Zaben Amurka na 2020: Kanun labarai uku da za ku iya wayar gari da su

Asalin hoton, Getty Images
A ƙarshe dai mun zo ranar. Kamar gasar marathon ta Olympics inda masu gudu suka shiga filin wasa a zangon ƙarshe na mita 400 a fili, suna ɗauke da gajiya zuwa layin ƙarshe.
Ya kasance wani yanayi mai ban mamaki, wani lokacin tashin hankali, tabbas Yaƙin neman zaɓen da ba a taɓa tunani ba da kuma ƙoƙarin gano abin da zai biyo baya gaba ɗaya.
Akwai yanayi da ake hasashe guda uku, kuma ba zan kasance na ƙarshe ba idan ɗaya daga cikinsu ya tabbata ( a zahiri akwai yanayi na huɗu, amma zan yi magana nan gaba.). Komi na iya faruwa.
Don haka bari mu duba abubuwa guda uku da za su iya faruwa.
1. Biden ya lashe zaɓe cikin sauƙi
Na farko shi ne ƙuri'ar ra'ayin jama'a ta yi gaskiya kuma Joe Biden ya yi nasara cikin ruwan sanyi a daren Talata.
Saurara, kasancewa mai jefa kuri'a a wannan lokacin zaɓen yana da matuƙar annashuwa kasancewa mai hasashen yanayi a gidan talabijin ɗin ƙasar Saudiyya: "Yau za ta kasance da zafi da kuma rana, haka kuma gobe za ta kasance da zafi da rana."
Duk da cacar baki a wannan ƴakin neman zaɓen - ba kamar shekaru huɗu da suka gabata ba - zaɓen gama-gari da kuma na muhimman jihohi sun tabbata. Babu abin da ya faru. Ba abin da ya sauya.
Biden ya ya samu gagarumin rinjaye a ƙasa da kuma jihohin Florida, da Arizona da North Carolina, kuma da irin tazara a - Wisconsin, Michigan da Pennsylvania.

Asalin hoton, Getty Images
2. Nasarar Trump ta ba da mamaki
Wannan zai iya kasancewa sakamako na biyu da zai iya faruwa.
Kamar a 2016 (ko da yake zan iya ɗaukar lokaci game da dalilin da hakan ba zai zama gaskiya ba) kuri'ar jama'a ba ta cinka daidai ba Donald Trump ya lashe wa'adi na biyu. Muhimmin abu ga nasararsa shi ne abin da ya faru a Pennsylvania da Florida.
Babu wanda ya yi tsammanin Biden zai kasance a gaba a muhimman jihohi da tazarar maki uku zuwa huɗu. A 2020 Trump ya fi samun karɓuwa ga Latinos fiye da 2016.
Haka ma Pennsylvania,inda yammacin jihar fararen fata ma'aikata za su iya yin tasiri ga nasarar shugaban.
A cikin wannan dokar kullen korona, ta tafi Florida, Ohio, Tennessee, Pennsylvania, North Carolina, Georgia da Virginia.
Kuma duk inda ka tafi za ka samu magoya bayan Trump cewa ba wai sonsa kaɗai suke ba - suna ƙaunarsa.
Kuma hasashen Trump shi ne kamar 2016 - lokacin da suka sa mutane suka fito kaɗa kuri'a akwai yiyuwar za su sake yin haka a wannan zaɓen.
Kuma ina son yin magana game da gangamin shugaban da yake.
'Yan Democrats sun yi ta ƙorafi cewa ana haɗa gangamin dubban mutane ba tare da bayar da tazara ba. Ba ni son shiga wannan mahawarar. Amma yin haka za ku yarda cewa wani lissafi ne mai kyau.
Kafin halartar waɗannan tarukan dole sai ka yi rijista a intanet, sannan a bi diddigi domin gano ko kana cikin kundin rijistar masu zaɓe - idan kuma ba ka ciki, za su yi maka rijista.
Dubban mutane aka yi rijista ta wannan hanyar domin kaɗa kuri'a kuma sakamakon haka a wannan zaɓen mai cike da ƙalubale, cire wannan shingen zai iya kawo wani sauyi.
Wani dalilin kuma da lashe zaben Trump ba zai zo da mamaki ba shi ne, Joe Biden yaƙin neman zaɓensa ba ya ƙarfafa guiwa.

Asalin hoton, Getty Images
Idan har wani ya wakilci wani tsohon mai gadi, to shi ne. Tsarin tsufa zalunci ne ga kowa, amma shugaban yana ganin ya fi Biden kuzari, duk da cewa tazarar shekaru uku ne kawai tsakaninsu. Ba kamar dai Biden yana "fata" don aron taken Obama na 2008 ba. Duk abin da yake da'awa shi ne, shi ba Donald Trump ba ne.
Amma wannan taken ya yi matukar tasiri a zaɓen 2020
3. Nasarar Biden ta ba da mamaki
Wannan shi ne yanayi na uku. Kuma kamar na biyu ne - kuri'ar jin ra'ayin jama'a sun bada ba daidai ba.
Sai idan wannan karon ba su karkata ne a ɓangare na daban. Kuma wannan shi ne idan Biden shi ya yi nasara ta tazara sosai.
Wannan zaɓen mai ɗaukar hankali, kwatankwacin nasarar Ronald Reagan kan Jimmy Carter a 1980. Ko kuma George HW Bush kan Michael Dukakis a 1988.
Saɓanin 2016, lokacin da Donald Trump ke bayyana saƙo ga Amurkawa cewa - yana son ya gina katanga - yana son hana Musulmi shiga ƙasar, yana son sake tattaunawa yarjejeniya cinikayya, yana son dawo da masana'antu - amma a 2020 ƙoƙari yake kan abin da zai bayyana idan har ya lashe wa'adi na biyu.
Don haka idan har Biden ya bada mamaki a manyan jihohi ya kuma lashe Texas, Ohio, Iowa, Georgia, da kuma watakila South Carolina.
Watakila idan ka kalli rumfunan zaɓe da tsarin zaɓen wuri da kuma yadda Democrats ta yi yakin neman zaɓen sosai, ka kuma kalli yawan sabbin masu jefa kuri'a, ba abu ba ne da za a ce ba zai yiyu ba
...sakamakon da zai iya faruwa (amma a 2020)
Na fada tun da farko cewa akwai yanayi na hudu da zai iya faruwa - Saboda yadda yadda kuri'in rukunin masu zabe wato Electoral college suka rabu a Nebraska, kuma abin da za a iya tunani shi ne hamayyar kuri'i 270 na masu zaben wanda zai ba ɗan takara nasarar lashe zaɓen. Amma zai iya kasancewa Biden yana da 269 haka ma Trump da 269.
Kuma bayan biliyoyin daloli da aka kashe, sakamakon zai kasance sun yi kankan, wanda ke tabbatar da Amurka ta rabu biyu.
Hakan bai taba faruwa ba, kuma na fada yana da wahala ya faru.
Amma ba zai yiwu ba kuwa?











