Sarkin Thailand Vajiralongkorn ya auri dogariyarsa

Asalin hoton, EPA
Sarkin na Thailand ya auri mataimakiyar shugaban fannin tsaron shugaban, kuma ya ba ta matsayin sarauniya, a cewar wata sanarwar da masarautar ta fitar.
Sanarwar mai cike da ban mamaki na zuwa ne mako daya kafin a gudanar da bikin rantsar da shi wanda za a yi a ranar Asabar, a dai dai lokacin da aka gama tabbatar da matsayinshi.
Sarki Maha Vajiralongkorn mai shekaru 66, ya zama shugaban kasar bayan da ya rasa mahaifinsa a 2016.
Ya yi aure so uku kuma duk ya rabu da su. Sarkin yana da yara bakwai.
Wata sanarwa da masarautar ta fitar ta ce sarki Vajiralongkorn ya yanke hukuncin kara wa dogariyarsa matsayi wato Janar Suthida Vajiralongkorn Na Ayudhyi, domin ta zama sarauniya Suthida kuma ta zamo daya daga cikin 'yan gidan na sarauta.
Dama dai Sarauniya Suthida ta dade da zama budurwar Vajiralongkorn kuma an yi shekara da shekaru ana ganin su tare a waje, duk da cewa basu bayyana ko suna tare ba.

Asalin hoton, Reuters
An nuno hoton bikin na su a gidajen talabijin na Thailand a daren Alhamis, a inda aka nuno yadda mambobin gidan na su da kuma masu aiki a fadar lokacin da suka halarci bikin.
An nuno yadda sarkin ya ringa zuba tsaftataccen ruwa a kan Sarauniya Suthida. Daga baya sai su ka saka hannu a kan takardar shedan auren su.
A shekara ta 2014, Vajiralongkorn ya baiwa Suthida Tidjai matsayin mataimakiyar shugaban dogaranshi. Suthida dai ta taba aiki a kamfanin jiragen sama na Thai Airways.
Ya kara mata matsayi zuwa janar a disambar 2016.
Tsohon sarkin, Bhumibol Adulyadej ya yi mulkin kasar na tsawon shekara 70, shi ne sarkin da ya fi dadewa a kan mulki duk duniya a lokacin da ya mutu a 2016.











