'Mahaifina yana yi wa tsarin masarauta makauniyar soyayya'

Asalin hoton, Jilla Dastmalchi
"Mahaifina ya koyar da ni cewa sukar lamirin sarakuna tamkar saɓo ne. Babban laifi ne."
Amma Danai*, yanzu mai shekaru 19, ya bijire wa gargadin mahaifin nasa. Dalibi mai karatun lauya a birnin Bangkok, yana daya daga cikin dubban masu zanga-zanga da ke mamaye titunan babban birnin Thai a kowane wata, suna neman a yi wa tsarin masarauta garanbawul.
Mahaifinsa Pakorn* mai yawan tafiye-tafiye, mai matsakaiciyar wadata ne. Duk da cewa ba a gida daya suke zaune ba, amma suna yawan haduwa da juna. Sai dai a duk lokacin da suka hadu sukan kaucewa yin magana a kan batun: masarauta.
"Muddin muka yi magana game da batun, za mu shiga zazzafar sa-in-sa kuma zai rushe mana duk wata walwala ta ranar,'' Danai ya ce.
"Mun taba yin gardandami a cikin motarmu bayan da na soki lamirin sarki. Mahaifina yana ganin babu wanda ya isa a fadi laifin sarki. Na tambaye shi ko menene dalili. Na yi yarintar da ba zan iya fahimtar komai ba, in ji shi. Ya fusata sosai, kana sai ya yi tsit bai sake yi min magana ba.
Takaddama a shafukan sada zumunta
Amma iyalai a Thailand ba wai a ƙeƙe-da- ƙeƙe ne kawai suke gardandami game da tsarin masarauta ba, da dama sun yanke shawarar su riƙa fafatawa a shafukan sada zumunta.
Kuma al'amuran sun ƙara tsanani.
Lokacin da wata ɗalibar jami'a ta bayyana a shafinta na Facebook cewa mahaifinta na son gurfanar da ita a gaban kotu saboda ra'ayinta na nuna ƙin jijin tsarin masarauta, ya mayar da martani ta hanyar wallafa cewar daga yanzu ya haramta mata amfani da sunan iyalansa.
A karon farko lokacin yana da shekara 17, Danai ya ƙalubalanci mahaifinsa game da batun na masarauta.
"Muna cikin Sinima. Kafin a fara saka fim, lokacin da aka saka taken masarauta kamar yadda aka saba, kowa ya miƙe tsaye don girmamawa ga sarki. Ban so yin haka ba, don haka sai na ci gaba da zama a kujerata. Mahifina ya tilasta mini tashi tsaye, amma na turje. Sai da jama'a suka fara sa mana ido, daga bisani na tashi.''

Asalin hoton, Jilla Dastmalchi
Kin tashi tsaye lokacin da aka saka taken masarauta karya dokar ne
Tarihin wannan al'ada
'Yan ƙasar Thailand tun suna ƙanana ake koya musu mutuntawa da ƙaunar sarkinsu, har ma da su ji tsoron abubuwan da za su iya biyo bayan duk wata suka game da shi. Ƙasar, wacce aka saba yi wa lakabi da wurin saka murmushi, ɗaya daga cikin ƙananan ƙasashen da ke amfani da dokar nan ta masarauta ''less majeste''. Hakan na nufin sukar lamirin sarkin, ko sarauniya ko mai jiran gadon sarauta karya doka ce -kuma duk wanda aka kama zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekara 15.
A yau, Danai ya daina tashi tsaye a cikin Sinima.
Tun a cikin watan Yuni ne, dubban ɗaliban jami'a suka bazu a kan tituna. Suma neman a rage ƙarfin iko da harkokin kuɗi na sarkin da ya kasance ba shi da iyaka.
Waɗannan buƙatu ka iya zama sabon abu ga mutane a wasu sassan duniya, amma a ƙasar ta Thailand babu wanda ya taɓa fitowa a fili ya ƙalubalanci masarautar.
Zanga-zangar ɗaliban ta gigiza akasarin 'yan kasar - da suka haɗa da mahaifin Danai', Pakorn.
"An haife ni lokacin mulkin sarki Rama na 9. Ya yi wa mutane abubuwan alkahairi fiye da 'yayansa. Lokacin da ya kwanta rashin lafiya, na kasance a shirye da in bar duniya muddin hakan ne zai iya tsawaita rayuwarsa.
Amma matasan baya bayan nan kamar da na ba su san komai ba.''
Sabon sarki

Asalin hoton, Jilla Dastmalchi
A shekarun baya ba taɓa zaton wannan fito-na-fito na matasan da dattawan ba. Amma naɗa sabon sarkin, Sarki Maha Vajiralongkorn, ya sauya komai.
Ba a cika ganin sabon sarkin a bainar jama'a ba, kana yakan fi zama a ƙasar Jamus - tun ma kafin ƙasar Thailand ta faɗa cikin matsalar annobar cutar korona.
Akwai ayoyin tambaya game da matakinsa na karɓe ƙarfin ikon duka rundunonin sojin da ke birnin Bangkok - karfin sojin a hannun masarauta ya zama wani abun ba zata a mulkin zamani na ƙasar ta Thailand.
Ana shan tattaunawa a kan yanayin harkokin rayuwarsa na ɓoye. Ya yi aure har sau huɗu, kana an bayyana cewa yana da matan waje da dama.
Amma kuma, ana kallon marigayi Sarki Rama na 9 a matsayin wani tsarkakakke. A duk inda ya shiga mutane kan kwanta a gaban shi suna kiran kan su a matsayin "kasa tafin kafarsa.''
"Akwai wani lokaci da ina cikin motata, sai na hango shi yana tahowa. Babu motar alfarma, babu jiniya. Mun haɗa ido. Na girgiza sosai. Ina tunanin yana son kawai ya yi wasu abubuwa kamar sauran mutane. Na ga wani annuri tare da shi, ganinsa wani abu ne na musamman.
Bincikar abubuwan da suka gabata
Amma Danai bai fahimci damuwar mahaifinsa ba. "Idanunsa sun rufe kan batun masarauta. Magana da shi tamkar magana da bango ne. Ba ya son ya saurara.''
Dangantaka ta yi tsami saboda bambancin ra'ayi game da sarki - rarrabuwar kawuna tsakanin matasa da dattawa a cikin al'umma.
Tun bayan da ɗalibai suka fara gudanar da zanga-zanga a lokacin bazara, kawunan iyalai a fadin ƙasar Thailand na kara rarrabuwa. Iyaye, 'yaya, 'yan uwa maza da mata, kawunnai da dangoginsu sun zame wa juna tamkar bare. Matasan Thai na sukar lamirin masarauta da ma duk abin da ta ƙunsa - kuma wannna ka iya zama wasa farin girki ne na gagarumar taƙaddama tsakanin iyalai a ƙasar.
*An sauya sunayen saboda kare wanda ke cikin labaris.











