Amsar tambayoyinku kan yadda zanga-zanga take a tsarin ƙasa

Wata mai zanga zanga a Najeriya

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Imam Saleh
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa

Wannan maƙala ce ta musamman bayan da muka buƙaci mabiyanmu da masu saurare su aiko da tambayoyinsu kan yadda zanga-zanga take a tsarin ƙasa.

A farkon watan Oktoban 2020 ne wasu yan Najeriya suka shafe kusan mako biyu suna zanga-zangar nuna adawa da rundunar ƴan sanda mai yaƙi da fashi da makami ta Najeriya.

Yawanacin ƙasashen duniya ko dai sun taɓa fuskantar zanga-zanga ko suna kan fuskanta a halin da ake ciki, abin da kan janyo tsayawar al'amura cak!

Zanga-zangar ENdSars ta Najeriya ta yi tasirin da ta kai ga mahukunta sun amsa kiran jama'a nan take, tare da rushe rundunar yaƙi da fashi da makami ta hukumar 'yan sandan Najeriya wato SARS.

'Yan Najeriya sun sha yin zanga-zanga ko a baya, ga misali wadda aka yi a shekarar 2012, sakamakon cire tallafin man fetur a wancan lokaci da gwamnatin tsohin shugaban Najeriya Good Luck Jonathan ta yi.

A sauran kasashen Afrika ma an yi zanga-zangar da ta rikiɗe ta zama juyin juya hali a wasu kasashe kamar Sudan, har ta kai ga hamɓarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar Albashir bayan shafe shekara 34 yana mulki.

A Amurka, an gudanar da zanga-zangar da ta fi kowacce jan hankali a shekarun baya-bayan nan, bayan kisan bakar fatar nan George Floyd, a nan ma ta rikide ta zama tashin hankali, da kuma kone kadarorin gwamnati da dama.

A Turai har yanzu ba a shawo kan zanga-zangar da ta ki ci ta ki cinyewa ba a Belarus, bayan nasarar da shugaba Alexender Lukashenko ya samu a zaben kasar mai cike da takaddama, wanda 'yan adawa ke cewa an tafka son rai a cikinsa.

A nahiyar Asiya ma haka abin yake, zanga-zanga a Hong Kong, yankin da mazaunansa ke neman tsayawa da ƙafafunsu na ci gaba da jan hankali, duk da dokar tsaro da China ta kafa, wadda ta kai ga tsare masu sukar gwamnatin China da dama.

A Thailand 'yan kasar ne suka zaburo don nuna turjiya game da tasirin masarauta, da kuma yadda 'yan gidan sarautar kasar ke mulkin danniya da take hakkin dan adam.

Don haka zanga-zanga a duniya ta zama Hantsi leƙa gidan kowa, babu wata nahiya da ba a yinta, yawancin kasashen duniya ko an taɓa yi ko ana kan yi.

Presentational white space

Mecece zanga zanga?

zanga-zangar endsars

Asalin hoton, Getty Images

Barista Bulama Bukari, lauya ne mai zaman kansa, ya ce zanga-zanga wani gangami ne da al'umma ke yi don nuna yarda ko rashin jin dadinsu game da wani abu da ya shafi rayuwarsu.

Ya ce yawanci ana yi ne ga gwamnati da tsare-tsarenta, ''ko dai a nuna gamsuwa ko kuma nuna damuwa a kan wani abu da ya taso, da gwamnatin ke so a yi''.

A cewar Baristan ana yin zanga-zanga ne zuwa ko dai a gidan gwamnati, ko wani muhimmin waje da za a taru don nuna damuwa tare da daukar alamun goyon baya ko rashin goyon baya dangane a kan abin da ake zanga-zangar a kansa.

A wurare da dama dalilin da ke sa mutane yin zanga-zanga bai wuce rashin gamsuwa da yadda gwamnati ke tafiya da al'amura ba, musamman kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki, da more rayuwa.

Mutane kan yi fitar ɗango, ko dai a ƙafa ko a ababen hawa suna rera waƙe, ko kuma bayyana buƙatunsu cikin waƙa haɗe da damuwa don bayyana kokensu.

Da wuya ka ji an yi zanga-zangar goyon bayan gwamnati, amma hakan ba wai yana nufi ba a yi ba, sai dai kafin ka ji an yi zanga-zangar goyawa hukumomi baya za ka ji an yi ta ƙorafi ko rashin gamsuwa da wani al'amari bila adadi.

Yaya ya kamata ayi ta?

Presentational white space

A cewar Barista Bulama Bukarti, kamata ya yi a yi zanga-zanga cikin lumana ba tare da cutar da kowa, ko lalata kayan wani, ballantana har ta kai ga rasa rai.

Kamar a Najeriya akwai dokar da ta yi tanadin cewa dole ne a nemi izinin hukumomi, wato ƴan sanda kafin a yi zanga-zanga, amma a yanzu an soke ta.

To amma duk da haka ana son a tuntuɓi jami'an tsaro ko da yake bai zama wajibi ba, sai dai hakan zai taimaka wajen samar da tsaro da kariya a wuraren zanga-zangar, ta yadda za a daƙile duk wani yunƙuri na tayar da hankali.

''Hakan zai kuma bayar da damar kare ƙadarorin gwamnati da a lokuta da dama ake ƙonawa ko a lalata su'' a cewar Barista.

Ya kuma ƙara da cewa a nasu ɓangaren jami'an tsaro dole ne su samawa masu zanga-zanga tsaron da ya kamata a matsayinsu na ƴan kasa don kare rayuwarsu, da kuma sauran al'umma da ba su shiga zanga-zangar ba, da kuma wadanda ka iya amfani da wannan dama don aikata laifuka.

Presentational white space

Me doka ta ce a kan zanga-zanga?

A ƙasashen duniya da dama an amince da zanga-zanga, ana ma kallonta a matsayin ƴancin jama'a, da dole ne hukumomi su kare, idan kuma ta ki karewa wadanda abin ya shafa na iya shigar da kara don kwatar hakkinsu.

Kamar a Najeriya sashe na 40 na kundin tsarin mulkin kasar ya tabbatarwa kowanne dan kasa yancin yin zanga-zanga ko gangami ko wanne iri ne, ko na siyasa ko kasuwanci ko wata bukata da yake da ita, ciki har da zanga-zanga.

Barista Bukarti ya ce dokokin kasashen Afrika da suka tabbatar da ƴancin dan adam ma sun tabbatarwa jama'a wannan yanci.

Baya ga haka dokokin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya na kare ƴancin dan adam da kasashen duniya suka rattabawa hannu sun bai wa mutane damar yin zanga-zanga, hasalima sun kira ta a matsayin daya daga cikin manya-manyan ƴancin da jama'a ke da shi.

Ya ya kamata a shawo kanta? Tambaya daga Umar Yusuf Gammo da wasu da dama

Presentational white space

A kasashe da dama mahukunta kan yi amfani da ƙarfin ikonsu wajen shawo kan zanga-zanga, ta hanyar amfani da jami'an tsaro wajen daƙile ta, a wasu lokutan ma a kan kama jama'a a kai su gidan yari, sai dai masana doka na ganin cewa ba haka ya kamata a ce ana yi ba.

Kasashe da dama da suka yi kaurin suna wajen tauye hakkiin jama'a na amfani da irin wannan salo, abin da ke kara yamutsa al'amura, irin abin da Hausawa ke cewa ''garin neman gira, sai a rasa ido''.

zanga-zangar Libiya

Asalin hoton, AFP

Kwamared Sani Bala Tela, wani ɗan gwagwarmaya ne a Najeriya, kuma a cewarsa akwai hanyoyi da dama da ya kamata gwamnati ta bi don shawo kan zanga-zanga.

Daga cikin ya ambato maslaha, wato hukumomi su zauna da masu zanga-zangar domin jin kukansu, mene ne buƙatunsu? Me suke buƙata? Alabashi ta duba yiwuwar amincewa da su ko kuma a yi dai-dai ruwa dai-dai tsaki.

''Zaman lafiya ya fi komai, don haka durƙuwasawa wada ba gajiya ba ne'' in ji Sani Bala Tela.

To sai dai ɗan gwagwarmayar ya ce gwamnati na da haƙƙin kare rayuka da dukiyoyin jama'a idan ta lura suna neman fakewa da guzuma su harbi karsana, domin tabbatar da zaman lafiya da walwalar ƴan ba ruwana.

Shi kuwa Barrister Bulama Bukarti cewa ma ya yi jami'an tsaro na da damar amfani da ruwan zafi ko barkonon tsohuwa a kan masu zanga-zanga don tarwatsa su, idan dukkanin hanyoyin shawo kan rikici a yayin zanga-zanga ya ki aiki.

Sai dai lauyan ya ce haramun ne jami'an tsaro su yi harbi, ma'ana su harbi wadanda ke zanga-zanga ko wanne hali ake ciki.

Sai dai ya ce ana iya karfi dai-dai ruwa dai-dai tsaki a kan masu zanga-zanga, yayin da aka lura tashin hankali yayin zanga-zanga na neman wuce makaɗi da rawa.

Presentational white space

Shin zanga-zanga mafita ce? Tambaya daga Jabir Garba Ƙauran Wali da wasu da dama

''Eh to, a ƙasashe da dama zanga-zanga ta yi tasiri wajen sauya al'amura, hukumomin kan amince da buƙatun jama'a a wasu lokutan, amma wasu lokutan ihunka banza take zama'' a cewar Dan gwagwarmaya Kwamared Sani Bala Tela.

Ya ce a ƙasashe da dama da aka san haƙƙin mutane zanga-zanga ta yi tasiri wajen kawo sauyi da kuma juyin juya hali, da kan haifar da ci gaba, wasu kasashen kuma rikiɗewa ta yi ta koma yaƙin basasar da har kawo wannan lokaci babu ana fama da shi.

A ƙasashe kamar Sudan ta haifar da sauyin gwamnati da mutane ke nema ido rufe a wannan lokaci, wato hamɓarar da gwamnatin shugaba Omar Al-Bashir, tare da kafa sabuwar gwamnati, a halin da ake ciki ma ana shirin gabatar da shi a gaban kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta duniya.

zanga-zanga yemen

Asalin hoton, EPA

A wasu kasashen kuwa zanga-zangar rikiɗewa ta yi ta koma tashin hankali, daga nan ta zama yaƙin basasa, da har kawo wannan lokaci ana da na sanin abin da ya faru.

Libya :- Mai karatu zai iya tuna yadda zanga-zanga ta fara a Libiya, inda wasu yan kasar ke neman tsohon shugaban ƙasa Mu'ammar Gaddafi ya sauka daga kan mulki shi kuma ya ƙi sauka, abin da ya haifar da yaƙi a ƙasar, har ta kai ga kasashen duniya ciki har da Amurka da Faransa suka shiga yaƙin.

Har kawo wannan lokaci tasirin al'amarin da ya faru na daɗa shafar tsari, babu tsayayyiyar gwamnati a Libya, gwamnati biyu ake da ita, akwai ta birnin Tripoli wadda ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya, akwai kuma ta Khalifa Haftar wadda ke samun goyon bayan ƙasashen Rasha da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Siriya :- Haka ma kasar Siriya da har yanzu ake yaƙin basasa, lamarin ya faro ne daga zanga-zangar neman Shugaba Bashar Al-assad ya sauka daga kan mulki, nan ma ya ƙi sauka, nan ma dai abin ya rikiɗe ya zama gagarumin tashin hankali, a halin da ake ciki an rushe kusan kafatanin Syria sakamakon hare-hare ta sama, sannan tsawon shekaru bakwai kenan kasashen duniya na gwada ƙwanji, ta hanyar kai harin in ba ka yi ba ni wuri a kasar.

Yemen :- A nan ma dai wasu al'ummar ƙasar sun yi tutsu a shekarar 2014, inda suke nemi Shugaba Abdrabbuh Mansur Hadi ya sauka, amma ya ƙi, daga zanga-zanga abin ya juye ya zama yaƙin basasa, abin da ya buɗe wa kasashen duniya kofar shiga don gwada ƙarfin makamansu.

An kashe dubban mata da ƙananan yara a yaƙin da yaki ci ya ƙi cinyewa, sannan akwai ƙawancen ƙasashen duniya na musamman da Saudiyya ke jagorantar yin luguden wuta a kan ƴan tawayen Houthi, wadanda take zargi da janyo rikici a ƙasar.

Presentational white space

Kasashen da jama'a ba sa iya zanga-zanga

zanga-zanga a yeman

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Kasashe irin su Saudiyya ba a zanga-zanga

Babu wata kasa a duniya da dokokinta suka haramta zanga-zanga, sai dai a kan samu wasu da duk da jama'a na da damar yin ta, sukan hana a duk sa'ad da jama'a suka yunƙuro don nuna damuwarsu dangane da yadda al'amura ke gudana.

Kamar a Saudiyya ba safai jama'a ke fitowa hatta a kafafen sada zumunta don sukar gwamnati ba, ballantana a zo ga batun jama'a su taru a tituna don nuna adawa da wani salo da gwamnati ke tafiya a kai, ko ta bijiro da shi.

A wasu kasashe har ila yau kamar Singapore, da wuya ka ga ana zanga-zanga, saboda dokokin da suka tanadi cewa babu wani mutum da zai iya gudanar da wani taro har sai ya nemi izini daga hukumomi, sannan akwai tsattsauran hukunci da aka tanada a kan duk wanda aka samu da karya wannan doka.

Presentational white space