Maza biyar da matansu suka fi su shahara a duniya

Kamar yadda maza suka shahara kuma suka mamaye siyasar duniya haka ma mata.

A wani bincike na Farfesan jami'ar Stanford Alvin Roth kuma wanda aka bai wa lambar yabo ta Nobel ya nuna cewa duk da irin nasarar da ɗaya daga cikin ma'aurata ya samu cikin aure, dukkaninsu za su iya samun farin ciki idan suka fahimci juna.

Wannan tunanin yana da tasiri musamman ga mazan da suka samu nutsuwa a tare da matansu da suka fi su shahara.

An ƙarfafa wannan tunanin na Farfesa Rotha wani bincike a 2015 mai taken "Nazari kan yadda mazaje masu ruwa da tsake ke tasiri ga nasarar matansu."

A binciken an kammala cewa goyon baya da mazaje ke ba matansu yana ƙara ba su damar samun nasara da shugabanci.

Don haka ga mata biyar bisa goyon baya da suka samu suka fi mazajensu shahara a duniya:

Douglas Emhoff mijin Kamala Harris

Douglas Emhoff mijin Kamala Harris

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kamala Harris da mijinta Douglas Emhoff

Kamala Harris ta zama mace ta farko kuma baƙar fata ta farko da ta zama mataimakiyar shugaban Amurka.

Ta kafa tarihi, duk da cewa mijinta Douglas Emhoff shi ma ya kafa na shi tarihin.

Gwamnatin Biden ta buɗe masa shafin Twitter a hukumance, inda Mista Emhoff ya zama namiji na biyu mafi girma a matsayinsa na mai gidan mataimakiyar shugaban ƙasa a tarihin Amurka. Kuma Bayahude na farko mijin mataimakiyar shugaban ƙasa.

An haifi Douglas Emhoff a Brooklyn kuma iyayensa Yahudawa ne, Barbara da Michael Emhoff.

Ya yi karatu a jami'ar jihar Califonia, Northridge inda ya kammala digirinsa na farko da kuma karatun shari'a.

Ya yi aiki a kamfanoni da dama na shari'a da kuma kamfaninsa kafin ya zama abokin hulɗar DLA Piper.

Ya kuma koyar a matsayin Farfesa a ɓangaren shari'a a Jami'ar Georgetown

Ya kasance wani abin misali cewa maza na iya kasancewa a wani matsayi na ƙarfafawa mata guiwa.

Joachim Sauer mijin Angela Merkel ta Jamus

Joachim Sauer mijin Angela Merkel ta Jamus

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Angela Merkel da mijinta Joachim Sauer

Joachim Sauer Farfesan kimiyya ne a Jami'ar Humboldt da ke Berlin.

Yana ɗaya daga cikin membobin kwamitin amintattu na gidauniyar Friede Springer, tare da tsohon shugaban kasar Jamus Horst Köhler da sauransu.

A 1998 ya auri Angela Merkel wacce ita ma masaniyar kimiya ce. Ya taɓa aure da ƴaƴa biyu kafin ya auri Merkel wacce ita ta taɓ aure kafin ta aure shi.

Lokacin da Angela Merkel ta zama shugabar gwamnatin Jamus a 2005, Sauer ya zama namiji na biyu mafi girma a Jamus bayan shugaban ƙasa.

An haife shi ne a 1949 a Hosena Jamus, kuma ya zurfafa bincike ne a fannin ilimin sinadarai (Chemistry) a Jami'ar Humboldt da ke Berlin inda ya kammala digirinsa na uku a 1974.

Sauer ya zama cikakken Farfesa a 1993 a Jami'ar Humboldt a Berlin.

Saboda shaharar da matarsa ta yi a fagen siyasa, Sauer ya fi samun kulawar kafofin yaɗa labarai fiye da yadda yake samu a bincikensa na kimiyya.

Lokuta da dama ya ce sha cewa bai damu da nuna kansa ba, kuma ya ki amincewa ya tattauna da kafofin watsa labarai kan fannin siyasa.

