Coronavirus a duniya: Ta yaya za a iya yi wa mutum biliyan bakwai riga-kafin Covid-19?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, Daga Naomi Grimley
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar BBC kan abubuwan da suka shafi duniya
Kungiyoyi da kasashe a duniya na ci gaba da fadi tashin ganin sun samar da riga-kafin da zai kawo karshen annobar Covid-19.
Firaministan Burtaniya Boris Johnson ya bayyana hakan a matsayin "gagarumar hoɓɓasa da duniya ke gani a wannan rayuwa".
Amma baya ga batun binciken kimiyya da fasaha kan kirkiro riga-kafi mai ɗorewa, ina batun samar da isasshen riga-kafin da zai wadatar da al'ummar duniya biliyan bakwai.
A Burtaniya, Jami'ar Kimiyya ta Harwell da ke Oxfordshire ce cibiyar wannan bincike.
Za ta kasance cibiyar ƙirƙira da samar da riga-kafin na Burtaniya, wato VMIC, tsarin da aka bijiro da shi bayan ɓullar Covid-19.
"Mun kai wani mataki na wa'adin da muka gindaya. Don haka muna sa ran kammala komai kafin ƙarshen shekara ta 2022, amma kafin nan za mu wallafa bayanan da muka tattara a intanet a 2021,'' a cewar Matthew Duchars, shugaban cibiyar ta VMIC.
'Tamkar gashin ket'
Har yanzu dai Mista Duchars bai soma hutun bazara ba, saboda yana da ƙwarin gwiwar cewa wannan wuri zai samar da riga-kafin Jami'ar Oxford. Yana yawan tuntuɓar tawagar da ke kan aiki a cibiyar Jenner, wadda ke kusa da Oxford.
Ya ce aikin wani babban nauyi ne da aka ɗora musu.
"Yana da muhimmanci sosai, ba wai ga Burtaniya kaɗai ba har da duniya, a yi ƙoƙarin samar da riga-kafin a ciki gaggawa da inganci,'' a cewarsa.
"Bari na yi muku gwari-gwari - abu ne kamar kana gashin ket a gida. Kana iya daukar tsawon sa'o'i a ƙoƙarin haɗa haɗɗaɗen ket sannan sai ka zo ka yi ƙoƙarin fita ka gasa irinsa har miliyan 70, kuma dole kowanne ya kasance ya haɗu, ka ga kuwa akwai ƙalubale.''
Jami'ar Oxford zuwa yanzu ta tanadi wuraren gwaji na wucin-gadi domin soma samar da riga-kafinta, tun kafin ma ta ji me sakamakon zai kasance idan aka yi gwaji a duniya.
Rige-rigen bijiro da riga-kafin zai samar da bilyoyin riga-kafin cutar korona. Sannan a zo matakin batun rabawa da gwada ingancinsa a sassan duniya.
Gamayyar kungiyoyin da ke sa ido kan riga-kafi -Gavi - ta bukaci kasashe su soma nazari kan fito da riga-kafin da suka gano tun a yanzu.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai ba abu ne mai sauki ba, samun hadin-kan duniya, saboda kasashe masu arziki sun soma ƙulla yarjejeniya da kamfanonin samar da magunguna domin ganin cewa su kadai za a dinga bai wa riga-kafin idan an dace.
Son zuciya
Shugaban Gavi, Seth Berkley, ya ce daya daga cikin kalubalen da yake fuskanta shi ne yadda kowa ke neman zama "kasar da ya samar da riga-kafi".
"Idan kana da tanadi mai kyau na riga-kafi da ke yawo a kasashe, ba za ka iya koma wa kasuwanci da aka saba ba, balaguro ko zirga-zirgar mutane.
Yana da muhimmanci mu sa a ranmu cewa: Ba za mu tsira ba, in dai ba mun tabbatar kowa ya tsira ba.''
Yayin da ake kokarin ganin kasashen da suka samu ci gaba sun gano riga-kafin gaske, ya zama dole Mista Berkley ya yi nazari kan ingancin riga-kafin da za a fito da shi. Ana yi ta samun rahotannin kan rububin neman burgewa.
"Akwai damuwa sosai," a cewar Mista Berkley, ''don haka mun yanke hukuncin sayo kwalbar zuba ruwan sirinji biliyan biyu, adadin maganin da muke sa ran samarwa kenan kafin karshen shekara ta 2021.''
Idan wannan kwalabe ana musu kallon matsala, to su ma haka firij, tun da akasari waɗannan riga-kafi dole a adana su a waje mai sanyi.
Wuri mai sanyi
Farfessa Toby Peters, kwarare kan adana kayan sanyi a Jami'ar Birmingham, na ƙoƙarin taimaka wa ƙungiyoyi kamar Gavi nazari a kan yadda za su takaita yawan bukatar sanya riga-kafi a firij musamman a ƙasashe masu tasowa.
Ya ce: "Ba wai firjin ajiye riga-kafi ba ne, ya shafi sauran kayayyaki da hidindimu: hidimar jigila su a jirgi; motar da za ta dauka zuwa wurin ajiya, da baburan da za su kwashe su da mutanen da za su rarraba a yankuna. Duk waɗannan ayyuka ne ba masu sauki ba."

Asalin hoton, Getty Images
Farfesa Peter na tattauna wa da kamfanonin abinci da lemuka a duniya da su gwada tsarin da zai tafi daidai da bincikensa.
"Domin tabbatar da cewa an yi nasara a riga-kafin, dole kasashe su yi aiki tare wajen ganin wa za a fi bai wa fifiko a cikin al'ummarsu."
Waye na farko?
Dokta Charlie Weller, shugaban riga-kafi a Wellcome Trust na Burtaniya, ya ce akwai bukatar kasashe su yi tambayar da babu wasa a ciki.
"Wa ke bukatar riga-kafi? Suwa ye suka fi fuskantar barazana? Su wa za a fi bai wa fifiko? Saboda abin ba ɓoyayye ba ne, kuma rashin haka zai haifar da giɓi ko ƙarancin riga-kafin, don haka akwai bukatar yin zaɓi."
To ko yin riga-kafin zai kasance mai wahalar sha'ani.
Misali Burtaniya na duba yiwuwar amfani da kafar da take zabe a matsayin hanyar tantance al'ummarta. Amma ga kasashe matalauta abin da kamar wuya.
Dokta Weller ya dage akan cewa fanin lafiya mai karfi shi ne jigo, da jami'an lafiya masu kwarewa da zasu iya yiwa rukunin mutanen allura
Masana kimiya na da kwarin gwiwar cewa riga-kafi zai samu. Sai dai akasari su na cewa suna tashin cikin dare domin tunanin yadda riga-kafin zai wadatar ko yadda za a yiwa bilyoyin al'ummar duniya wannan rigakafi.










