'Yan sanda na tuhumar wasu da tsafi a Edo

'Yan sanda sun ce za a gabatar da mutanen a gaban kuliya

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto, 'Yan sanda sun ce za a gabatar da mutanen a gaban kuliya

Hukumar 'yan sanda a jihar Edo da ke kudancin Nigeria ta ce ta damke mutane sama da dari da daya bisa zarginsu da hannu a ayyukan tsafe-tsafe.

A cewar 'yan sanda, ayyukan mutanen sun hada da kashe bil-adama da yin garkuwa da sace-sace da kuma sauran manyan ayyuka na asha.

Daga cikin mutanen, hukumar ta 'yan sandan ta gabatar da wasu goma sha daya gaban manema labarai a Abuja.

Mataimakin babban jami'in hulda da jama'a na 'yan sandar kasar, Umar Shelleng ne ya shaida wa BBC cewa an samu makamai da hotunan wasu mutane da ake zargin sun kashe su a hannun mutanen.

Ya kuma kara da cewa ana kara bincike a kan lamarin, kuma sun gano akwai likitoci da injiniyoyi har ma da 'yan makaranta a cikin manyan masu aika-aikan nan.