Ikemba Iweala mijin Ngozi Okonjo-Iweala

Ikemba Iweala mijin Ngozi Okonjo-Iweala

Asalin hoton, @NOIweala

Bayanan hoto, Ngozi Okonjo-Iweala da mijinta DR Ikemba Iweala

Dakta Ikemba Iweala likita ne asalin jihar Abia daga Umuahia. Ya yi karatu a Jami'ar Ibadan, Najeriya.

Ya samu horo kan fannin tiyata a Birtaniya inda ya yi aiki a asibitoci da dama na Ingila.

Ya kuma yi aiki a asibitin Jami'ar George Washington a Washington DC.

Dakta Iweala ya tabbatar da shi mutum ne mai kyautatawa iyali duk da aikinsa na likitanci mai cin lokaci.

Zai kasance mai farin ciki da auren Ngozi Okonjo-Iweala, da ta riƙe muƙamin ministar kuɗi da kuma ministar harakokin ƙasashen waje.

Ta kasance mamba a kwamitin gudanarwar kamfanonin ƙasashen waje da suka haɗa har da Twitter da ARC da GAVI da sauransu. Yanzu ita ce mace ta farko kuma ƴar Afirka da ta zama shugabar ƙungiyar kasuwanci ta duniya (WTO).

Sun haifi ƴaƴa huɗu, mace ɗaya maza uku.

Peter Murrell mijin Shugabar Gwamnatin Scotland, Nicola Sturgeon

Peter Murrell mijin Firaministar Scotland Nicola Sturgeon

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Nicola Sturgeon da mijinta Peter Murrell

Peter Tierney Murrell shi ne babban jami'in jam'iyyar SNP ta Scotland da matarsa Firaminista Nicola Sturgeon ke jagoranta.

An haife shi a 1964 a Edinburgh, kuma ya yi karatu a Jami'ar Glasgow a Scotland.

Murrel ɗn siyasa ne inda tun 1999 yake rike da muƙamin babban jami'in jam'iyyar Scottish National Party, kuma ana ganin jagorancinsa ne ya kai ga nasarar da ta samu a zaɓen 2007.

A 2010 ya auri Nicola Sturgeon, amma tun a 1988 suka fara haɗuwa a wani taron matasan jam'iyyar SNP da Murrell ya haɗa. Tun 2003 suka yi baiko.

Clarke Timothy Gayford, mijin Firaminista Jacinda Ardern

Mijin Firaminista Jacinda Ardern yana renon ƴar su

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mijin Firaminista Jacinda Ardern yana renon ƴarsu

Clarke Gayford, mai shekara 44, ɗan jarida ne kuma mijin Firaiministan Zealand Jacinda Ardern.

Ya fara karatunsa a makarantar Palmerston North Boys' High. A 1995, ya tafi Jami'ar Otago inda ya kammala karatun digiri.

Ya kuma tafi makarantar koyon aikin yaɗa labarai ta New Zealand Broadcasting School a Christchurch, New Zealand. Daga can ne ya fara aikin yaɗa labarai a Cow TV (1999) zuwa Channel 9.

A 2003, ya fara aiki yaɗa labarai gadan-gadan a kafar da ke yaɗa kaɗe-Kaɗe ta C4 channel, inda yake gabatar da shirin matasa.

Daga nan kuma ya ci gaba da aikin yaɗa labarai a fannoni da dama ciki har da shirin kamun kifi wanda aka nuna a ƙasashe sama da 35.

Rahotanni da dama sun ce a 2019 Gayford ya nemi auren Ardern. A cewar kafar yaɗa labaran New Zealand, ya sha raka Ardern ƙasashe da dama ciki har da taron shugabannin ƙasashe rainon Ingila a London.

Wannan maƙala ce daga Olalekan Adigun mai sharhi daga Lega, amma BBC ta yi wasu sauye-sauye