Yadda za ku shigar da koke ga ƴan sandan Najeriya ta intanet

Asalin hoton, @PoliceNG
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ƙaddamar da shafin intanet da zai dinga bayar da rahotanni game da masu aikata laifuffyka ta Intanet.
Cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Alhamis ta ce matakin wani ɓangare ne na ƙokarin sauƙaƙe wa jama'a turo da rahotannin aikata laifuka.
Rundunar ta ce hakan zai taimaka wajen gaggauta ganowa da kamawa da gudanar da bincike da kuma hukunta masu aikata laifuka.
Hanyoyin shigar da rahoto
Rundunar ta ce a kowane lokaci kuma a ko ina mutum yake zai iya bayar da rahoton laifukan da suka shafi intanet a shafin da ta buɗe.
Za a iya samun shafin idan aka danna nan .
Sannan za a iya shigar da koke game da wata matsala ko kan aikin ƴan sanda a shafin.
Sai dai rundunar ta ɓukaci a gabatar da sahihan bayanai tare da ƙauracewa bayar da bayanan ƙarya a lokacin da suke tura rahoto a shafin.
Babban Sufeton ƴan sandan Najeriya M. A Adamu, ya ce za a tabbatar da amincin duk rahotanni da korafe-korafen da aka shigar a shafin da kuma ɓoye sunayen waɗanda suka tura tare da ba su kariya.
Shafin zai dinga bayar da bayanai

Asalin hoton, @PoliceNG
Sabon shafin rundunar ƴan sandan da aka samar zai dinga bayar da sabbin bayanai da nasarorin da ƴan sanda suka samu.
Haka kuma shafin zai kasance hanyar wayar da kan jama'a kan batutuwan da suka shafi laifukan da ake aikatawa ta intanet.
Da kuma hanyoyin da mutane za su bi domin tsira daga hare-haren masu kutse a intanet.











