Muhammadu Buhari: Shugaban Najeriya ya gargadi gwamna Rotimi Akeredelu na Ondo kan korar makiyaya

.

Asalin hoton, Presidency/Akeredolu

A karon farko, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mayar da martani kan matakin da gwamnan Ondo da ke kudancin kasar, Rotimi Akeredolu ya ɗauka na korar makiyaya daga dazukan jihar.

A wani saƙo da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan kafofin watsa labarai Malam Garba Shehu ya aika wa manema labarai, ya bayyana cewa fadar shugaban ƙasar na sane sannan tana bibiyar abubuwan da ke faruwa musamman kan batun matakin da gwamnan na Ondo ya ɗauka.

A cewarsa, rashin daidaito a irin yadda ake aika saƙo ne yake jawo ce-ce-ku-ce game da ainihin saƙon da ake so a aika wa jama'a.

"Babu wani abin cewa illa kira ga ɓangarorin su yi sulhu da kuma neman gwamnatin jihar da kuma shugabancin Fulani su ci gaba da tattaunawa domin fahimtar juna domin kawo ƙarshen rashin tsaron da ake fama da shi a jihar cikin sauri," in ji shugaban.

Shugaban ya yaba wa gwamna Akeredolu inda ya ce a matsayinsa na babban lauya kuma tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi ta Najeriya ba sa tsammanin zai kori dubban makiyaya waɗanda suka shafe rayuwarsu a cikin jihar sakamakon ayyukan wasu ɓata-gari da ke aikata laifuka a daji.

Shugaba Buhari ya kuma ce idan da gaske ne, lallai ƙungiyoyin kare haƙƙi na kan gaskiyarsu ta nuna damuwa kan cewa wannan matakin zai iya tayar da zaune tsaye.

Sai dai Garba Shehu ya shaida wa BBC Hausa cewa suna jira su gani ko gwamnan zai yi biyayya ga umarnin Shugaba Buhari idan ba haka ba za su ɗauki mataki na gaba.

Ya kuma ƙara jaddada cewa garkuwa da mutane da fashi da makami da satar dabbobi laifi ne kuma ko su wa ke aikata irin laifukan bai kamata ana yi wa wata ƙabila kuɗin goro ba ana siffanta ta da wani laifi na musamman.

Makiyayi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana zargin makiyaya da satar mutane domin karbar kudin fansa, sai dai sun sha musanta zargin

A makon nan ne gwamnan jihar ta Ondo ya bai wa makiyaya da ke dazukan jihar wa'adin kwanaki bakwai su bar dazukan.

Gwamna Akeredolu ya ce a matsayinsa na babban mai kula da sha'anin tsaro na jiharsa, ba zai zura ido ba ya bari ana ci gaba da aikata laifuka.

A cewarsa, sun dauki matakin ne da zummar tabbatar da tsaron rayuka da na kaddarori a jihar ta Ondo yana mai bayar da umarni ga jami'an tsaro su tabbatar da an aiwatar da dukkan umarnin da ya bayar.