Zaben Amurka 2020: Me ya sa ba mu samu sakamako ba?

Promo image showing ballots, a clock and a question mark

An daɗe da rufe rumfunan zaɓen shugaban Amurka amma har yanzu ba tabbas kan makomar takarar fadar White House tsakanin Donald Trump da Joe Biden ba. Ko Me ya sa?

Ya kasance a ko yaushe abu yiwuwa ba a sami sakamako a daren zaɓe.

Miliyoyin Amurkawa sun ƙada kuri'unsu tun kafin ranar zaɓen saboda annobar korona, wanda ke nuna jinkirin kiɗayar kuri'u abu ne mai yiyuwa.

Yaushe aka saba samun sakamakon zaɓen Amurka?

Yawanci sakamakon a bayyane yake a daren zaben.

Jihohi da dama suna kammala zaɓe a lokuta mabambanta. Abin da ke biyo baya shi ne yawan kuri'u kamar yadda aka ruwaito a kowace jiha.

Ba a kammala ƙidayar kuri'un a daren da aka yi zaɓe - wannan dama haka yake - amma kuri'un da aka samu za su iya tabbatar da wanda ya yi nasara.

Kafofin yaɗa labaran Amurka na iya hasashen wanda ya yi nasara a jihar idan har sun tabbatar da wanda ke kan gaba.

Ba wannan ba ne sakamakon ƙarshe amma kuma yana tabbata idan an kammala ƙidayar kuri'un zaɓen.

Ba ƙuri'un jama'a ba ne da suka kaɗa kuri'a ke tantance makomar zaɓen Amurka, amma yawan jihohin da ɗan takara ya lashe.

Duk wanda ya yi nasara a wata jiha yana da kason "kuri'un wakilai na kwalejin zaɓe" amma ta la'akari da yawan jama'arta

Ɗan takara kuma dole sai ya samu yawna ƙuri'u 270 na wakilan kwalejin zaɓe kafin lashe zaɓe shugaban ƙasa.

A 2016, an tabbatar da nasarar Trump bayan samun nasara a jihar Wisconsin saboda ya samu ƙuri'u fiye da 270.

Me ya sa wannan shekarar ta bambanta?

Annobar korona ta sa mutane yin zaɓe da wuri tun kafin ranar zaɓen ta hanyar zuwa kaɗa kuri'a ko kuma aikawa ta akwatin gidan waya.

Kuri'un da aka kaɗa ta akwatin gidan sukan ɗauki lokaci kafin a ƙidaya su domin sai an tantance, kamar sa hannu da kuma tabbatar da adireshi.

A mail carrier of the United States Postal Service delivers mail in Washington, DC, USA, 18 August 2020

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Annobar korona ta sa mutane yin zaɓe da wuri ta hanyar zuwa kaɗa kuri'a ko kuma aikawa ta akwatin gidan waya.

Wasu jihohi kamar Florida sun amince da wannan tsarin na fara zaɓe kafin ranar zaɓen. Wannan ne dalilin da ya sa aka samu tsaiku ga sanin sabon shugaban ƙasa.

Arizona ma wata jiha ce mai matukar muhimmanci da ƙuri'u ke da tasiri, don haka akwai yiyuwar za a samu taikun samun sakamako a jihar.

Waɗanne jihohi ake jira?

Jihohi kamar Pennsylvania da Wisconsin ba su amince da jefa kuri'a kafin ranar zaɓe ba.

Jihohin suna da muhimmanci - Wani jami'in zaɓe ya ce za a yi kwanaki ana ƙidayar kuri'a.

Sauran jihohi kamar Georgia, Michigan da North Carolina suna cikin lissafi.

Wane abu ne kuma ke kawo tsaiku?

Kusan rabin jihohin sun amince da tsarin aika ƙuri'a ta akawatin gidan waya bayan ranar zaɓen, idan har an tantance masu jefa kuri'ar a ranar 3 ga Nuwamba. Don haka wasu ƙuri'un sai bayan ranar zaɓen za a kiɗaya su.

Haka nan ana tsammanin za a samu ƙaruwa a zaɓen na ɗan lokaci - ƙuri'un da mutanen da suka buƙaci zaɓar akwatin gidan waya amma suka yanke shawarar zaɓa da kansu maimakon hakan.

Kuma waɗannan ba za a haɗa su da ƙidayar farko ba, saboda suna buƙatar bincike don tabbatar da mutane ba su yi zaɓe sau biyu ba.

Yaya ake kidaya kuri'u?

Yawancin kuri'un - ta takarda ko ta intanet - ana ƙidaya su da na'ura.

Amma jami'an zaɓe sai sun tantance takardar zaɓe da na'urar ta ki tantancewa.

Bayan rufe runfunan zabe, za ta tura bayanan zuwa ga babbar cibiyar tattara sakamako.

Poll worker cleans voting machine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Na'urar zabe a California

Wani lokaci ta intanet ake tura wa.

Amma a wasu wuraren, idan aka samu tanganɗar na'ura dole a karanto sakamakon daga wayar salula.

Da zarar an kammala tattara sakamakon, sakamakon zai nuna a shafin intanet na jihohi.

A ɗaya ɓangaren kuma ana shaida wa ƴan jarida alkalumman sakamakon a jihohi domin bayar da rahotanni.

Idan an kammala tattara sakamakon na jiha, daga nan hukumomi za bayyana sunan ɗan takarar da ya yi nasara a jihar.

Me zai faru idan aka samu saɓani game da sakamakon zaben?

Annobar ta riga ta haifar da shari'o'in zabe sama da 300 a cikin jihohi 44, a cewar wata cibiyar zaɓe ta MIT.

Kuma ƙuri'ar shugaban ƙasa na iya ganin ƙalubalen shari'a akan komai daga buƙatun tantancewa kan kuri'un da aka ƙadata gidan waya zuwa masu alaƙa da sauyin da annobar korona ta haifar.

Shugaba Trump ya ce sakamakon zaɓen ka iya ƙarewa a kotun ƙoli.

A 2000, an taɓa sake ƙidaya lokacin da ɗan takarar Democrat Al Gore ya sha kaye a Florida kuma an yi tsawon wata ɗaya - daga ƙarshe kotun ƙoli ta ba ɗan takarar Republican George W Bush nasara.