Riga-kafin Coronavirus: Matar da ke jagorantar samar da maganin coronavirus

Farfesa Sarah Gilbert a wajen aiki

Asalin hoton, University of Oxford, John Cairns

Bayanan hoto, Farfesa Gilbert da tawagarta na fatan samar da riga-kafin cutar korona nan ba da jimawa ba

Farfesa Sarah Gilbert, ta shaida wa BBC cewa dole su yi aiki cikin sauri domin samar da magani ko riga-kafin cutar korona.

Masanar kimiyyar wadda ke aiki a Jami'ar Oxford, na cikin hanzari wajen ganin ta samar da riga-kafin cutar korona wadda ta shafi mutum fiye da miliyan 15 tare da kashe wasu fiye da dubu 630 a duniya.

Tare da 'yan tawagarta su 300 a Jami'ar ta Oxford, sun yi kokari wajen bin hanyoyi daki-daki na samar da riga-kafin wanda ake ganin samar da itan zai dauki dogon lokaci.

Ta ce ' Mun yi kokari mun yi aikin a cikin watanni hudu kawai'.

Sakamakon farko sun ba da kwarin gwiwa: gwajin da aka yi kan mutane ya nuna alamun nasara cewar riga-kafin ka iya aiki ba tare da matsala ba kuma zai inganta karfin garkuwar jikin da zai yaki kwayar cutar.

Ko da yake ba a tabbatar da sahihancin abin da aka samar ba a yanzu, amma kuma za a fara amfani da shi ne zuwa nan da karshen shekarar da muke ciki, kuma akwai fatan cewa an kai wa gaci.

Wacece Sarah Gilbert?

Farfesa Sarah Gilbert a wajen aiki

Asalin hoton, University of Oxford, John Cairns

Bayanan hoto, Gilbert Farfesa ce data kware a bangaren samar da riga-kafin cututuka a Jami'ar Oxford

Farfesa Gilbert na jagorantar tawagar da ke kokarin samar da riga-kafin cutar korona.

Tawagarta a Jami'ar Oxford, ta hada gwiwa da kamfanin samar da magunguna na AstraZeneca, sun kuma yi gwajin riga-kafin a kan mutum 1,077.

Tun lokacin da riga-kafin da suka samar aka ga alamun nasararta bayan mutanen da aka yi wa gwajin garkuwar jikinsu ta nuna cewa za ta iya yakar kwayar cutar koronar, ta zamo abin kwatance da alfahari.

Ko da yake ya yi wuri a gane cewa ko riga-kafin ta isa ta kare mutane daga cutar.

Sunan Farfesa Gilbert ya watsu ko ina a kafafen yada labarai, sannan kuma ana ta nemanta don a yi hira da ita a kafafen yada labarai.

Amma, kamar sauran abokan aikinta, ta saba zuwa aikinta ne kawai amma ba ta son a nunata a kamara.

Matasa masana Kimiyya

Wata masanar kimiyya na aiki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai dama da aka bude ga matasa masana kimiyya

Farfesa Gilbert ta ce, a ko da yaushe tana son tayi aiki a bangaren bincike na bangaren lafiya, amma a lokacin da ta ke shekara 17 ba ta san ta inda za ta fara ba.

Matakin farko shi ne ta samu takardar shaidar kammala karatun digirinta a bangaren nazarin kimiyyar halittu daga jami'ar gabashin Anglia, sai ta wuce ta ci gaba da karatu inda ta kai matakin da ta samu matsayin farfesa a bangaren Biochemistry.

Daga bisani kuma ta je ta yi nazari a bangaren bincike a kan magunguna da ma yadda za a hada mgani.

A shekarar 1994, Farfesa Gilbert, ta zama kwararriya a bangaren bincike da samar da magunguna a Jami'ar Oxford.

Mafi yawancin bincikenta ta yi su ne a kan samar da riga-kafin cututtuka.

Ta na aiki ga kuma iyali

Scientist with full protection gear examining a sample

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Yin aiki kana da iyali abu ne mai matukar wuya

Farfesa Gilbert, ta haifi 'ya'yanta 'yan uku a 1998, da shekara ta zagayo kuma ta zama malama a jami'a.

Ta ce 'Abu ne mai matukar wuya ka hada aiki da kuma kula da iyali, a lokacin ba ni da wani mataimaki, makarantar kula da yara da ya kamata na kai 'ya'yana kudin ya yi yawa don yafi albashina'.

Mijinta shi ne ya yanke shawarar ajiye aikinsa domin ya kula da 'ya'yan nasu, amma ta ce gaskiya abun da wuya matuka.

Ta ce, 'Na dauki tsawon watanni 18 a matsayin hutun haihuwa domin na kula da 'ya'yana wadanda na haifa bakwaini, kai na sha wahala sosai'.

To sai dai farfesar ta ce wani abu da aikin kimiyya shi ne ba dole ne ka yi aiki kullum ba ko kuma tsawon sa'o'i.

A shekarar 2004, ta kara samun ci gaba a jami'ar da take aiki, shekaru uku bayan nan ta yi wani bincike a kan riga-kafin cutar mura wanda ta yiwa wani wajen bincike a Landan aiki, a nan ta kara samun daukaka.

Taimako daga iyali

Yadda ake samar da riga-kafin cutar korona

Asalin hoton, Science Photo Library

Bayanan hoto, Yadda ake samar da riga-kafin cutar korona

Yayin da 'yan ukunta ke girma, sai take samun saukin abubuwa in ji ta.

Yanzu shekarun 'ya'yanta 21.

Dukkansu suna karatu a fannin kimiyyar sarrafa sinadaran kwayoyin halitta wato Biochemistry, ma'ana suna bin sawun mahaifiyarsu.

Suna kuma sha'awar aikin mahaifiyarsu na yadda take kokarin samar da riga-kafin cutar korona inda har dukkansu suka amince a yi gwajin riga-kafin da su.

Farfesar ta ce, a yanzu abu mai muhimmanci shi ne mun fi mayar da hankali a kan gwajin riga-kafin da kuma tunanin yadda za a samar da shi isasshe domin a rage yaduwar cutar a duniya baki daya.