Coronavirus a Indiya: Annobar ta shiga cikin ƙabilar da ke barazanar ƙarewa

kabilar ta Andamans

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Soutik Biswas
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, India correspondent

Annobar korona ta yaɗu a cikin wata ƙabilar da ke cikin daji ta Andamans a wani tsibiri na Indiya.

Wani jami'in lafiya ya shaida wa BBC cewa mutum 10 daga cikin ƙabilar sun kamu da cutar a cikin wata ɗaya da ya gabata.

Huɗu daga cikin su da ke zaune a wani surƙuƙukin tsibiri an gano sun kamu da cutar ne a makon da ya gabata, sauran shidan kuma da ke zaune a birni wata ɗaya da ya wuce.

An yi amannar yawan ƴan ƙabilar Greater Andamanese bai fi 50 da ƴan kai ba, kuma yawanci suna zaune ne a ɗaya daga cikin tsibirai 37 na yankin archipelago.

A yankin gabashin na ƙabilar Andamans da Nicobar an samu masu cutar korona 2,985 da mace-mace 41 tun bayan da aka samu ɓullar cutar a yankin a farkon watan Yuli.

An gano mutane na farko da suka kamu da cutar korona ne a cikin ƙabilar Greater Andamanese da ke barazanar ƙarewa a makon da ya gabata a yayin da aka gano dukkan mutum 53 na ƙabilar sun kamu, kamar yadda Dr Avijit Roy ya shaida wa BBC.

Ma'aikatan lafiya da na gaggawa sun je tsibirin ta kwale-kwale a makon da ya gabata don yi wa duk ƴan ƙabilar gwaji a rana ɗaya.

"Dukkansu sun ba mu haɗin kai,'' in ji Dr Roy.

An kwantar da biyu daga cikin waɗanda suka kamu a asibiti, yayin da sauran biyun kuma aka keɓe su a wata cibiyar kula.

Dr Roy ya ce an kuma gano wasu mutum shida ƴan ƙabilar da ke zaune a birni sun kamu da cutar a watan da ya gabata. Dukkansu sun warke daga cutar.

Da yawan ƴan ƙabilar sun yi bulaguro tsakanin Gaɓar Teku na Blair da tsiirinsu, kuma ta yiwu sun kamu da cutar ne a yayin tafiyar, kamar yadda ya ce. Wasu ƙalilan daga ƙabilar suna ƴan ƙananan ayyuka a birane.

Dr Roy ya ce ana tabbatar da cewa annobar ba ta yaɗu ba a cikin ƙabilar shi ne babban abin da aka sa a gaba yanzu.

"Muna sa ido sosai kan mu'amalarsu da yi musu gwaji sosai,'' a cewarsa.

Ƙabilar Andamans na ƙunshe da ƙananan ƙabilu biyar da suka haɗa da Jarawas da North Sentinelese da Great Andamanese da Onge da kuma Shompen.

Jarawas da North Sentinelese har yanzu ba su haɗe da sauran ƙabilun ba. Ƴan ƙabilar North Sentinelese ba sa maraba da baƙi, kuma ba sa yarda kowa ya shiga tsibirinsu.

A shekarar 2018, an harbe wani Ba'amurke John Allen Chau da kwari da baka a yayin da ya yi ƙoƙarin shiga yankinsu.

A Jarawa man with a painted face

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu yawon bude ido da dama suna tafiyar sa'a biyu domin ganin yan 'yan kabilar.

A cewar wata ƙungiya mai cibiya a Landan, wacce ke aiki don nemar wa ƙabilu ƴancinsu, ta ce yawan mutanen ƙabilar Greater Andamanese ya kai fiye da 5,000 a lokacin da Burtaniya ta yi musu mulkin mallaka a tsibiran a shekarun 1850. Wasu cututtuka da suka yi ta fama da su ne suka yi sanadin rage yawan mutanen.

''Akwai matuƙar tashin hankali a ce an samu ƴan ƙabilar Great Andamanese da cutar korona. Dukkansu sun san bala'in da wasu annobobin suka jawo musu a baya na rage yawan mutanensu,'' a cewar wata babbar mai bincike na ƙungiyar Sophie Grigg.

A shekarar 2010 wani babban mai mai jin yarukan ƙabilar Great Andamanese naƙarshe Boa Senior, ya mutu yana da shekara 85. Tsibiran na ɗaya daga cikin waɗanda suke da ƙabilu daban-daban a duniya.

Su kuwa ƴan ƙailar Jarawa masu mutum 476 da suke zaune a wani daji tsakanin kudu da tsakiyar ƙabilar Andaman, tuni suka sake matsawa tare da keɓe kansu a can cikin daji bayan ɓarkewar annobar, a cewar jami'ai

A Jarawa man standing in water with a bow and arrow

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yankin Andamans mazauni ne na kabilu biyar dake fuskantar barazanar karewa, ciki har da 'yan kabilar Jarawas.

An tura tawagar ma'aikatan lafiya da likitoci don yi wa fiye da mutum 115 gwaji a cikin ƙabilar Ongi da ke zama a tsibirin, in ji Dr Roy. Sannan za a gwada ƴan ƙabilar Shompen.

Dukkan ma'aikatan lafiyar da ke shiga yankin sai an musu gwajin Covid-19 kafin su je, sannan a killace su tsawon mako ɗaya bayan sun koma.

Dr Roy ya ce zuwa yanzu an gano cutar korona a tsibirai 10 na archipelago.