Ɗalibar da ke ƙalubalantar tsarin Masarautar Thailand

Asalin hoton, BBC News Thai
"Ina cike da tsoro a cikin zuciyata, ina tsoron abin da zai biyo baya," in ji Panusaya Sithijirawattanakul .
A watan Agusta, Panusaya mai shekara 21 ta hau kan wani dandamali a Thailand, inda ta ƙalubalancin sarautar ƙasar.
Ta yi bayanin ne ga dubban ɗalibai suna ta shewa a ɗaya daga cikin manyan jami'o'in Thailand, inda ta karanto wasu kudirori 10, take kira da a yi gyara ga masarauta.
Wannan wani yunƙuri ne mai tsoratarwa. 'Yan ƙabilar Thais, tun daga haihuwarsu ana koya musu su so sarautar ƙasar su, amma su guji abin da zai biyo baya idan sun yi magana kan sarautar.
'Rayuwa na yawan sauyawa'
Thailand na daga cikin ƙasashe ƙalilan da ke da dokar da ke hani ga cin mutuncin saraki ko masarauta. Duk wanda ya caccaki sarki ko sarauniya ko kuma yarima mai jiran gado za a iya yanke masa hukuncin zama gidan yari na shekara 15.
Amma a 'yan watannin da suka wuce, masu goyon bayan mulkin dimokraɗiyya sun mamaye ƙasar, kuma ɗalibai kamar irin su Panusaya na daga cikin waɗanda ke kan gaba.
"Ni na san cewa rayuwata ba za ta taɓa tsayawa yadda take ba har abada," inji ta a wata hira da BBC.

Asalin hoton, Reuters
An nuna wa Panusaya kudirin ne sa'o'i kaɗan kafin ta karanta shi a gaban masu zanga-zanga da dama da ke a Bangkok, babban birnin ƙasar. Abin da suke nema a yi a ƙasar shi ne dole ne masarautar ƙasar ta rinƙa fayyace komai ga zaɓaɓɓun 'yan siyasa, da kuma buƙatar rage kasafin masarautar ƙasar da kuma hana masarautar yin katsalandan a siyasar ƙasar - wanda waɗannan kalamai ne waɗanda suka girgiza ƙabilar Thais.
"Sun miƙo mani kudirin, kuma suka tambaye ni idan zan iya amfani da shi. A lokacin, kowa na tunanin abin da zan karanta na da ƙarfi matuƙa, nima kaina na yi tunanin hakan. Sai na amince na zama wadda zan karanta abin.
"Na riƙe hannun 'yan uwana ɗalibai, inda nake tambayarsu ko abin da muke yi daidai ne," in ji Panusaya.
"Amsar ita ce eh hakane, abin da ya kamata kenan. Sai na ƙara zama, na zuƙi taba sigari, kafin na hau kan dandamali."
Ko da ta hau dandamalin, ta shaida wa ɗumbin jama'a cewa: "Duka bil adama launin jininsu ja ne. Ba mu da bambanci.
Jawabin da Panusaya ta yi ya jawo ce-ce-ku-ce - inda kuma a lokacin da take jawabin malaman jami'ar da dama sun tafa mata, a wani ɓangaren kuma kafafen watsa labarai mallakar masarauta sun ta caccakar lamarin.
'Rashin kishin ƙasa cuta ne'
Kwanaki kaɗan bayan faruwar wannan lamari, an ta caccakar Panusaya a shafukan Facebook na manyan masu goyon bayan masarautar ƙasar, inda wasu ke zargin ta da cewa 'yan jam'iyyar adawa ne suka zuga ta, lamarin da ta musanta.
Apirat Kongsompong, wanda wani babban janar ne a ƙasar ta Thailand da har yanzu soji na taka rawa wurin mulkin ƙasar, ya bayyana cewa masu wannan zanga-zangar "rashin kishin ƙasa ne ya sa suke hakan, ya kuma ƙara da cewa abin da suka yi ya fi annobar korona illa.
"Ɗora wa ƙasa karan tsana cuta ce, kuma cutar da ba ta da magani," in ji shi.

Asalin hoton, Reuters
Amma duk da haka, Panusaya ta bayyana cewa ko lokacin da take ƙaramar yarinya, ta tuna lokacin da take saka alamar tambaya kan gidan sarautar ƙasar.
A wata rana da ake maka zafi, kwatsam sai wani jami'in gwamnati ya je gidan su Panusaya ya ƙwanƙwasa ƙofa, ya buƙaci mutanen gidan da su fito waje su zauna su jira wucewar motocin gidan sarauta.
"Me ya sa za mu fito har na tsawon sa'a ɗaya da rabi mu tsaya cikin rana domin jira mu ga wucewar jerin motoci? Ban san me ke faruwa ba. Na ƙi fita waje na tsaya da taron mutane."
Panusaya ita ce 'yar auta daga cikin 'yan uwanta uku mata, kuma tun tana ƙarama ta nuna cewa tana son siyasa. A lokacin da take makarantar sakandire, labarin siyasa shi ne abin da ta fi so ta tattauna da ƙawayenta.
A lokacin da aka yi juyin mulki a 2014, sai mahaifinta wanda shi kaɗai ne a gidansu wanda ke bin labarun siyasa, ya ba ta ƙwarin gwiwa kan cewa ta yi bincike kan lamarin.

Asalin hoton, EPA
Sai dai a lokacin da Panusaya ke tasowa tana ƙarama, 'yan makarantar na cin zalinta. Wata makaranta da ta je a Amurka na watanni biyar ta sauya ta baki ɗaya.
"Na dawo gida a matsayin wata ta daban, inda ba na tsoron furta abin da ke cikina."
Sai ta ƙara zama 'yar gwagwarmayar siyasa bayan ta shiga jam'ar Thammasat. Shekara biyu da suka wuce, ta shiga wata ƙungiya ko kuma jam'iyyar ɗalibai a makarantar da ake kira "Dome Revolution".
A watan Fabrairu, ta taimaka wajen haɗa wata zanga-zangar goyon bayan dimokraɗiyya bayan rushe jam'iyyar Future Foward, wata jam'iyya ce wada ke da goyon bayan matasa wadda aka rushe bayan wani hukuncin kotu mai cike da ruɗani inda aka zargi jam'iyar da karɓar bashiba bisa ƙa'ida ba daga shugaban jam'iyyar.
Jam'iyyar ta yi koƙari matuƙa a zaɓen 2019, kuma ana kallon rushe ta a matsayin wani yunƙuri na daƙile masu goyon bayanta da ke ƙaruwa a kullum.












