Lamidon Adamawa ya yi tsokaci kan 'yan gudun hijira

Lokacin karatu: Minti 1

Yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalar 'yan gudun hijira sakamakon tarzomar Boko Haram, musamman a arewa maso gabashin Nijeriya, Mai martaba, Lamidon Adamawa, Alhaji Muhammadu Barkindo Mustafa ya bukaci masu ruwa da tsaki su kara himma wajen taimaka wa 'yan gudun hijirar, wadanda rahotanni ke cewa adadinsu ya kai kimanin muliyan uku.

Babban basaraken garjiyar wanda jiharsa ta Adamawa ke daga cikin yankunan da matsalar 'yan gudun hijirar ta fi Kamari, ya bayyana haka ne a lokacin da tsohon sakataren wajen Birtaniya, kana shugaban kungiyar agaji ta duniya da ake kira International Rescue Committee, Mista David Miliband, ya kai masa ziyara a fadarsa cikin wannan mako.

Wakilinmu, Is'haq Khalid, ya tattauna da Lamidon na Adamawa, inda ya fara da tambayarsa shin me zai ce game da ayyukan da kungiyoyin agaji musamman na kasshen duniya ke yi wajen taimaka wa 'yan gudun hijirar?