Hukumar NDLEA ta yi babban kamu

Asalin hoton, AFP
Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya Custom, reshen jihar Ogun, a kudu maso yammacin kasar, ta mika wa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA, wasu manyan buhunhuna 90 cike da ganyen wiwi.
An dai cafke wannan tabar wiwi ne bayan wani samame da rundunar ta custom ta kai a bakin iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin.
Buhunhunan tabar wiwin dai suna da nauyin kilo 1225.
Hukumar NDLEA ta ce za ta kona buhunhunan ganyen wiwin a kan idon jama'a.






