Nasarori da matsalolin da aka sha samu a zuwa duniyar Mars
Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:
Ana ƙoƙarin sauƙa a duniyar Mar har sau biyu a shekarar nan ta 2021 - a tsakanin ƙasashen Amurka da China.
Jirgin sama jannati na hukumar sararin samaniya ta Amurka Nasa na shirin sauka a duniyar Mars ranar 18 ga watan Fabrairu.
Idan har aka yi nasara, to zai zama shi ne babban abin hawa da aka ta ba aika wa wata duniyar.
Sannan a watan Mayu ko Yuni, jirgin sama jannati na Tianwen-1 shi ma zai gwada sauka.
Sai dai ba dukkan jiragen da aka taɓa aika wa Mars ba ne suka samu sauka a can.