Coronavirus: Yadda za ku kaucewa shiga damuwa da tabin hankali

News about coronavirus pouring out of a smartphone

Asalin hoton, Emma Russell

    • Marubuci, Daga Kirstie Brewer
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

Coronavirus ta jefa duniya cikin rashin tabbas, kuma labarai game da cutar a kullum na nuna kamar ba sauki.

Dukkanin wannan na tasiri ga lafiyar kwakwalwar mutane, musamman wadanda ke fama da yanayi na fargaba da matsalar da ta shafi lafiyar kwakwalwa da ake kira Obsessive Compulsive Disorder (OCD).

Don haka ta yaya za mu kare lafiyar kwakwalwarmu?

Lokacin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar da shawarwari kan yadda za mu kare lafiyar kwakwalwarmu a lokacin annobar coronavirus, yawancin mutane sun yi na'am da matakin musamman a kafofin sadarwa na Intanet.

Kamar yadda wata kungiyar agaji da ke kula da lafiyar kwakwalwa a Birtaniya Nicky Lidbetter ta bayyana, tsoron fita daga hayyaci da kuma kasa jurewa hali na rashin tabbas su ne alamomi na damuwa.

Don haka abu ne da za a iya fahimtar cewa yawancin mutanen da dama ke fama da matsalar damuwa a yanzu suna fuskantar kalubale.

"Yawancin tushen damuwa na farowa ne daga zulumi kan rashin tabbas da kuma jiran faruwar wani abu - coronavirus na kan wannan karamin ma'aunin," in ji Rosie Weatherley, mai magana da yawun cibiyar kula da lafiyar kwakwalwa ta Birtaniya Charity Mind.

Karin bayani kan coronavirus
Karin bayani kan coronavirus

Don haka ta yaya za mu kare lafiyar kwakwalwarmu?

1. Takaita karanta labarai da kiyayewa kan abin za ka karanta

Healthcare and medicine vector art illustration. Coronavirus news arouses much fear, girl screaming on TV

Asalin hoton, Getty Images

  • Takaita yawan lokacin da kake dauka kana karatu ko kallon wani abin da ba zai sa ka jin dadi ba. Watakila ka tantance lokacin da ya fi dacewa ka duba labarai.
  • Akwai labarai na karya da dama da ke yawo - Ka kiyaye ta hanyar dogaro da majiya mai tushe kamar shafukan intanet na gwamnati da kuma hukumomin lafiya.

Karanta labarai da yawa game da coronavirus ya haifar da fargaba ga Nick, uba ga 'ya'ya biyu a Birtaniya da ke fama da damuwa.

"Idan ina cikin damuwa, tunani na sa na fita hayyacina na fara tunanin sakamako marar kyau," in ji shi.

Nick ya damu ne da iyayensa da kuma tsofaffin da ya sani.

"Yawancin lokaci idan ina cikin damuwa nakan fita cikin yanayi. Amma wannan ya fi karfina," in ji shi.

Kauracewa shafukan watsa labarai da kafofin sadarwa ya taimaka min sosai na samun sa'ida daga damuwa.

Ya kuma samu taimako, daga kungiyoyin agaji kan kula da lafiyar kwakwalwa.

2. Samun hutu daga kafofin sadarwa da kauracewa duk abin da zai haifar da damuwa

Infographics of woman with facemask looking at her tablet

Asalin hoton, Getty Images

  • Kaucewa wasu kalamai da za su janyo matsala a Twitter da kuma daina bibiyar shafin
  • Kaucewa shafukan WhatsApp da boye bayanai a Facebook da kake ganin za su jefa ka cikin damuwa

Alison, mai shekara 24, daga Manchester a Birtaniya tana fama da matsalar damuwa kuma tana ganin ya dace ta san komi tare da bincike game da lamarin - amma kuma a lokaci guda tana sane cewa kafofin sadarwa na haifar da matsalar.

"A watan da ya gabata na danna wani maudu'i kuma ganin wasu bayanan karya da ban tantace ba kan jefa ni cikin damuwa har na kai ina kuka," in ji ta.

Yanzu ko tana taka-tsantsan kan shafukan da suka dace ta shiga da kuma kaucewa danna duk wani maudu'i kan coronavirus.

Tana kuma kokari ta kauracewa shafukan sada zumunta da kallon TV ko karanta littattafai maimakon su.

Wannan layi ne

Karin labaran da za ku so ku karanta

Wannan layi ne

3. Wanke hannaye - Amma ba wai a wuce gona da iri ba

Infographics of person washing hands.

Asalin hoton, Getty Images

Kungiyar OCD Action ta samu karin neman taimako daga mutane wadanda fargabarsu ta dogara kan annobar coronavirus.

Yawancin wadanda ke fama da matsaloli na damuwa da ake fadawa su yawaita wanke hannu sukan bijirewa umurnin.

Lily Bailey, marubuciyar wani littafi mai taken Because We Are Bad, ta ce shawarwari game da wanke hannu na kara jefa mutane cikin damuwa musamman wadanda suka warke.

Illustration of cleaning products

Asalin hoton, Emma Russell

Ta bayyana cewa yawancin mutane da ke fama da matsala ta damuwa, samun sauki shi ne samun damar fita daga gida - killacewa wani kalubale ne

"Idan aka tursasa muna mu zauna a gida, muna da lokaci sosai, kuma rashin walwala na iya sa damuwar ta yi muni," in ji ta.

4. Ci gaba da yin mu'amula da mutane

Coronavirus vector illustration - people talking on smartphones

Asalin hoton, Getty Images

Yawan wadanda suka killace kansu, yanzu lokaci ne da za ka tabbatar kana da lambobin da suka dace da adireshin imel na mutanen da ka damu da su.

"Amincewa da zuwa diba lafiya akai-akai da kuma ci gaba da mu'amula da mutanen da ke kusa da kai," in ji Weatherley.

Idan ka killace kanka, ya kamata ka samu daidaito kan ayyukanka tare da tabbatar da cewa a kullum ka samu sauyi.

Sakamakon zai iya kasancewa mai dadi da amfani a tsawon mako biyu.

Za ka iya tsara abin da za ka yi ko karanta littafi da ka dade kana so.

5. Gujewa yawan damuwa

Downtime - a cup of tea in the garden

Asalin hoton, Emma Russell

Yayin da za a shafe makwanni da watanni cikin wannan annoba ta coronavirus yana da muhimmanci ka samu lokaci.

Kungiyar kula da lafiyar kwakwalwa ta Mental health Charity Mind ta bayar da shawarwari kamar kokarin samun hasken rana da motsa jiki da cin abinci sosai da kuma shan ruwa sosai.

Wannan layi ne

Karin labarai masu alaka