Coronavirus: Giwaye na cikin tsaka mai wuya

Asalin hoton, Alex Johncola
- Marubuci, Daga Celia Hatton
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
Sama da giwaye 1,000 ke cikin yunwa a Thailand saboda yadda annobar coronavirsus ta zabtare kudaden shiga a fannin yawon bude ido, a cewar masu kare hakkin dabbobbi.
Rashin baki zai haifar da barazana ga masu kula da dabobbi da dama, da ke fafutukar ganin sun ciyar da giwayen Thailand 4,000 da ake garkame da su.
Dabbar na iya cin kilo 200 na abinci a rana guda.
Thailand ta ce ta sake samun sabbin mutane 127 da suka kamu da coronavirus a ranar Litinin, wanda hakan ya kawo adadin masu dauke da cutar 1,651 a kasar.
Lek Chailert, ta gidauniyar Save The Elephant Foundation da ke kare giwaye, ta shaida wa BBC cewa: ''Idan ba a samu agaji ko tallafin ceto rayukan wadannan giwaye ba, wasu na dauke da juna-biyu, za su mutu cikin yunwa ko kuma a tura su bara a kan tittuna.''

Asalin hoton, Save the Elephants
Ko kuma, wasu giwayen a sayar da su ga gidajen adana dabbobbin dawa ko kuma a koma tsarin sana'ar nan ta giwaye da aka haramta a 1989.
''Yanayin da ake ciki mai wuyar sha'ani ne in dai ba wai an samu taimakon kudin tallafi ba ne a cikin gaggawa". a cewar Lek Chailert.
Akwai kalubale wajen kosar da dabbobbin da kuma kasancewarsu cikin koshin lafiya a lokuta da dama, ga shi kuma yanzu lokaci ne na bazara, wanda hakan ya sake ta'azzara lamarin.
Kerri McCrae, ta wata kungiya mai suna Kindred Spirit Elephant Sanctuary da ke kare dabbobbi ta Mae Chaem, da ke arewacin Thailand, ta ce kauyawan da ke rayuwa a kusa da ita sun kawo mata karin giwaye akalla bakwai saboda sun daina samun kudi daga baki.
Ta ce ''Ciyar da giwayen abu ne mai muhimmanci sai dai matsalar ita ce babu isassun dazukan da zasu wadatar a ciyar da su".


Asalin hoton, Kerri Tumenne
Ms McCrae, 'yar asalin Ireland ta Arewa da ta kafa gidauniyar, ta ce ta na tukin sa'o'i uku a kullum domin neman ciyayi da buntun dawa don ciyar da giwaye biyar da suke karkashin kulawarta.
Ta ce suma wasu masu kula da giwayen yanayin da ake ciki na tilasta musu bin sawun ta.
Kasar, da ta dogara da baki wurin samun kaso mai tsoka na bunkasar tattalin arzikinta, an tilasta mata rufe iyakokinta ga baki da kuma kafa dokar hana fita.
Giwayen da ke cikin farin ciki, a cewar McCrae za ka iske su suna wasa da hancinsu ko bude kunnuwa ko su yi wasa da kasa domin jin sanyi-sanyi.
Sai dai su na shiga damuwa sosai idan su na jin yunwa, wanda hakan ke tasiri ko nunawa a yanayinsu.
''A wasu lokutan masu giwayen kan shiga cikin yanayi na zabi tsakanin kansu ko giwayensu,'' a cewar Ms McCrae.
Tac e ''Wadannan mutane ba su da hali sosai, amma suna iya kokari wajen ganin sun sanya farin ciki da tabbatar da cewa wadannan giwaye sun rayu".












