Shafin Instagram da ke gyara aurarrakin da bambancin addini ya raba

Martina Roy da Zain Anwar lokacin bikin aurensu

Asalin hoton, Aikin Soyayyar India

Bayanan hoto, Martina Roy Kirista ta auri Zain Anwar Musulmi, a watan Satumba bayan shafe shekaru bakwai suna jiran amincewar danginsu

A kasar Indiya, inda ake bai wa asali da addini muhimanci wajen batun aure da soyayya, wani shafin Instagram ya ɓullo da wani shiri da ke gyara aurarrakin da bambance-banbancen addinin ko asali yake yi wa dabaibayi, wato dabaibayin addini ko asali ko ƙabilanci da kuma jinsi.

Wakiliyar BBC Geeta Pandey ce ta hada rahoton daga birnin Delhi.

An daɗe ana nuna fusata game da aure tsakanin mabambanta addini da asali a tsakanin iyalan Indiya masu ra'ayin mazan jiya, amma a shekarun baya-bayan tattaunawar da ake yi game da irin wannan auratayya ta ƙaru matuƙa.

Kuma akasarin an fi raina batun auratayya tsakanin mata mabiya addinin Hindu da kuma Musulmai maza.

Kamar dai yadda bambance-bambancen yake da tsanani, a watan da ya gabata ne hankula suka ƙara karkata a kai sosai, bayan da wani fitaccen kamfanin ƙera sarƙoƙi da ƴan kunnaye a ƙasar ta Indiya ya janye tallace-tallacensa da ke nuna wasu ma'aurata mabanbanta addini, bayan da ya rika samun suka a kafafen sada zumunta..

Tallar ta nuna bikin nuna farin ciki da aka shirya wa wata mata mai juna biyu wacce mai bin addinin Hindu ce, da surukanta Musulmai suka shirya mata.

Kamfanin na Tanisq ya yi wa wannan talla laƙabi da sabon tsarinsa na Ekatvam - da ke nufin ''haɗin kai '' da harshen Hindu.

Hakan na nufin nuna farin ciki ne game da tunani kan "hadin kai tsakanin mabambanta addini da ƙabila", - hakan ya ƙara fito da giɓin da ake da shi a tsakanin al'ummar Indiya.

Ƙungiyoyi masu tsattsauran ra'ayin addiinin Hindu sun bayyana cewa tallar tana kyautata " jihadin soyayya'' - kalaman nuna ƙin jinin addinin Islama, da ke nuna cewa Musulmai maza na yaudarar mata mabiya addinin Hindu don su aure su, don su Musuluntar da su.

Rupa and Razi Abdi

Asalin hoton, India Love Project

Bayanan hoto, Rupa da Razi Abdi sun shafe shekaru 30 da yin aure

Zazzafar muhawarar shafukan sada zumunta, ta haifar da ƙaurace wa wannan alama da aka tallata, inda ta faɗaɗa ya zuwa manyan labaran shafukan Twitter . A wata sanarwa, kamfanin ya bayyana cewa ya janye tallar ne tare da yin la'akari da kare lafiyar ma'aikatansa.

Makonni biyu bayan wannan takaddama game da tallar,wasu ma'aurata 'yan jarida Samar Halarnkar da Priya Ramani da wani abokinsu marubuci dan jarida Niloufer Venkatraman ya kaddamar da wani shafin Instagram kan Soyayyar India, yana bayyana shi a matsayin '' murnarsoyayyar mabanbanta addini/ asali da hadin kai a wadannan lokuta na nuna kin jinin juna da rarrabuwar kawuna''.

Mr Halarnkar ya shaida wa BBC cewa sun dade suna '' tunani game da wannan aiki har na tsawon shekara, ko ma fiye da haka'' kuma takaddama game da tallar ta kamfanin Tanisq ta kara masa karfin gwiwa wajen samun wannan dabara mai kyau wacce lokacinta ya zo.

"Mun matuƙar damu game da - labaran ƙarya game da soyayya da kuma auratayya tsakanin mabambanta addini,'' ya shaida min.

''Akwai labarun da ke cewa akwai wasu munafunce-munafunce, dalilan yin auratayya, cewa ana amfani da soyayya a matsayin makami. Amma ba mu san wani wanda ke da irin wannan tunani ba, wanda ke da wata manufa bayan son yin aure.''

