An kashe mutane fiye da 30 a Borno

Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima
Bayanan hoto, Gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima

Rahotanni daga garuruwa hudu na jihar Borno sun ce mutane fiye da talatin sun mutu a hare-hare da ake zarin 'yan Boko Haram sun kai.

Haka kuma bayanai sun nuna cewar an kona gidaje tare da jikkata wasu mutane da dama.

Lamarin ya auku ne a garuruwan Krenuwa da Moforo da Kimba da kuma Kubribu.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan Boko Haram ke tsananta hare-hare a wasu kauyukan jihar Borno.

Sannan kuma ga 'yan mata dalibai fiye da 200 da aka sace a Chibok da ke jihar Borno.

Kungiyar Boko Haram ta kashe dubban mutane musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Abuja babban birnin kasar.