Sunday Igboho: Babban sufeton ƴan sanda ya ce a kamo mutumin da ke farautar Fulani a Oyo

,

Asalin hoton, SUNDAY IGBOHO

Babban Sifeton Ƴan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayar da umarni ga kwamishinar ƴan sandan jihar Oyo, Mrs Ngozi Onadeko, da ta kamo mai fafutikar kare haƙƙin Yarabawa Chief Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a shirin BBC na Ra'ayi Riga, inda ya ce ba da daɗewa ba ya kammala magana da babban sifeton ƴan sandan, kuma ya shaida masa cewa ya bayar da umarni a kamo Igboho kuma a kai masa shi Abuja.

Igboho dai na daga cikin abubuwan da ake tattaunawa a shafukan sada zumunta a Najeriya a ranar Juma'a tun bayan da ya sake ziyartar garin Igangan da ke Ƙaramar Hukumar Ibarapa ta jihar kuma ya jaddada cewa duka Fulanin da ke zaune a jihar ta Oyo dole su tashi muddun aka ci gaba da garkuwa da mutane.

Ko a makon da ya gabata sai da Igboho ya ziyarci al'ummar Fulanin da ke zaune a Igangan ɗin, inda ya ba su kwanaki bakwai da su bar jihar, inda yake zargin Fulanin da ke yankin da kitsa garkuwa da mutane da kashe-kashe da kuma wasu laifuka da ke faruwa a yankin, amma a komawarsa ta wannan karon, ya yi musu ƙarin haske kan abin da yake nufi.

Malam Garba Shehu ya ce suna fuskantar matsala wajen hukunta masu laifuka saboda yadda kungiyoyin da ke ikirarin kare hakkin bil'adama suke yi wa gwamnati katsalandan.

Garba Shehu dai ya ƙara da cewa umarnin da babban sufeton ƴan sandan ya bayar a halin yanzu, shi ne a kamo Igboho a kai shi Abuja sa'annan a gurfanar da shi a gaban kotu.

Ko a farkon makon nan sai da gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya bai wa makiyaya da ke dazukan jihar wa'adin kwanaki bakwai su bar dazukan.

Wannan lamari ya jawo ce-ce-ku-ce matuƙa a Najeriya inda har sai da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan wannan lamari inda ya gargaɗesa kan wannan matakin.