Ta hanyar shirin Auren Soyayya a Indiya, ya ce, ''kawai muna samar da wani dandali ne inda mutane za su iya bayar da labarinsu''.

Mahaifan Niloufar

Asalin hoton, Aikin Soyayyar India

Bayanan hoto, Aikin ya fara da labarin mahaifiyar Niloufer Venkatraman 'yar asalin Parsi da mahaifinta mai bin addinin Hindu

Tun daga ranar 28 ga watan Oktoba - lokacin da wannan aiki ya fara, labarin farko da muka samu daga Ms Venkatraman game da mahaifiyarta 'yar kabilar Parsi ta ƙasar Iran, Bakhtawar Master da kuma mahaifinta ba Indiye S Venkatraman - a kullum mu kan wallafa sabbin labarai.

Amsa kiran da muka samu, in ji Mr Halarnkar, na da yawan gaske ''Muna ta ƙoƙarin ganin mun jure. A kullum muna samun saƙonni daga mutanen da kan ce ''ina son bayyana labarina, ko labarin iyayena' ko labarin kakannina.

Hakan kuma na nuna cewa auratayya tsakanin mabambanta addini, da mabanbanta asali ko ƙasa ba sabon abu ba ne, sun daɗe suna faruwa.

''Amma, ya ƙara da cewa, ''yana da matuƙar muhimmanci a yi magana a kansu yanzu fiye da a da.

"A daidai lokacin da ake ƙirƙirar ƙiyayya, yana da matuƙar muhimmanci a bayyana labarin irin wannan soyayya da yadda ta faɗaɗa, kana ba wai abu ne ƙarami ba.''

A ƙasar Indiya, fiye da kashi 90 bisa 100 na auren da ake yi, haɗa shi ake yi - kuma da wuya iyalai su duba batun da ya wuce addini da kuma asali a yayin da suke haɗa auren.

Kamar yadda wani bincike kan ci gaban al'umma na ƙasar Indiya ya nuna, kashi biyar bisa 100 kacal ne na auratayya tsakanin mabambanta asali.

Auren tsakanin mabambanta addini kuwa ya kasance ba kasafai ba - wani bincike ya saka shi a mizanin kashi 2.2 bisa 100.

Kuma duk wanda ya zaɓi yin aure a wajen wannan tsari, ya kan fuskanci tsangwama da cin zarafi - kuma ma zai iya fuskantar kisa.

Vineeta Sharma and Tanvir Aeijaz

Asalin hoton, India Love Project

Bayanan hoto, An tambati Tanvir Aeijaz da Vineeta Sharma wane addini ƴƴansu za su bi

A shekarun baya-bayan nan, da gwamnatin Hindu ce ke kan mulki, ra'ayin gargajiya ya ƙara samun tagomashi a Indiya, kana batun rarrabuwar kawuna tsakanin addinai ya ƙara girma.

Kana auratayya tsakanin mabambanta addini - musamman tsakanin mata masu bin addinin Hindu da kuma Musulmai maza - ana ɗaukar sa a matsayin wata mummunar manufa ne.

"A cikin watan Fabrairu, "Mr Halarnkar ya ce, "gwamnati ta shaida wa majalisar cewa batun ''auren jihadi'' ba shi da gurbi a cikin doka kana babu wasu bayanai da aka samu daga wasu hukumomin gwamnati, amma tunani game da hakan ya ƙaru.

''A kwanakin baya-bayan nan, a ƙalla jihohi huɗu da jam'iyyar BJP ke mulki sun sanar da samar da dokar da za ta kawo ƙarshen wannan ''mummunan abu a cikin al'umma.''

Wannan ''labarin ƙiyayya'' ne shirin Soyayyar Indiya ke ƙoƙarin ƙalubalanta ta hanyar tarin labaran da take tattarawa, da masu karantawa ke bayyana cewa'' mai nishaɗantarwawa da kuma ilmantarwa''.

Gajerun labaran masu yawan adadin haruffa 150, a kan rubuta su ne ta hanyar yin barkwanci da nuna ƙauna; da kuma bayar da labarin ma'auratan da suka yi amanna cewa soyayya ba ta ji ba ta kuma gani.

