zai faru ne a daidai lokacin da farin watan zai kasance a can nesa a sama da tsakiyar dare,.
Yayin da yankunan arewaci da kudanci masu nisa za su iya kallo ne kawai wasu daga cikin matakan kafin farin watan ya sake komawa daidai.
8. Husufin Rana

Asalin hoton, Getty Images
A ranar 10 ga watan Yuli Wata zai yi wa Rana inuwa - amma wannan ba zai kasance husufin da aka saba gani ba.
A wannan lokaci, Watan zai kasance daga nisan kilomita 404,300 daga duniya, wanda ke nufin inuwarsa ba za ta yi girman da za ta iya lullbe daukacin ranar ba.
A maimakon haka Watan zai wuce ta gaban tauraruwar "ring of fire" wacce za ta kasance a bayyane.
Ka tuna cewa kada ka kuskura ka kalli ranar kai tsaye, ba tare da amfani da isasshiyar kariya ba kamar tabarau na musamman na kallon husufi.
Za ka iya kallon wannan lamari na ba kasafai ba daga kasashen Canada, da arewa maso yammacin Greenland, da arewa maso gabashin Siberia… da kuma me yiwuawa a ko ina a fadin duniya - ta shafin yanar gizo.
9. Duniyoyin adawa

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da duniyoyi ke zagaya Rana, akwai lokutan da Duniyar kasa ke samun kanta kai tsaye tsakanin Rana da wata duniyar: wannan shi ne abin da masu ilimin taurari ke ce wa ''duniyoyin adawar'.'
"Duniyoyi mafi kusa da Duniyar kasa a bayyane suke ga idanu, amma ''masu adawa' suna bayar da dama sosai wajen ganinsu,'' in ji masanin ilimin taurari Dhara Patel daga cibiyar bincike ta Royal Observatory Greenwich.
"Duka duniyoyin Saturn da Jupiter za su kai ga adawa a ranar 2 ga watan Agusta,''in ji Patel, za kuma su ''kasance kusa da mu fiye da duk wani wuri a cikin wannan shekarar ".
Idan kana da mudubin hangen nesa (haka kuma za ka iya gwada kyamarar hangen nesa), wannan wata dama ce ta kallon wadannan duniyoyi da misalin karfe daya na dare," in ji Patel.
10. Kaddamar da madubin hangen sararin samaniya na James Webb Space (JWST)

Asalin hoton, Getty Images
Idan dai akwai duk wani taro da ke da masana ilimin taurari wuri guda - to na kaddamar da katafaren madubin hangen sararin samaniya ne na James Webb Space Telescope, ko JWST da ake sa ran yi a ranar 31 ga watan Oktoba.
Bayan shafe watanni ana tafiya don samun kai wa ga zagayen duniyoyi ''da kuma aiki mai cike da sarƙaƙiya saboda madubin hangen nesan ya yi wa jirgin rokar girman gaske," in ji masanin taurari a cibiyar Royal Observatory Greenwich, Ed Bloomer.
Wannan na da matuƙar kyau saboda zai bai wa masana kimiyya damar gudanar da ''bincike kan wasu taurari da kuma curewar taurarin wuri guda, da sauran yanayin zamantakewar taurarin duniyoyin," in ji Bloomer.
Ba daidai ba ne a yi tunaninsa a matsayin maye gurbi ga - tsohon madubin hangen nesan Hubble Space, amma yana nuna cewa zai taimaka wa injiniyoyi masu tasowa, da kuma wasu muhimman ayyuka da ka iya tasowa nan da wasu shekaru masu," Bloomer. Ya kara fada.
Ana dai fatan madubin na JWST zai samar da sabbin hotunan da ''ka iya zama masu kyau kamar irin wadanda muka samar a baya," in ji masanin.











