An kone wasu kauyuka a Jihar Borno

Rahotanni daga Najeriya sun ce wasu da ake ake zaton 'yan Boko Haram ne sun ci gaba da kai farmaki a wasu kauyuka na arewacin Borno dake iyaka da Kamaru.
Mazauna yankin sun ce an kashe mutane da dama an kuma kone wasu kauyuka a Karamar Hukumar Kala Balge.
Sun ce kauyukan da aka konen sun hada da Gazirga da Al-kulkule da Chokobe da kuma Kulfa.
Sun dai ce tunda sanyin safiyar Asabar ce maharan ke ta kai farmaki a kauyukan babu kakkautawa.
Wani mazaunin yankin ya gaya wa Sashen Hausa na BBC cewa mutane da dama sun tsere zuwa Kamaru.
Ya ce an fafata tsakanin mazauna yankin da 'yan bindigar kafin 'yan bindigar su yi galaba saboda kauyawan ba su da makamai.
Ya ce babu jami'in tsaro ko daya a wajen, balle ma a kai masu dauki.
Hukumomi dai basu ce komai ba akan lamarin.










