Fulani sun yi zargin kashe iyalansu a harin da 'yan banga suka kai musu a jihar Oyo

Asalin hoton, Getty Images
Wasu Fulani makiyaya da ke zaune a jihar Oyo ta kudu maso yammacin Najeriya sun yi zargin cewa wasu 'yan baga da ke ikirarin kare kabilar Yarbawa sun kai musu hari ranar Juma'a.
Harin ya yi sanadin mutuwar matar Malam Aliyu dan sarkin Fulanin jihar ta Oyo, a cewarsa.
Wannan hari na zuwa ne a yayin da wa'adin da jihar Ondo ta bai wa Fulani makiyaya su bar dazukan jihar ko kuma a tliasta musu yin hakan ya zo karshe.
Da alamu kuma an fara aiwatar da wannan barazana, domin wasu Fulani makiyaya da ke zaune a garin Igaga na yankin karamar hukumar Ibarapa ta jihar Oyo, sun yi zargin an kai masu hari ranar Juma'a da yammacin, har an kashe wasunsu, kuma an kona masu rugage da duk kayan da su ka mallaka.
Gwamnatin jihar Oyo ta ce ba ta bayar da umarnin a kai wa Fulani makiyaya hari ba, kuma ba ta goyon bayan hakan.
Amma duk da haka tana kokawa kan matsalar masu aikata miyagun laifuka da ke raɓewa da makiyaya a jihar.

Asalin hoton, Reuters
'Kowa ta kansa ya ke a wannan lokaci na firgici'
Bayanai daga garin Igaga sun ce Fulani makiyaya sun tsere daga wuraren da suke zaune, kuma sun sami mafaka a cikin jeji.
Aliyu, dan sarki Fulanin jihar ta Oyo, ya yi mana karin bayani ta waya, daga wani waje da ya samu ya boye.
"Yanzu wallahi ina cikin daji, cikin wani rafi. Yarabawa 'yan ƙasa ne suka kai mana hari daidai ƙarfe huɗu na yamma," in ji shi.
Ya kuma bayyana wurin da aka kai mu su harin, "An kai mana harin ne a Igaga na jihar Oyo."
Ya ce maharan sun isa wurin da suke dauke da bindigogi, kuma sun rika yin harbi na kan mai-uwa-da-wabi.
A cewarsa: "An ƙona mana gidaje, an ƙona motocin sarki. Yaran da ke cikin ɗaki an ƙona su da ransu. Wasunsu an sare su, sai wasu da aka harbe da kuma wadanda aka ƙone."
Aliyu dan Sarkin Fulani ya kuma ce ba zai iya tantance yawan wadanda aka kashe ba: "Idan na ce ma ga yawan mutanen, na yi ma ƙarya ne."
Amma ya ce shanunsu na cikin daji wajen kiwo. Saboda haka ne ya ce bai san ko lamarin ya shafe su ba.
Ya shaida wa BBC cewa kowa ta kansa yake a wannan lokaci na firgici da tashin hankali.
Kuma cikin ɗimauta da kuka, ya ce an kashe musu mutane:
"An kona min gida, an kashe min matata, da ɗan da take tare da shi. Tana cikin ɗaki aka share ta yayin da take goyon karamin yaro a bayanta."
Saboda irin tashin hankalin da ya gani, Aliyu bai iya ci gaba da bayyana wa BBC halin da suke ciki ba, domin ya fashe da kuka, yana maimaita cewa, "an kashe mana mutane, an kashe komai da komai a nan"
Aliyu dan Sarkin Fulanin jihar Oyo tun da farko ya shaida wa BBC cewa sun kwashe fiye da shekara hamsin suna zaune a wannan gari na Igaga.
Martanin gwamnatin Jihar Oyo
Yayin da wakilin BBC ya tuntubi kwamishinan yaɗa labarai na jihar ta Oyo, Dakta Wasiu Olatubosun, kwamishinan ya nisantar da gwamnatin jihar da wannan hari da aka kai wa Fulani makiyaya da yammaci Juma'a.
Ya ce gwamnatinsu ba ta goyon bayan wani mutum ko mutane su kai wa Fulani makiyaya hari a duk fadin jihar.
Matsalar kawai da su ke ta tsokaci kan ta ita ce ta batun masu fakewa da makiyayan suna aikata miyagun laifuka, kamar sace mutane don neman kuɗin fansa, da fashi da makami, da kai hare-hare da makamai, da dai sauransu.
Saboda haka, kwamishinan yada labarai na jihar ta Oyo ya kara da cewa yayin da duk wani mutum ya yi wa Fulani waccan barazana, cewa zai kawar da su daga jihar, gwamnatin jihar ta yi amanna hukumomin tsaro za su dauki matakin da ya dace, tun kafin a kai ga tafka wannan ta'asa a yau.











