Chibok: Kwamiti ya gabatar da rahoto

Asalin hoton, AFP

Kwamitin gano gaskiyar sace 'yan matan Chibok fiye da 200 ya gabatar da rahoto ranar Juma'a, inda ya ce babu wata Daliba da aka 'yantar bayan 57 sun kubuta tun da farko.

Da yake gabatar da rahoton karshe, shugaban kwamitin, Burgediya Janar Ibrahim Sabo ya ce 'yan mata 219 ne har yanzu ba a gano ba, tun bayan sace su a ranar 14 ga watan Afrilu.

Kwamitin ya kuma ba da shawarar kada a bayyana sakamakon bincikensa ga al'umma saboda dalilan tsaron kasa da kuma yunkurin kubutar da 'yan mata.

Ya ce bai kamata batun 'yan matan Chibok ya zama wani al'amari na zarge-zarge ba, don kuwa babu abin da hakan zai amfana.

Sace 'yan matan Chibok fiye da 200 ranar 14 ga watan Afrilu, batu ne da ya ja hankulan al'ummar duniya inda aka rika sukar gwamnatin Nijeriya kan gaza ceto 'yan matan ta hanyar gangamin "A dawo mana da 'ya'yanmu mata".