'Boko Haram: Gwamnati ba ta gaza ba'

Asalin hoton, hausa
Ministar kudin Nigeria, Ngozi Okonjo Iweala ta musanta zargin da ake yi cewar gwamnatin kasar ta gaza wajen kawo karshen hare-haren bama-bamai a kasar.
A cewarta gwamnatin kasar na iyaka kokarinta domin tabbar da zaman lafiya a cikin kasar.
Dr Iweala ta ce "Mun nuna cewar zamu iya magance abubuwan da ke faruwa, wanda ya dasa bam a Kano, an tsare shi. Kuma gwamnati na kokari don yin abinda ya dace da ita".
Kalamanta na zuwa kwana gwada bayan da aka kashe mutane fiye da 20 a wani harin bam a wata kasuwa da ke birnin Maiduguri a jihar Borno.
'Yan Nigeria da dama na caccakar gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan a kan cewar ta kasa kawo karshen zubar da jinin da ake yi.
A halin yanzu dai kusan watanni uku kenan da 'yan Boko Haram suka sace wasu 'yan mata dalibai kusan 300 a Chibok da ke jihar Borno.
Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewar rikicin Boko Haram ya raba mutane fiye da 650,000 da muhallinsu.







