Masar, Habasha da Sudan za su raba ruwan Nilu

Habasha zata kashe fiye da dala biliyan hudu wajen gina madatsar ruwan
Bayanan hoto, Habasha zata kashe fiye da dala biliyan hudu wajen gina madatsar ruwan

Kasashen Masar da Habasha da kuma Sudan sun sa hannu kan yarjejeniyar share-fage raba ruwa daga kogin Nilu da ya ratsa tsakanin kasashen uku.

Yunkurin ya biyo bayan sabuwar madatsar ruwa mai samar da wutar lantarki da Habasha za ta gina, wadda kasar ke fatan za ta magance mata matsalar karancin wutar lantarki.

Shugabannin uku sun yi maraba da yarjejeniyar da aka cimma a birnin Khartoum na Sudan.

Sai dai a baya shugaban Masar Abdul Fatah Al-sisi ya ce madatsar ruwan tana janyo damuwa a Masar.

Ya ce "Duk da cewa Madatsar ruwa da aka yi wa lakabi da Renainssance za ta kawo cigaban rayuwa ga miliyoyin al'ummar Habasha ta hanyar samar da makamashi da baya gurbata muhali, sai dai ga 'yan uwansu a can Masar da ke zama a bakin kogin Nilu wadanda suma adadinsu ya kai haka, lamarin na janyo musu damuwa saboda rayuwarsu ta dogara ne a kan kogin wajen samun ruwa."