Maria Manjil da Sandeep Jain a ranar aurensu

Asalin hoton, India Love Project

Bayanan hoto, Maria Manjil da Sandeep Jain sun yi aure shekara 22 da suka gabata

Rupa, wata malamar addinin Hindu, ta rubuta game da yadda mahaifiyarta ta yi lokacin da ta faɗa mata cewa tana shirin auren wani Musulmi mai sunay Razi Abdi.

"Za a ambaci 'talaq, talaq, talaq' har sau uku ya ce ya sake ki,'' mahaifiyarta ta ce, tana mai nuna damuwa game da al'adar sakin aure na Musulmai, da yanzu doka ta hana a ƙasar Indiya.

"Amma kuma, a lokacin da iyayena suka hadu da Razi kana suka fahimci cewa mutumin kirki ne, mummunan zaton da suke da shi ya gushe,'' ta rubuta, tana bayyana su a matsayin '' mutane da ba su da boye-boye''.

Shekaru 30 kenan tun bayan da Rupa da Razi suka yi aure. Suna da manyan ƴaƴa maza biyu, kuma sun yi bikin Sallar Idi da na Hindu na Diwali tare a cikin gidansu.

Yayin da yake rubutu game da aurensa da Salma, ɗan jarida TM Veeraraghav ya ce a gidansu, addini '' ba shi da muhimmanci kamar kunun shinkafa da madara da kuma dafa-dukan shinkafa mai naman rago!''

"Na kasance wanda ba ya cin nama da dangoginsa sai ganyaye, tana jin daɗin cin naman ragonta da kuma albarkar soyayyarmu (ɗansu Ainesh) da ya samu jin daɗi daga duka duniya biyu. Ainesh Hindu ne ta wani gefen kuma Musulmi, duk dai ya danganta."

A sabon labarin da muka wallafa, Tanvir Aeijaz, wani Musulmi da ya auri Vineeta Sharma, mai bin addinin Hindu, ya rubuta game da saka wa ɗiyarsu suna, Kuhu.

An tambayi ma'auratan ko sunan Musulmi ne ko Hindi? Kana wane addini ne ɗiyar tasu za ta bi idan ta girma?

"Wannan auren Hindu da Musulmi namu ka iya zama zakaran gwajin dafi kan batun nuna bambance-bambancen addini da yadda mutane suka ɗauke shi,'' ya rubuta.

''Sun rasa ta cewa, kusan cikin nuna damuwa cewa za a kira soyayyarmu soyayya, ba soyayyar jihadi ba.''

Salma da TM Veeraraghav lokacin bikin aurensu

Asalin hoton, India Love Project

Bayanan hoto, TM Veeraraghav da Salma sun ce a gidansu addini ba shi da muhimmanci kamar kunun shinkafa hadi da dafadukan shinkafa da naman rago!''

Shafin na Instagram ya kuma wallafa labaran wasu aure-auren da suka faru tsakanin mabambanta addinai da kuma asali.

Maria Manjil, wata ƴar ɗarikar Katolika ce, kuma wadda ba mai barin cin nama zuwa cin ganyaye ba ce, ta kuma fito daga cikin iyalai masu sassaucin ra'ayi a birnin Kerala, wacce ta auri Sadeep Jain, ɗan asalin arewacin Indiya, kuma wanda ba ya cin nama sai ganyaye, da ya fito daga iyalai masu ra'ayin bin al'ada, ta rubuta ''kalubalen'' da suka fuskanta a cikin shekara 22 na aurensu, amma kuma ta amince cewa ta yi daidai da ta aure shi.

"Ta yaya za ka juya wa abin da kake so baya?" ta rubuta, ''Na fahimici yanayin kirki, kamala, ilimi, da kuma matukar ƙaunar da ya nuna min. Ba zai yiwu in bar shi ba don kawai addininsa daban kuma yarensa daban da nawa.''

Mr Halarnkar ya ce, labarai ne da kan saka ka ji daɗi game da wannan duniya da kuma game da Indiya.

"Duka waɗannan labari ne masu kyau na ainihin abin da ke faruwa a Indiya. Mutane na bin hanyoyi daban-daban zuwa soyayya. Sun kasance abin tunawa cewa haka ne game da Indiya.''