Fatima Isaacs: Matar da ta kwato wa mata Musulmai sojoji 'yancin sanya hijabi a Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Legal Resources Centre
Rundunar sojin Afirka ta Kudu ta sauya tsarin tufafin jami'anta ta yadda sojoji mata Musulmi za su samu damar sanya hijabi.
Hakan wata nasara ce ga Manjo Fatima Isaacs, wadda ta kwashe shekaru uku tana shari'a da rundunar sojin domin ganin an tabbatar mata da 'yancinta na addini ta hanyar sanya hijabi a karkashin hularta ta soja.
A makon jiya rundunar sojin ta janye shari'ar da take yi da Manjo Isaacs lamarin da ya tabbatar mata da sauran sojoji Musulmi da damarsu ta sanya hijabi.
Ta fuskanci kora daga aiki a kan "bijire wa doka da kuma umarni" ta hanyar kin cire hijabin da take sanyawa.
Manjo Isaacs, wadda ke aiki a matsayin jami'ar bincike kan masu mutuwar farat-daya a asibitin sojoji, ta shaida wa jaridar Cape Times cewa hakan wata nasara ce ba wai kawai gare ta ba, har ma da sauran mutanen da ke "nunawa wariya" saboda addininsu.
"Muna zaune a kasar da ke bin tafarkin dimokradiyya abin da ke nufin bai kamata a rika nuna bambanci ga kowa ba bisa addinin da yake bi. Na yi amannar cewa addini shi ne ginshikin tarbiyya ga kasa. Wannan nasara ce mai cike da muhimmanci," a cewarta..
Ta kuma gode wa Cibiyar Legal Resource Centre (LRC), wato kungiyar da ta taya ta fafutukar ganin ta samun 'yancin sanya hijabi a 2019.
Bayan rundunar sojin ta janye karar da ta shigar a makon jiya, an amince cewa Manjo Isaacs za ta iya saka matsattsen dan-kwali, wanda bai rufe kunnuwanta ba, kuma fari - kodayake tsarin tufafin sojin ba zai sauya ba a hukumance.
Daga nan ne kungiyar ta LRC ta shigar da kara a kotu, inda ta ce tsarin tufafin rundunar sojin Afirka ta Kudu ya ci karo da kundin tsarin mulkin kasar.
Daga bisani, rundunar tsaron kasar ta "gyara tsarin sanya tufafi na addininta domin bai wa Musulmai mata damar sanya hijabi a saman kakin sojinsu," a cewar sakon da LRC ta wallafa a Tuwita..
"Ba za mu ci gaba da bibiyar wannan batun ba saboda a halin yanzu tsarin rundunar tsaron kasa ba zai nuna bambanci ga Musulmai mata da ke aikin soji ba."
Bayan kawo karshen mulkin fararen fata a Afirka ta Kudu a 1994, kasar ta sauya kundin tsarin mulkinta ta yadda ya kasance daya daga cikin mafi sassauci a duniya.












