Coronavirus; Abin da aka sani game da sabon riga-kafin cutar korona

A person holding an ampoule

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga James Gallagher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakili kan harkokin Lafiya da Kimiyya

Fatan da ake yi na samun riga-kafin Covid-19 ya samu gagarumin ci gaba, bayan da aka sanar da samun sakamako "mai girma".

Ƙwarya-ƙwayar bincike ya nuna cewa riga-kafin da kamfanin Pfizer and BioNTech ya samar zai iya hana kashi 90 cikin dari na mutane kamuwa da Covid-19.

Wacce nasara Pfizer/BioNTech suka cimma?

Sune na farko da suka gabatar da bayanai a matakin ƙarshe na gwajin cutar.

Wannan mataki ne mai matukar muhimmanci a yunkurin samar da riga-kafin, inda a wasu lokutan riga-kafin ba sa yin nasara.

Riga-kafin sun bi matakai daban-daban, wadanda suka hada da yin allurar wani ɓangare na ƙwayoyin halittar cutar ga mutane da zummar horas da garkuwar jikinsu.

An yi wa kimanin mutum 43,000 allurar riga-kafin, kuma hakan bai haifar da wata matsala ba.

Don haka yaushe za a samar da riga-kafin?

Kamfanin Pfizer ya yi amannar cewa zai samar da kwalba miliyan 50 na allurar riga-kafin daga yanzu zuwa ƙarshen shekarar nan, sannan ya samar da kwalaba bliyan 1.3 zuwa shekarar 2021.

Birtaniya za ta samu kwalaba miliyan 10 na allurar zuwa karshen 2020, yayin da tuni ta bukaci a ba ta karin kwalaba miliyan 30.

Yin allurar riga-kafin ya dogara ne da farko kan inda cutar Covid ke yaduwa lokacin da aka samar da riga-kafin da kuma rukunin mutanen da ta fi yi wa tasiri.

Alal misali, Birtaniya ba ta yanke shawara kan yadda za ta bayar da muhimmanci ga ma'aikatan lafiya da ke aiki da mutane da suka fi kasadar kamuwa da cutar ba, ko kuma wadanda ska fi hatsarin galabaita bayan sun kamu da cutar.

A taƙaice, za a fi mayar da hankali wajen yin riga-kafin ga mutanen da suka wuce shekaa 80 a duniya, da ma'aikatan lafiya.

Yawan shekaru na cikin abubuwan da suka fi sanyawa a kamu da Covid, don haka za a fi mayar da hankali kan mutanen da shekarunsu suka ja.

Masana harkokin lafiya da dama na ganin allurar riga-kafin ba za ta samu da yawa ba sai tsakiyar shekarar 2021.

Waɗanne sauran riga-kafi ake fafutukar samarwa?

Ana sa ran samun ƙarin sakamako na binciken da wasu rukunin masanan ke yi game da riga-kafin cutar ta korona nan da makonni ko watanni kaɗan masu zuwa.

Akwai hukumomi 10 da suka kai babban mataki na gwajin riga-kafin cutar korona

Manya daga cikinsu su ne:

  • Jami'ar Oxford da riga-kafin AstraZeneca da ke Birtaniya
  • Moderna da ke Amurka
  • CanSino da ke aiki da Beijing Institute of Biotechnology a China
  • Gamaleya Research Institute da ke Russia
  • Janssen
  • Beijing Institute of Biological Products and Sinopharm da ke China
  • Sinovac and Instituto Butantan da ke Brazil
  • Wuhan Institute of Biological Products and Sinopharm da ke China
  • Novavax da ke Amurka

Yana da kyau a sani cewa akwai nau'i huɗu na cutar korona da ke yawo a jikin ɗan adam. Suna haifar da mura kuma babu riga-kafinsu.

Akwai nau'ukan riga-kafin korona daban-daban?

Manufar samar da riga-kafi ita ce a nuna wani bangare na cutar ga garkuwar jiki da zummar gano yadda ta yi kutse cikin jiki sannan ya koyi yadda zai yake shi.

Amma akwai hanyoyi da dama da za a iya yin hakan kuma masu bincike suna yin amfani da hanyoyi da dama wajen yin hakan.

Dukkan riga-kafin Pfizer da Moderna suna sanya kwayoyin halittar cutar korona. Da zarar riga-kafin ya shiga cikin jiki, zai samar da sinadarin proteins da za su horas da gangar jiki. Wannan sabon tsari ne fil.

Riga-kafin Jami'ar Oxford da na kasar Russia suna daukar kwayoyin cutar da ba su da matsala wadanda aka sanya a jikin birai, sannan su jirkita kwayoyin halittarsu domin su yi kama da cutar korona, da fatan samun sakamako.

Me ya kamata a yi?

  • Dole a ɓullo da hanyar samar da riga-kafi mai girma wadda za ta kai ga samun biliyoyin riga-kafi
  • Dole masu sanya ido su amince da riga-kafi kafin a bai wa jama'a
  • Daga ƙarshe, za a fuskanci ƙalubale da dama wajen yin ainihin riga-kafin ga ƙasashen duniya

Mutum nawa suka kamata a yi wa riga-kafi?

Yana da matuƙar wahala a san hakan ba tare da sanin tasirin da riga-kafin zai yi ba.

Ana tsammanin za a yi riga-kafin ga kashi 60-70 cikin dari na al'ummar duniya domin a tsayar da yaduwar cutar cikin sauki.

Me ya sa ake buƙatar riga-kafin?

Idan kuna so rayuwarku ta dawo kamar yadda take a baya, to akwai buƙatar samun riga-kafi.

Ko da yake galibin mutane na cikin kasadar kamuwa da cutar korona. Dokar kulle da sauran matakan kariya ne suke rage yawan mutanen da ke mutuwa sanadin cutar.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus