Jack Dorsey: Shugaban Twitter na shan yabo da suka saboda goyon bayan EndSARS

Jack mai Twitter

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Mai shafin Twitter Jack Dorsey na shan yabo da suka kan nuna goyon bayansa ga zanga-zangar da ƴan Najeriya ke yi ta adawa da rundunar da ke yaki da fashi da makami.

Ƴan Najeriya sun ci gaba da yin zanga-zanga duk da gwamnati ta rusa rundunar tare da gaggawar kafa sabuwar runduna ta mai suna SWAT, matakin da ga alama bai gamsar da masu zanga-zangar ba.

Mista Dorsey ya nuna goyon bayansa ga zanga-zangar ta hanyar yaɗa wani asusun tallafawa masu zanga-zangar inda ya fito a shafinsa na Twitter ya roƙi mabiyansa su tallafa wa zanga-zangar EndSARS.

Ya wallafa bayanan asusun a shafinsa dauke da alamar tutar Najeriya. Mista Dorsey ya kuma yaɗa wasu labarai na zanga-zangar a shafinsa wanda ke nuna goyon bayansa ga masu zanga-zangar.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Abin da ƴan Najeriya ke cewa

Wasu ƴan Najeriya musamman masu goyon bayan zanga-zangar sun yi maraba da goyon bayan Jack yayin da kuma wasu suka mayar da martani da kuma musayar kalamai tsakanin masu yabo da sukar mai shafin na Twitter.

Wani mamba a Jam'iyyar APC, wanda kuma ya taɓa neman takara shugaban ƙasa Adamu Garba ya caccaki mai shafin na Twitter tare da yin barazanar kalubalantarsa a kotu idan har kalamansa suka ƙara tunzara jama'a har zanga-zangar ta kazance.

Adamu Garba ya ce zai fi dace wa idan Jack ya fita sha'anin siyasar Najeriya. Kuma ya kamata ya sani zanga-zangar EndSARS ta rikiɗe ta koma wata farfagandar siyasa, da ke iya saɓawa doka da oda a Najeriya.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Sai dai wasu ƴan Najeriya yabon mai shafin na Twitter suka yi inda wani ɗan Najeriya ya ce ya yafe wa Jack duk da ya datse masa yawan masu bibiyarsa a Twitter saboda ya nuna goyon bayansa ga zanga-zangar EndSARS tare yi masa addu'a

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Wannan kuma ta ce suna godiya da nuna goyon baya ga gwagwarmayar da suke. Ta ce zaluncin da ƴan Najeriya ke yi ya wuce hankali. Mun koma muna ɓoye wa abin da ya kamata a kare mu.

Kauce wa X, 4
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 4

Wannan ta yi wa Jack fatan yawancin rai inda ta rubuta cewa shekaru 600 ga Jack saboda nuna goyon bayansa ga zanga-zangar EndSARS

Wasu kuma na ganin kalaman na Jack rura wutar rikici ne a Najeriya.

Kauce wa X, 5
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 5

Ya ce wannan neman haifar da rikici ne a ƙasata, idan ba ka sani ba wasu sun mamaye zanga-zangar kuma wannan abin damuwa ne da tayar da hankali

Kauce wa X, 6
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 6

Wannan ya ce Jack ba ya da ƴancin yin haka. Ya fuskanci matsalolin ƙasarsa.. Ƴan Najeriya su zama masu hikima.. su yi gwagwarmayarsu ta hanyarsu.. kar su bari su faɗa masu abin da za su yi - domin za su yi kuka.