Yadda wani alkali a Thailand ya harbi kansa a kotu

Wani alkali a Thailand ya harbi kansa a yayin da yake gabatar da wani jawabi na bazata da ya soki tsarin shari'ar kasar.
Kanakom Pianchana ya sallami wasu Musulmi maza biyar da tuhumar da ake musu ta kisan kai a ranar Jumma'a kafin ya bukaci a samar da tsarin adalci a aikin shari'ar kasar.
Daga nan sai ya furta wata rantsuwa ta shari'a, kana sai ya fito da wata bindiga kumababu wata-wata sai ya harbi kansa a kirji.
An kuma ga wata sanarwa da ake ganin alkalin ne ya rubuta gabanin shari'ar, wanda a ciki yayi shagube kan yadda ake katsalandan a shari'ar.

Asalin hoton, Getty Images
Yadda lamarin ya auku
Alkalin yana aiki ne a wata kotu mai suna Yala a yankin kudancin Thailand mai fama da masu tada kayar baya.
Bayan ya sallami mutanen su biyar daga tuhumar da ake musu na kisan kai da mallakar makamai, sai ya yi jawabi wanda aka wallafa shikai tsaye a Facebook.
"Ana bukatar kwararran hujjoji kafin hukunt mutane. Saboda haka idan ba ka tabbata ba, to kada ka yanke musu hukunci," inji shi.
"Ba ina cewa wadannan mutane biyar din ba su aikata laifukan ba ne, wata kila sun aikata su."
Ya kuma kara da cewa "Amma ya kamata tsarin shari'a ya kasance mai inganc da adalci...yanke wa wadanda ba su aikata laifi ba na mayar da su tamkar abin tozartarwa."
Daga nan bidiyon da ake wallafa a Facebook ya yanke, amma wadanda ke cikin kotun sun ce alkalin ya karanta wata rantsuwa ta shari'a a gaban hoton tsohon sarkin Thailand kafin ya fito da bindiga kuma ya harbi kansa.
Daga nan aka garzaya da shi asibiti kuma yana samun sauki.












