Ko ya za ta kaya tsakanin Trump da Biden?

Asalin hoton, Getty Images
Sakamakon baya-bayan nan a zaben shugaban kasa a Amurka tsakanin shugaba mai-ci Donald Trump na jam'iyyar Republican da abokin karawarsa Joe Biden na jam'iyyar Democrat na cewa kawo yanzu, babu dan takarar da ya bayar da tazarar da za ta ba shi damar lashe zaben kai tsaye.
Donald Trump na jam'iyyar Republican ya lashe wasu jihohi da ya samu nasara a baya, da suka hadar da Florida, da Texas, abin da ya bashi damar haɗa kuri'ar masu zaɓen shugaban ƙasa 213.
Sai dai duk da haka, shugaban na bayan Biden na jam'iyyar Democrat da ke kan gaba da kuri'ar masu zaɓe 220.
Ana bukatar ɗan takara ya samu kuri'ar masu zabe 270 jimlatan kafin ya samu nasarar zama sugaban ƙasa.
Har yanzu ana can ana ci gaba da ƙidayar ƙuri'u a jihohin Pennsylvania, da Wisconsin, da Michigan, da Arizona, da Ohio, abin da ke nufin babu wanda ya lashe su.
Sai dai Mista Biden na kan gaba a jihar Arizona, wadda shugaban ƙasar ya lashe a lokacin da ya doke Hillary Clinton a zaben shekarar 2016.
Dole ne shugaban ya samu nasarar lashe jihohin Pennsylvania, da Florida, matsawar yana son ya zarce a matsayin shugaban ƙasa a karo na biyu.

Asalin hoton, Getty Images
Ya sakamakon yake zuwa yanzu ?.
Gidan talabijin na FOX News dake Amurka ya rawaito cewa Biden zai lashe jihar Arozona, amma magoya bayan shugaba Trump na ganin ya yi wuri a yi tunanin haka.
Trump na kan gaba a ƙuri'un da aka ƙirga a jihohin Pennsylvania, da Michigan da Wisconsin zuwa yanzu, amma ƙuri'un da aka ƙirga zuwa yanzu na ranar zaɓe ne, ba a kai ga lissafa na kafin zaɓe ba, wanda ake kyautata zaton magoya bayan Biden ne suka fi yawa a nan.
Zuwa yanzu dai babu wani abin mamaki dangane da sakamakon, kowa ya samu jihohin da aka yi tunanin zai samu.
BBC na hasashe cewa Mista Trump zai rike jihohin Alabama, Indiana, North Dakota, South Dakota, Kentucky, Tennessee, Oklahoma, Arkansas da West Virginia, kamar yadda kowa ke tsammani.
Sannan BBC na hasashen Joe BIden zai rike jiharsa ta Delaware, sannan zai lashe New York, Colorado, Vermont, Maryland, Massachusetts, New Jersey da Washington DC.
Abokiyar huɗɗar BBC a Amurka, wato tashar talabijin ta CBS na cewa Trump na kan hanyar lashe jihohin South Carolina, Nebraska, Kansas, Louisiana, da Wyoming.
Sannan CBS na cewa jihohin Minnesota, New Mexico, Maine, Connecticut, Illinois, Rhode Island da New Hampshire na hannun Mista Biden.
Mista Trump zai yi wa kasa jawabi daga ofishinsa na Fadar White House cikin daren Talata agogon Washington DC, inda shi kuma Mista Biden na gidan iyalinsa na Wilmington Delaware inda yake dakon sakamakon zaben tare da masu yi masa hidima.
Yadda aka yi fitar ɗango tun kafin ranar zaɓe

Asalin hoton, Getty Images
Tun kafin ranar zabe mutane fiye da mutum miliyan 100 ne suka kada kuri'unsu gabanin ranar zabe, wanda a tarihi ba a taba samun jama'a masu yawa da suka fito zabe kamar na wannan shekarar ba, kuma ana sa ran fiye da mutum miliyan 150 ne za su kada kuri'unsu - wanda alkaluma da ba a taba samu ba ne a zaben na shugaban Amurka.
Amma ban da zaben shugaban kasa, akwai zabukan 'yan majalisar wakilai da na dattawa da aka yi tare da na shugaban kasa.
Babu tantama cewa jam'iyyar Democrat za ta ci gaba da rike majalisar wakilai, amma za ta yi kokarin kwace rinjayen 'yan majalisa a majalisar dattawa.










